RUWAN KASHE GOBARA! 13

0 172

_13_

Dubanshi take idanuwanta cikeda kwalla hankalinta atashe amma ta kasa furta koda kalma daya sai hawayen dake sharara akan kumatunta,
“Dama nasan haka zata faru amma dan Allah kiyi hakuri ikhlas, ki dauki kaddarar da Allah ya aiko miki,ki sani wlhi ko matata ban sanarwa ba, duk duniya babu wanda yasan wannan abun”
Batare da tace komai ba ta juya ta nufi dakin ni’ima, kwanciya tayi tafara kuka mai cin rai wanda babu bata lokaci zazzabi mai zafi ya rufeta,elmustapha kam ta barshi a falo a tsaye yana nazari domin dama yasan haka zata faru dole,
Dakin yabita yaje ya babbata hakuri ya fito, tun daga ranar ikhlas ta shiga cikin kunci kullum ita kenan cikin kunci, gashi sai ta kule adaki tayita kuka, ko kuma ta shiga toilet ta zauna tayita faman kuka,
Elmustapha yana kokarin kyautata mata a kullum amma hakan baiyi sanadiyyar gogewar bakin cikin dake narke acikin zuciyarta ba, kullum cikin kuka take gashi zoben dake hannunta tarasa a inda ta sameshi dan haka ko wanne lokaci cikin zuba masa ido take tana kallonsa mintuna kadan kuma sai tafara kuka kullum ita kenan cikin kuka ga wani zazzabi da take fama dashi mai mutukar zafi.
Yauma tana kwance akan gadon ni’ima ta zubawa zoben dake hannunta ido sai kawai ta fashe da kuka mai sauti,
Sautin kukanta har falo domin hatta elmustapha da ni’ima suna jiyota,
“Barrister anya kuwa yarinyar nan tagama warkewa daga haukan nan? Ni ina ganin mu mayar da ita asibiti asake dubata domin kullum ita kenan acikin kuka, koda wanne lokaci acikin kuka take”
Mikewa elmustapha yayi ya nufi dakin da ikhlas take ni’ima ta mara masa baya,
Suna shiga suka sameta tana kuka sosai kamar ranta zai fita,
“Ikhlas meya faru?” Elmustapha ya tambayeta cikin tashin hankali, shiru bata amsa ba sai rage sautin kukan da take yi da tayi, tambayar duniya taki amsa mishi hakan yasa ni’ima kama hannunshi ta fitar dashi waje ta dawo wurin ikhlas,
Akusa da ita ni’ima ta zauna ta dafa kafadarta tana kallonta,
“Kiyi hakuri ikhlas, dan Allah kidaina wannan kukan, wai meyake damunki ne? Ko zazzabin da kike yine yake saki kuka kullum?”
Hawayen idonta tafara kokarin sharewa amma har lokacin hawayen basu tsaya ba,
“Babu abinda yake damuna Anty ni’ima”
Hannuwanta ni’ima ta kama ta rike cikin nata “haba ikhlas tayaya kike tunanin Zan yarda da wannan bayanin naki wanda yafi kama da tatsoniya”
Murmushin karfin hali ikhlas ta kakaro tayi ta kalli ni’ima tace,
“Ba tatsoniya bace anty ni’ima gaskiyata na fada miki sai dai nikaina ban san abinda yake sani kuka ba, narasa dalili”
“Yakamata dai ki daure kidaina domin wannan kukan da kikeyi bashida wani amfani atare dake, narokeki pls kiyi hakuri kidaina”
“Anty ni’ima nadaina, bazan sake ba insha Allah”
Tashi ni’ima tayi tafita domin komawa wurin elmustapha,
Abakin gadonshi ta sameshi azaune yayi tagumi yana kallon sama daga gani acikin damuwa yake,
Zama tayi akusa dashi tana mamakin yadda yadamu da ikhlas sosai,
“Barrister naje na lallabata dakyar ta hakura tabar kukan”
“Yawwa ni’ima Allah ya saka miki da alkairi”
“Amin, amma wannan bazai hanamu kaita asibitin ba anjima”
“Ehh ina sane zamuje ai”.
Misalin karfe 5 na yamma suka nufi asibiti,
Asibitin da elmustapha yakai ikhlas lokacin da ya tsintota yanzun ma can ya nufa, kasancewar clinic ne na kudi yasa babu wani dogon layi,likitan elmustapha ya samu yayiwa bayanin duk abubuwan da suke faruwa da kukan da ikhlas take yi kullum dare da rana,
Checking dinta dr yayi amma ba lalurar haukan bace dan haka yagane cewar bacin ran fyaden da akayi matane yake damunta shiyasa take yin wannan kukan,
Bayani yayiwa elmustapha cewar arinka kwantar mata da hankali kullum sannan adaina barinta ita kadai adaki tana zama, zaman kadaicin shine yake haifar mata da tunane tunane har ranta ya baci,
“To amma dr zazzabin dake damunta akullum fa?” Ni’ima ta tambayeshi,
“Wannan ma babu damuwa zan rubuta mata magani yanzu inyaso sai ku rinka bata tana sha, insha Allah zata daina”
“Mungode dr” elmustapha yace dashi bayan dukkaninsu sun mike domin tafiya,
Sai da suka tsaya awani chemist suka sai mata magungunan sannan suka nufi gida, yanzu kam ta dan saki ranta da zuciyarta ta dan rage damuwar dake addabarta, koda suka koma gidan ma bin ni’ima kitchen tayi ta taimaka mata suka shirya abincin dare sunayi suna hira har suka kammala.
Haka zamansu ya kasance tare kullum elmustapha yana kokarin yiwa ikhlas abubuwan da zasu sanyata farin ciki danma wani lokacin yana tsoron idon ni’ima domin babu wuya ta tayar masa da daru, kullum cikin fita dasu wuraren hutawa yake, musamman ma da ya fahimci cewar ita ikhlas ma’abociyar son irin wadannan wuraren ce, amma har yau bai sake yimata maganar danginta ba tunda ya fahimci bata son maganar asalima duk ranar da yayi mata maganar to wuni zatayi tana kuka.
Haka zamanta yaci gaba da tafiya acikin gidan, kullum elmustapha cikin yi mata hidima yake kamar ya goyata dan kulawa hakan ya sa ni’ima fara canjawa ikhlas fuska domin ita ta tsani duk wata wacce zata yi kokarin rabar mijinta.
Yau ta kama ranar lahdi elmustapha yana gida baije ko ina ba, misalin karfe 10 nasafe yana zaune afalon gidan yana karanta jaridar weekly trust, ikhlas ce tafito sanye cikin doguwar riga Arabian gown wacce elmustapha yasai mata lokacin da ya siyo mata kaya,
“Kai kadaine azaune?” Tafada tana dan murmushi,
Dago kanshi yayi yana kallonta, ba karamin kyau tayi masa ba komai nata das das kamar ita ta tsara halittarta,
“Ni kadaine sai ko ke da zaki tayani zama”
Murmushi tayi ta zauna akujerar dake fuskantarsa,
“Ina anty ni’ima?”. Ta tambayeshi sai dai ko rufe bakinta batayi ba ni’ima tafito daga cikin kitchen a fusace hannunta rikeda cup guda biyu, tun daga nesa ikhlas ta fahimci sauyin fuskar da ni’iman tayi, ahankali ta sauke kwayar idonta kasa.

WhatsApp: 08161892123

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.