RUWAN KASHE GOBARA! 29

0 154

_29_

Kuka taci gaba dayi ko kallon inda jaririn yake ba tayi ba,
Kawo mata jaririn nurses din suka yi suna ta yaba kyansa,
“Maman boy ga yaronki, kyakkyawa mai koshin lafiya gashi big” daya daga cikin nurses din tafada,
Bata jiyo ba kuma batayi magana ba sai uban kuka take yi marar sauti, agefenta suka kwantar mata dashi domin duk azatonsu bacci take yi kasancewar anyi mata allurar bacci,
Tana jinsu suka fita daga cikin dakin da take sunata yaba kyawun jaririn, har bacci ya dauketa bata juya ta kalli yaron ba tana jinsa dai yanata mutsul mutsul a inda aka kwantar dashi.
Baccin awa biyu tayi ta tashi lokacin jaririn yana kuka, bata juya ba amma tana jin kukan har cikin ranta,
Wata nurse ce ta shigo da Sauri tana tambayarta,
“Maman boy baki tashi bane? Ki tashi ki bawa boy abinci”
Kin juyowa tayi tai shiru hakan da tayi ya sanya nurse din tabata tana girgizata amma fur taki motsawa, suna cikin wannan dramar su ammi suka shigo itada hajiya da hussain,
“Yawwa gwanda da kuka zo, maman boy taki bawa jariri nono” nurse tace dasu tana kokarin fita daga cikin dakin,
“Haba ikhlas ya za ayi ki hana danki nono? Menene amfanin hakan?” Inji hajiya ta fada tana kokarin daukar yaron,
“Rashin hankali mana in banda rashin hankali shi jariri ina ruwansa yasanma abinda ya faru da har zaki huce akanshi?” Ammi tafada cikin fada,
Jin haka yasa ikhlas rushewa da wani sabon kukan mai sauti,
Rarrashinta hajiya da ammi suka fara yi,
“Yi hakuri ikhlas kinji, kika yi juriyar rainon cikinsa ma har kika haifeshi balle shayar dashi, kiyi hakuri ki karasa ladanki kinji” ammi tace da ita tareda dafa kafadarta,
“Ammi ban son ganinsa dan Allah kuje ku kaishi gidan marayu ko ku yar dashi..” Tafada tana kuka,
“A’a ikhlas ko daya ba za ayi haka ba, dayawa daga cikin yaran da suke tasowa babu tarbiya babu tausayi a zukatansu to wadanda akayi cikinsu aka kasa daukar kaddara aka jefar dasu ne, kuma da ace za arinka yin hakuri ana rungumar yaran ana basu kulawa to da sai kiga kilama sun zama silar taimakon addinin Allah” ammi tabata amsa tana kallonta cikeda tausayawa,
“Gashi kuwa kamar balarabe sai uban dogon hanci kamar in cire in kara anawa” hajiya tafada cikin barkwanci,
Ganin taki dagowa ya sanya hussain daka mata tsawa domin dama kawai ya tsaya yana kallonsu ne yaga iya gudun ruwanta,
“Ke….! Tashi ki karbeshi ki bashi nono ko nazo nayi bol dake, tashi nace”
Tashi tayi tana kuka har lokacin bata daina ba,
“Yi mata ahankali yan biyu, ai zata tashi” hajiya ta katseshi,
“Bazaki karbeshi ba, hajiya mika mata shi, karbeshi, banza shashasha, wannan wanne irin shirmene? Akansa zaki huce kome? Kefa kikace kin dauki kaddara to kuma sai ki gajiya tun daga yanzu?” Matsawa yayi kusa da ita ya sassauta murya,
“Nasan abinda kike yiwa kuka, tsoro kike kar ya girma ya tambayeki waye babanshi ko? To ni dinnan ni Hussain nine ubansa, zan zame masa gata zan reneshi tamkar dan da na haifa jinina, in dai ina raye to yaronki bazai taba kukan rashin uba ba nayi miki alqawari, ki saki ranki ki kwantar da hankalinki, ki kula da danki daga nan har zuwa lokacin da zaki yayeshi, zan dauki nauyin komai nasa na rayuwa nayi alkawari”
Dakyar ta mika hannu ta karbeshi daga hannun hajiya tana kuka tadorashi akan cinyarta tana kallonsa, hakika tasan ita kyakkyawa ce ta asali to amma bata taba ganin kyau irin na wannan yaron ba, yaro kamar ba’indiye, sumar kanshi kadai abar kallo ce gata sinkif ta sauko har goshinsa takusa rufe masa ido,
Feeding dinshi tafara yi amma ta daina kukan da take yi, zubawa yaron ido tayi tana jin wani irin sonshi yana ratsata,
“Wanne suna kike son asa masa?” Hussain ya tambayeta,
“Yaya da niyyata asaka masa ABDALLAH” tafada tana share kwallar idonta,
“Hakan ma yayi, bari naje na dawo”
Tare da ammi suka fita suka barta da hajiya,
Tunda ya kama nonon yana sha take kallonsa, lallai Allah babu yanda bai iyaba, kalli yaro kato dashi mai koshin lafiya, amma babu uba yanzu wasu ma’auratan kuma suna can sukuma suna neman haihuwar ido rufe amma basu samu ba,
Sai da yasha ya koshi sannan ta mikawa hajiya shi ta koma ta kwanta.
Ammi ce tadawo dauke da kaya niki niki su flasks din ruwan zafine dana abinci da kayan tea da sauran kayan bukata,
Take aka shirya jariri cikin kayan sa riga da wando farare sol,
Abinci ammi ta zuba mata ta hada mata tea mai kauri ta bata, tana gama ci ta koma ta kwanta, nan asibitin yafara karbar bakuncin yan gida domin duk sunzo ganin jariri, duk wanda ya karbeshi sai ya yaba kyansa dan haka ta dauri aniyar zata rinka yi masa addu’ar maganin baki.

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.