Ronaldo Zai Koma Amurka Da Buga Wasa

0 397

Rahotanni daga kasar Amurka sun bayyana cewa tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United da Real Madrid da PSG da AC Millan, David Beckham yana son siyan Cristiano Ronaldo a sabuwar kungiyar daya bude mai suna Inter Miami. A shekarar data gabata ne dai tsohon dan wasan ya kaddamar da sunan kungiyar da kuma bajonta a gaban magoya bayan da zasu goyi bayan kungiyar kuma tuni shirye shirye sukayi nisa wajen ganin kungiyar tasamu nasara. Kusan shekara hudu da rabi kenan da fara shirye shiryen kafa kungiyar kuma tuni Bechkam, wanda ya bugawa kasar Ingila wasa ya nuna cewa yanason yakawo dan wasan Jubentus, Cristiano Ronaldo kungiyar domin ya karkare buga wasanninsa a kasar Amurka. Sabuwar kungiyar ta Bechkam dai zata fara buga gasar kasar Amurka a shekara ta 2020 sai dai kafin lokacin kwantaragin Ronaldo da Jubentus saura shekara daya yakare hakan yasa Bechkam yake ganin zai iya samun dan wasan idan lokaci yazo. Tun bayan komawarsa kasar Amurka dai Bechkam ya saka hannun jari a kungiyoyi da dama sai dai daga baya kuma shima ya yanke shawarar bude sabuwar kungiya domin buga wasa a kasar Amurka. Ragowar ‘yan wasan da ake ganin Bechkam zai nema sun hada da tsohon dan wasan Manchester United, Wayne Rooney da James Milner da Radamel Falcao da kuma dan wasa Neymar dake buga wasa a kungiyar PSG.

Leave A Reply

Your email address will not be published.