RUWAN KASHE GOBARA! 26

0 163

_26_

A gefenta ammi ta zauna tafara matsa mata kafafunta tana cewa,
“Har yanzu kina yin wannan ciwon kafar ne kamar lokacin da kina yarinya?”
“Ammi ciwon kafa kuma?”
“Lokacin da kina yarinya kina yawan yin ciwon kafa dan har asibiti nake kaiki duk azatona sikila ce dake domin alokacin ma abbanki cewa yayi kasar waje zai fitar dake adubaki to kuma har nabar gidan bai fitar dake ba” share Yar kwallar data tarar mata agefen ido tayi bata bari ikhlas din tagani ba,
“Ammi yanzu dai banayi nawarke”
“To ki tashi kiyi wanka da ruwan zafi sai kiji dadin jikinki”
“To ammi ki kyaleni na dan sake hutawa”
“To huta”
Cigaba da matsa mata kafarta ammi tayi har aka fara kiraye kirayen sallar isha,
Sai alokacin ikhlas ta mike tashiga bathroom tayi wanka tafito yanzu jinin dake fita a jikinta ya dan ragu sai dan digo take gani sabanin da wanda kamar an bude fanfo,
Mai ta zauna ta Shafa tana kallon ammi wacce ke salla agefenta,
Wasu riga da wando marassa nauyi ta dauko ta saka ta tashi domin yin sallar isha,
Tana cikin yin sallar ne ta jiyo sallamar yayunta yan biyu, sauri tayi ta sallame ta kwasa zuwa falo,
Kamarsu daya ba ataba banbancesu komai nasu iri dayane gasu kyawawa farare masu hanci, tamkar taje ta rungumesu take ji,
Su dinma tsayawa sukayi suna kallonta,
“Ammi wacece wannan?” Hussain ya tambaya yana kallonta,
“Nima ban santa ba” ammi ta bashi amsa cikin barkwanci,
“Hassan ka ganeta? Ikhlas ce kanwarmu, wallahi itace, kalli gefen goshinta inda ta ji ciwo da scissors lokacin da ammi tana koyon dinki”
“Wallahi itace kam” hassan yafada yana mika mata hannu, hannunsu ta kama tana murmushi sai kuma suka fara kuka gaba dayansu,
Ammi ce tayi karfin halin rarrashinsu har suka hakura sukayi shiru suka shiga hirar yaushe gamo? Sun dade tare suna hira har sai da karfe 2 nadare yayi sannan kowa ya hakura ya nufi makwa cinsa,ita dai ikhlas bayan ammi taje ta rungumeta ahaka bacci yayi awon gaba da ita.
*
Abangaren Lamido kuwa tunda ya tafi kasar Kenya kullum cikin damun bash yake awaya ko ya gane masa pretty dinshi, amma koda yaushe amsar bash guda dayace,
“Ban ganta ba ni nama manta kamanninta”
Dafe kai Lamido yayi yana tunaninta acikin zuciyarsa shidai yasan ko zai manta wata ya mace to banda pretty domin tazama wani sashe na rayuwarsa,
Tsoron Baffa ne kawai ya hanashi dawowa gida domin yace bai yarda yazo gida ba har sai ya gama karatunsa wato shekaru uku kenan, dakyar ya samu yayi masa sassauci ya yarda yazo ganin gida idan yayi shekaru biyu acan,
“Pretty a ina zan dada ganinki? Idanuwana suna son ganinki koda kuwa acikin mafarkine, pretty wallahi ina sonki”
Kullum haka yake furtawa tamkar wani zararre hakanne ma yasa bash gama yarda da cewar Lamido ya samu tab’i a brain dinshi kuma ita wannan mahaukaciyar ba mutum bace aljana ce.
Wayarshi ya jawo yashiga kiran bash dama video call suke yi akullum,
“On top ya?” Bash yace dashi yana murmushi,
“Bash kasan dai maganar gizo kullum bata wuce ta koki, dan Allah bash ka taimakeni, wallahi ni idan nadawo gida yanzu raina in yayi dubu sai ya baci kasan dai irin fadan Baffa musamman ma akaina, nafi kowa laifi agidan nan”
“Lamido magana ta gaskiya wannan yarinyar ba sake ganinta zakayi ba dan haka kacire ran kara sake haduwa da ita acikin rayuwarka?”
“Dan Allah dakata min, waye ya fada maka bazan sake ganinta ba?” Lamido yafada azuciye domin shi mutumne mai zuciya da zafin rai,
“Saboda aljana ce, Lamido ko kaso ko ka ki wallahi sai nafada maka gaskiya, wannan yarinyar aljanace kawai ta zautar da kai ne,in banda haka tayaya daga haduwa da ita sau daya zaka mace asonta har kana ikirarin ka tsani kowacce mace sai ita kadai kake so”
“Kaga malam da Allah kar ka bata min rai, sai anjima”
Katse wayar Lamido yayi yana tsaki ransa duk yagama baci sam baya son yaji bash ya kira pretty da aljana saboda shi yasan ba aljana bace mutumce sannan shi kansa yana son ya cireta daga cikin zuciyar tasa amma hakan yaki yiyuwa domin tagama mamaye dukkan sansan hanyoyin jinin jikinsa.

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.