RUWAN KASHE GOBARA! 17

0 165

_17_

 Farin handkerchief ya dauka ya nannade wurin da ya yanka ahannun nashi gashi rubutun ya fito rado rado,
Fita yayi sukayi exchanging din wurin zama shida bash, inda shi bash din ya koma wurin zaman driver yajasu suka shiga cikin kasuwa,
Basu sha wahalar samun artist din da zai zanawa Lamido hoton ba, wuri suka samu suka zazzauna Lamido yafara siffantowa mai zanen kamanninta, shidai bash kallon Lamido kawai yake yi yana tausaya masa domin yasan aljana ne yarinyar nan, lallai indai hakane Lamido yayi kuskure da ya dauka RUWAN KASHE GOBARA BA SAI MAI KYAU BA,
Suna nan zaune aka gama zanen, Lamido ya kurawa hoton ido hakika bazai taba iya mantawa da ita ba,
Kudin zanen ya biya ya dauki hoton suka tafi, kai tsaye gidansu Lamido bash ya wuce dasu, fita Lamido yayi ya nufi dakin baccinsa yana zuwa ya ajiye hoton akan bedside drewar dinshi.
Dakin innah ya nufa, itada baffa ya samu suna zazzaune afalo,
Akasa ya zauna ya sunkuyar da kai,
“Barka da hutawa baffa” yafada kansa akasa,
“Yawwa lamido, ina fata dai kana shirye shirye ko? Domin tafiyarka yau saura kwana 6 kuma wannan tafiyar kanka zaka yiwa bani ba, amma duk da haka ina baka shawara da ka zama mutum nagari, ka ajiye wannan shashanci da kake yi, inda zakaje garine wanda babu wanda zai saka babu wanda zai tsawatar maka, ni nayi maka hakane domin kasamu ingantacciyar rayuwa domin acikin sharrudan tuba sauya matsugunni yana ciki ma’ana mutum ya nisanci wurinda yake sabon Allah idan garine to ya sauyashi ya koma wani, shiyasa kaima zan daukeka daga kasar nan in kaika wata domin kayi nesa da abokanai wadanda suke zugaka suna rubzaka izuwa ga halaka”
Tunda aka fara maganar baice komai ba sai sunkuyar da kai da yayi yana shafa sumarsa,
“Kana jina ko?”
“Ina jinka Baffa kuma insha Allah zan kasance kamar yadda kake so”
“Yawwa Allah yayi maka albarka”
“Amin baffa”
Mikewa yayi ya koma dakinsa yana shiga ya zauna agefen gado yana kallon hotonta, daukar hoton yayi ya rungume akirjinsa yana mai fatan Allah yasa yanada rabon ganinta.
Tun daga ranar ya fara duk wani shiri domin barin kasar Nigeria zuwa kasar Kenya,kullum cikin rokon bash yake yi akan ya taimaka ya cigaba da duba masa wannan mahaukaciyar ko bayan tafiyarsa,
Daren ranar da zai tafi yadade azaune yana kallon hotonta ji yake kamar zai rasata Idan yatafi, dakyar yasamu yayi bacci yana rungume da hotonta.
Washe gari da safe iyayensa da yan uwa suka yi masa rakiya zuwa airport domin jirgin karge 9 zai bi zuwa garin Nairobi babban birnin kasar Kenya,
Daidai lokacin da yagama sallama dasu innah ya juya domin tafiya bayan yaja hannun abokinshi bash wanda shima yaje rakiyar,
“Bash dan Allah karka manta da sakon da nabar maka, kayi duk iya kokarinka ka binciko min ita dan Allah, bash nasan kai gani kakeyi kamar ba mutum bace a tunaninka aljana ce, to wlhi ba haka bane pretty mutum ce”
“Karka damu abokina insha Allahu burinka zai cika zaka hadu da ita”
“Allah yasa haka” Lamido yafada yana goge yar kwallar data taru acikin idonshi, hannun bash Yakama suka yi musabaha yajuya yatafi domin anata shelar cewar jirgin yakusa tashi.

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.