RUWAN KASHE GOBARA! 3

0 207

_3_

Wata irin faduwar gabace ta addabi zuciyar Lamido gashi zazzabin jikinsa ya tsananta tamkar wanda ake karawa,
“On top yarinyar nan fa bata nan may be tayi wani wurin” bash yace dashi yana kallonshi,
Fuskarshi ya yamutsa wanda take kumatunsa suka lotsa ya tashi daga dan kwanciyar da yayi ya juyo yana kallon bash,
“Bash bari na leka waje ko wancan kangon ta koma” Lamido yafada yana kokarin bude kofa,
Rikoshi bash yayi yace “haba Lamido da wannan ruwan zaka fita alhalin kuma kace zazzabi kake ji”
“Bari nadubo kawai” Lamido ya fada atakaice ya bude kofar motar yayi waje ruwa yana dukansa, kangon da yakaita dazu ya hara amma koda yaje babu alamun mutum aciki haka ya dawo yanata dube dube ruwan sama kuwa sai laftarshi yake yi,
Cikin motar ya koma duk yagama jikewa nan sanyi yace muje zuwa, kakkarwar sanyi ya shiga yi sosai tamkar mazari,cikin rawar murya yace,
“Bash dan Allah muje mu dan dudduba hanya ko tafiya tayi”
Batare da bash yayi magana ba yafigi motar suka tafi amma har sukayi tafiya mai nisa titin babu kowa hatta abin hawan dake wucewa ma tsilla tsilla ne saboda dare yayi,
“Kaga Lamido yarinyar nan ba ganinta za muyi ba kawai mu hakura mu tafi gida”
Kada kai Lamido yayi yana rawar sanyi yabi duk ya kankame jikinshi, heather bash ya kunna acikin motar take motar ta dumame da dumi amma Lamido shidai har lokacin kakkarwar sanyi yake yi.
Misalin karfe 12:00 suka isa gidansu Lamido, har barandar side din Lamido bash ya kaishi sannan ya fita ya tafi da motar zuwa gida,
Yana tafiya yana dafa bango har ya shiga bedroom dinshi wanda yasha kyawawan furnitures komai agyare limbis, heather ya kunna ya cire rigar jikinshi da jeans dinshi ya saka kayan sanyi riga da wando red colour masu layi layin blue ajiki,
Kan katon gadonshi yaje ya kwanta ya lulluba da bargo nan kuma yafara tunanin mahaukaciyar dazu, hannuwanshi yafara shafawa sai radadi wurin data yakusheshi yake yi, wurin yayita bi yana tabawa har su wuyanshi duk ta daddaye masa fata,tausayinta yaji yana shigarshi,
“Yanzu shikenan yarinyar nan narabata da darajarta wacce Allah ya halicceta da ita, na cuceta gaskiya, na rabata da abinda yafi komai daraja awurinta kuma ba acikin hayyacinta ba” yafadi hakan acikin ranshi,
Juyawa yayi ya rungume pillow yana tuno kyawun surarta domin bata da maraba da buzuwa duk yadda akayi ta hada iri da buzaye domin tun daga kan gashin kanta har zuwa hasken fatarta duk irin na buzaye ne, ko daga wanne gari tazo nan oho Allah ne kadai yasan daidai.
Kasa bacci Lamido yayi sai wani uban zazzabi da ya rufeshi take yafara fitar da numfashi mai dumi, yana cikin wannan halin har asuba tayi bai iya tashi ba sai lokacin ya samu bacci ya daukeshi.
Har 9 lamido yana kwance adaki yana bacci jikinsa zafi zau da zazzabi,
Cikin bacci yaji ana tashinshi,
“Lamido, Lamido!”
Ahankali ya bude idonshi, mahaifiyarshi ya gani tsaye tana dubanshi,
“Innah,karfe nawa yanzu?” Yafada yana kokarin tashi amma jiri yake ji sosai,
“Yanzu karfe 10 Lamido, baffanka yana jiranka shiru baka zo ba”
Komawa yayi ya kwanta, “innah banida lafiya zazzabi nake yi” yafada yana yamutsa fuskarshi,
“Shiyasa fa naji jikinka da zafi, sannu bari naje na fada masa”
Tashi tayi ta fita yana ganin fitarta ya dauki wayarshi ya soma kiran bash, yana dagawa yafara yi masa magiya,
“Bash dan Allah kaje ka dubo min wannan yarinyar, wallahi jiya da ita na kwana araina”
“Wai meyasa ka damu da yarinyar nan ne? Haba Lamido dan Allah ka manta da ita tunda ka rigada ka samu abinda ka nema agareta, shikenan kawai awuce wurin”
“What?” Lamido yafada cikin daga murya,
“Haba bash idan nayi haka wallahi Allah bazai barni ba, dole ne na nemo yarinyar nan na nemar mata lafiya nabata dukkan farin ciki na rayuwa”
“To Allah yasa asameta” bash yace dashi,
“Amin, idan zaka zo ka taho min da kodin, dan Allah bash kayi dukkan kokarinka ka nemo min yarinyar nan ayau”
Kashe wayar yayi yafara neman number din wani likita wanda ya kasance abokinshi,
Yana dauka yafara yi masa bayanin yanada marar lafiya mai tabin hankali yana son ya hadashi da likitan mahaukata domin samar mata magani,
“Babu damuwa akwai dr na mahaukata yana zuwa duk ranar Thursday kuma kwararre ne insha Allah za adace”
Likitan yabashi amsa ta cikin wayar.

WhastApp: 08161892123

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.