RUWAN KASHE GOBARA! 27

0 190

_27_

Kullum Lamido cikin tunanin prettyn shi yake duk yabi ya zauce domin shi kadai idan yana zaune sai kaji yana magana ahankali,
“Pretty dan Allah ki sake bayyana agareni wallahi ina sonki, wai baki san yanda sonki yake neman illata rayuwata bane”
Kullum cikin fadin haka yake gashi da farin jinin yanmata duk inda ya shiga mata na sonshi suna bibiyarshi amma wani lokacin yakan tuna hudubar bsffanshi wacce yayi masa lokacin da zai bar gida kan ya kula da kansa ya daina yawon bin mata ya daina shan kodin, hakan da yake tunowa ne wani lokacin sai yaji jikinsa yayi sanyi.
Haka lokaci yaci gaba da tafiya batare da Lamido yaji labarin pretty ba kamar yadda yake kiranta, kullum bash shawara yake bashi akan yayi hakuri ya cire yarinyar nan daga cikin zuciyarsa amma ya gagara, wani lokacin idan ya zauna shi kadai a bedroom dinsa sai ya dauko hotonta ya zuba mata ido yana kallon kyakkyawar surarta, Allah ya bata duk wata cikakkiyar sura da ake bukata awurin ya mace amma kuma sai ya gusar da hankalinta,
Tsintar kansa kawai yayi yana mai zubar mata da hawayen tausayi,
“Pretty da ace Allah zai sake hadani dake da zan aureki ahaka zan nuna miki gatan da ba ataba nunawa wata ya mace ba afadin duniyar nan kamar yadda SULTAN ya nunawa fatinshi, wallahi da sai kin zama tauraruwa acikin mata fiyeda yadda Lamin ya mayar da Junada acikin MACE GUDA DAYA TILO, zan soki ahaka zan rayu dake ahaka kuma zan nuna miki soyayya ahaka fin wacce umar faruk ya nunawa KAUSAR YAR AUTAR MATA,da sai kin zama abar kwatance kamar yadda jawad ya mayar da pherty acikin MARTABA TA,ke kadaice matar da naji ina son kasancewa da ita samada yadda Awwab ya kasance da Nihal cikin KWARYA TABI KWARYA, soyayyar da nake miki tafi wacce Hakeem yayiwa Ayshanshi cikin BIYAYYAR IYAYE, zan baki kulawa irin wacce Junior ya bawa jiddanshi cikin SANADIN GATA, domin na tabbatar ke bakiyi kamada Muhibbat din Yasir ba ta cikin AURE YAKIN MATA, tabbas kin fi sameenat iya tarairayar miji domin ita tsabagen sakacinta yasa zaid auro mata yar aikinta acikin RUWAN DARE, kullum addu’a ta Allah ya mallaka min ke na rayu dake kwatankwacin yadda Abbu ya rayu da bintinshi cikin WANI HASKE hakika kema haske ce agareni pretty”
Yafada yana share kwallar idonshi, haka rayuwarshi taci gaba da kasancewa har ya shafe kwanaki masu yawa a kasar Kenya, alokacin ya dan rage surutai akan pretty amma kuma sonta da kaunarta yana nan makale acan kasan zuciyarsa, gashi yaci gaba da hallayarshi ta shan kodin domin anashi ganin hakane kadai hanyar da zaibi wurin rage damuwar dake addabarshi, neman mata kuwa ba koda yaushe yake yiba sai dan jifa jifa amma wani abu da bai sani ba shine duk wadannan abubuwan da yake yi ana sanar da baffansa domin dama ya baza c.I.d akansa.
*
Tunda ikhlas ta koma wurin mahaifiyarta ta tsinci kanta acikin rayuwa mai dadi, kullum cikin tarairayarta ammi take itada yayunta da duk sauran mutanen gidan ga kakarta mahaifiyar ammi itama kullum suna tare Suna tsokanar juna irin wasan jika da kaka dan haka tuni ikhlas ta manta da wata aba wai ita damuwa, nan da nan ramar da tayi ta bace ta ciko tayi bul da ita.
Yau satinta uku da zuwa Suna zazzaune acikin falon ammi itada da yayunta hassan da Hussain da ammi, hira suke yi sosai ammi tana basu labarin irin rayuwar da suka yi da mahaifinsu da kuma uwar mijinta da kishiyarta har kawo sanadin data baro gidan,
Dukanninsu babu wanda bai ji tausayin ammi ba, kallon ikhlas ammi tayi,
“Ke kuma wacce irin rayuwa kikayi dasu? Dan nasan yakumbo bata kaunar jinina bazata taba sonki ba”
“Hakane ammi hakika yakumbo bata kaunarmu abbanmu kadai take so ban taba ganin uwar da take son danta amma bata son jininsa ba sai akan yakumbo…!”. Labarin irin rayuwar da tayi tashiga sanar dasu har haukan da tayi da kuma abinda ya faru wanda yayi sanadiyyar tahowarta wurin ammi,
Kuka ammi take sosai, hankalinta idan yayi Dubu to duk ya baci, ba ita ba harta hassan da Hussain ma labarin ya girgizasu amma duk abinda yafi firgata su shine jin wai ikhlas tana dauke da juna biyu ahalin yanzu har na tsawon wata biyar.
“Ammi kiyi hakuri ki daina kuka,mu taru mu nemo mafuta acikin wannan al’amari kawai” Hussain yace da ita,
“Hussain wacce mafita kuma, nidai yakumbo da Nafi sun gama cutata kuma in Allah ya yarda sai Allah yayi min sakayya” ammi tafada cikin kuka,
“Ni anawa ganin idan dare yayi kawai mu dauki ikhlas mu kaita private hospital azubar da cikin nan domin wlhi haifeshi babbar tawayace acikin rayuwarta, idan ta haifi cikin nan mijin aure ma sai ta rasa” inji Hussain,
“A’a hussain, gaskiya wannan ba shawara bace saboda karfa muje garin gyaran gira mu rasa ido, ina nufin kar muje garin zubar da cikin nan mu rasata gaba daya” hassan yafada,
“To kana nufin barinta zamuyi ta haifi dan shege?” Hussain yafada cikin kufula domin dama shi mutumne marar hakuri ga zuciyar tsiya hassan yafishi hakuri,
“To akanta aka fara? Ba kaddara bace?” Hassan yabashi amsa,
“To wlhi bazai yiyuba bazata Haifi dan shege ba balle azo ana nunata da baki kuma shima dan azo ana yi masa gorin uba wata rana” hussain yafada yana huci,
“Yaya hussain dan Allah kar ku kaini wurin zubar da cikin nan wallahi zan iya mutuwa dan bakuga wahalar dana sha bane a Zaria lokacin da abba yasa azubar da cikin” ikhlas tafara rokonsa tana kuka,
Tashi hussain yayi afusace “zan tattakaki idan kika sake magana, haka kikeso mu zuba ido muna ji muna gani rayuwarki ta samu nakasa? Banza shashasha ana son ayi miki gata kina bujirewa”
Ammi na zaune tana kallonsu har lokacin bata iya cewa ko uffan ba.

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.