RUWAN KASHE GOBARA! 16

0 167

_16_

Kujerar da yake kai ya kwantar ya mike yana tunata acikin ranshi, har yanzu yakasa mancewa da ita haka kuma ya kasa mancewa da yanayin da ya tsinci kansa aciki lokacin da ya keta mata mutuncinta,
Wani kunci yaji yana shigarsa sakamakon tunowa da yayi da maganar da me shagon nan yafada masa cewar may be saceta akayi,
“To asaceta akaita ina? Mtsww Allah yasa ba haka bane,kai karyane ma wlh”
Zaune yatashi yana bubbude lumsassun idanuwanshi,
Shigowar kiran bash cikin wayarsa ne yasashi karkacewa ya zaro wayar yana duban kan screen din,
“Hello bash” yace ahankali,
“On top ya” bash yabashi amsa daga dayan bangaren,
“Bash ka ganni akusa da plaza dinnan ta bakin kasuwa dan Allah kazo ka sameni awurin”
“Ok bari nazo”
Kashe wayar yayi yana mai duban hanya sai yan waige waige yake yi wai ko Allah zaisa yaganta,
Sabuwar reza ya ciro daga wani dan akwati wanda aka tanada acikin motar domin yin ajiya,
“I Luv you pretty” ya furta ahankali gamida bude rezar, hannun shi nadama ya samu yafara tsagawa yana rubuta ‘pretty’ tuni jini yafara fita daga jikin fatarsa yana sauka akan jeans din dake jikinsa,
Runtse idonshi yayi,ahankali ya budesu sakamakon jin shigowar bash cikin motar,
Kallonshi bash ya danyi idonsa jajur kamar gauta ga jini kuma yana fita a hannunsa,
“Lamido menene haka” ya tambayeshi atsorace,
“Bash narasata, wlhi ina sonta, ita kadai ce macen da nake so, bash ka tayani nemanta domin ta tafi da farin cikina,bash ina sonta, i love her soo much,ina ji ajikina kamar i can’t survive with out her, she’s part of my life, pls bash ka taimakeni na nemota”
Tunda yafara wadannan sumbatun kallonsa kawai bash yake yana tausaya masa domin da alama ya dan zautu kadan akan wannan mahaukaciyar,
“Ya isa haka Lamido,insha Allahu zaka sameta amma kuma yakamata ka cireta daga cikin ranka because may be you will not meet her again, so kaga karka jawowa kanka damuwa and nikuma nama rasa ta yadda akayi yarinyar ta shiga ranka haka farat daya”
“Bash nikaina ban san yadda akayi ba, banida masaniyar tayaya nafara sonta sai dai wlhi bash ina jin sonta acikin ruhina fiyeda tunaninka, she’s very beautiful and amazing, bash rashin samun yarinyar nan atare dani wlhi kamar rashin samun rayuwata ne I love her..!”
Dafashi bash yayi cikeda tausayawa aranshi yana mamakin wai Lamido shi dayake wulakanta mata yau gashi kuma yashiga wani hali akan wata, watanma mahaukaciya,
“Lamido tun farko kaine ka jawowa kanka wannan matsalar, tun farko kaine kayi sakaci har sonta ya ratsaka gashi yanzu kashiga wani hali, ni ina ganin ka daure ka cireta daga ranka, ga yanmata nan hadaddu classic bebs da yawa masu sonka”
“No bash, i can’t, wallahi bazan iya ba”
“To shikenan yanzu a ina kake tunanin zaka iya samota,danni wallahi idanma naganta ba lallai naganeta ba”
“Bash zan samota, duk inda naganta zan ganeta domin wlhi aranar da nayi mata fyaden nan fuskarta kawai nake kallo, ban taba ganin mace mai kyau kamarta ba”
“Allah yabaka lafiya abokina dan dama nadade ina zargin cewa da aljana kayi karo wallahi”
“Wallahi ba aljana bace mutumce kamar kowa, yanzu kazo ka tuka mu ka kaini cikin kasuwa layin artists domin ina son azana min hotonta ayanzu”
Murmushi bash yayi amma aransa yagama yarda kawai Lamido gamo yayi da aljana ta zautashi.

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.