RUWAN KASHE GOBARA! 14

0 139

_14_

Fuska babu walwala ni’ima ta wuceta ta karasa wurin elmustapha ta mika masa cup din hannunta tana harararsa kasa kasa,
Cup din ya karba yayinda ita kuma ta zauna akusa dashi tafara kurbar furar da ta damo musu,
“Inata ikhlas?” Yace da ita yana kallonta,
Kallonshi itama take yi aharzuke cikeda masifa akan fuskarta,
“Kamar ya? Ita bata da hannu ne ko kuma bata da kafa da har sai nakawo mata tana zaune? Wai ni baiwa aka daukeni ne agidan nan ko yaya?”
Dauke kanshi yayi ya juya ga ikhlas wacce take zaune jugum tana saurarensu,
“Ikhlas kije kitchen ki zubo fura da nono tana nan acikin fridge”
Girgiza kai tayi “a’a bazan sha ba”
Tana gama fadin haka tamike ta nufi daki tana sharar kwalla, ya zama dole ta tattara tabar gidannan domin zamanta agidan zai haifar da rashin zaman lafiya tsakanin wadannan ma’auratan,
Tana zaune tana kuka elmustapha ya shigo cikin dakin,
“Ikhlas kiyi hakuri kinji”
Daga kanta tayi tana kallonsa, batare da tace komai ba, har ya karaci bata hakurin yatashi yafita batace komai ba, yana fita yaga ni’ima tsaye abakin kofa tana kallonsu cikeda takaici,
Wuceta yayi bai tanka mata ba hakan ya sake kular da ita, key din motarshi ya dauka yafice daga cikin gidan yabar ni’ima tana zancen zuci,
“Shiyasa kawayena da yan uwa suketa bani shawara kan kar nasake nayarda nabar yarinyar nan agidan nan gashi yanzu tun ba aje ko inaba nafara ganin sakamako wlh bazai yiyuba dole sai tabar gidan nan”
Mikewa tayi tafice daga falon ta nufi farfajiyar gidan taje ta zauna.
Kuka sosai ikhlas ta keta yi har tsawon wani lokaci,tana nan zaune sai taga rashin dacewar zaman dakin alhalin kuma gidan nan ba nasu bane, toilet ta shiga taje ta wanke fuskarta tafito tafita falo, ni’ima tasamu mike kan doguwar kujera tana kallon wani american film _50 ways to kill your mammy_ a kujerar kusa da ita ta zauna,
“Sannu anty ni’ima”
“Yawwa sannu ikhlas, kin gaji da zaman dakin kin fito?”
“Wallahi” ikhlas tafada cikin yake, babu wanda yasake magana acikinsu har elmustapha ya shigo,
Mikewa ni’ima tayi ta tareshi da murna cikin kissa,amma shikuma duk hankalinsa yana kan ikhlas domin ya ganta wani jugum,
“Ikhlas ga kayan makulashe nataho muku dashi” yafada cikeda fara’a akan fuskarshi, hakanne ya sa ni’ima sakinshi takoma gefe tana kallon ikon Allah,
Da kanshi ya dibarwa ikhlas dukkanin kayan da ya shigo dashi ya mika mata, ya dauki sauran yakama hannun ni’ima zuwa dakin baccinshi,
Kayan tafara bi da kallo, su chocolates ne manya kala kala harda takarcen cheeze sai kace wasu yara,
Murmushi tayi tana yaba kirki da kuma adalci irin na elmustapha domin duk abinda ya siyo agidan to itama sai ya bata nata, ko matarsa ya saiwa abu itama sai ya siya mata.
Kayan ta diba ta nufi dakin ni’ima dasu. Aranar da daddare suna zazzaune yatashi yafita zuwa wurin motarsa ya dawo hannunsa dauke da bakar leda,
Lesuka ne guda biyu masu kyau ya siyo musu iri daya ai nanfa ni’ima ta tada masifa,
“Wlhi bazai yiyuba yau sai kafada min idan matsayina dana wannan yarinyar dayane awurinka, haba nagaji nagama gajiya da wannan cin fuskar da kuke yimin acikin gidannan”
“Menene haka ni’ima?” Ya tambayeta cikeda mamaki,
“Oho muku, ban sani ba, wannan abun da kakeyi ni ban san ma’anarsa ba, ka kawo min yarinya gida ka ajiyeta ban san alakarku da ita ba, banida da dangantaka da ita, wallahi bazai yiyu ba, idan kishiyata ce ya kamata ka fito fili ka fada min”
“Ni’ima ki cire kowanne irin zargi acikin ranki”
“Was? Walhi bazai yiyuba haka kawai ka dauko yarinya ka kawo min tahanani sakewa agidana, komai tare kake yimana sai kace wasu kishiyoyi, wallahi sai tabar gidannan adaren nan bazata sake kwanar min agida ba..”
Cikin fada shima ya mike “dayake gidan nakine ko? Kece kika gina min gidan da har kike tutiya dashi? Babu inda zataje sai dai idan kece zaki bar gidan”
“Babu inda zanje amma ita wlhi sai tabar gidan nan”
Mikewa ikhlas tayi tafada daki da sauri, hijabi kawai ta dauko wanda elmustapha ya sai mata amma baya dashi bata dauki komai ba,
Wurinsu takoma tana kuka hawaye fal kuncinta,
“Anty ni’ima nagode da taimakon da kuka yimin keda mijinki, sannan ina mai baki hakuri sanadiyyar fadan da nake hadaku keda mijinki, kiyi hakuri zan bar miki gidanki acikin daren nan basai gari ya wayeba”
Rike kugu ni’ima tayi ta dauke kai, “babu inda zakije, anan zaki ci gaba da zama har sai idan kece kika gaji da zaman dan kanki” elmustapha yafada cikin fushi,
“Wlh bazata zauna ba, muddin zata zauna agidan nan to ni bazan zauna ba,sai tabar gidan nan idan bata da dangi akwai gidan gajiyayyu tatafi can mana”
Ita dai ikhlas bata sake magana ba tayi hanyar waje tana tafe tana kuka.

https://arewarulers.com/sitemap.xml
No Comments
  1. smart hub says

    nice

Leave A Reply

Your email address will not be published.