RUWAN KASHE GOBARA! 30

0 282

_30_

Da wannan tunanin tayi bacci ba ita ta farka ba sai misalin karfe 3 narana, lokacin data tashi hajiya ce kawai adakin tana kishingide itama tana dan baccin,
Gefenta ta kalla jarinrinta ne kwance shima amma kuma rabi ajikinta yake, hular kanshi tafara gyara masa tana kallon fuskarsa, idanuwansa manyane domin kusan ma sunfi nata girma,
“Abdallah” tafada ahankali,
Turo kofar dakin akayi aka shigo ammice da yayanta hassan suka shigo dauke da kaya,
Farfesun kajine ammi ta iyo mata ga kuma kayan marmari cikin yeluwar leda,
“Tunda kin tashi ai sai kici abincin ko?” Ammi tace da ita tana kokarin zuba mata farfesun,
“Woww,fine boy” hassan yafada lokacin da ya dauki yaron,
“Wannan yaron ai yafi uwarshi kyau” hassan ya sake fada,
“Ni cewa ma nayi zan cire hancinsa na lika anawa” hajiya dake kishingide agefe tafada tana dariya,
“To hajiya Kodai kina kamune?” Hassan ya tambayeta cikin zolaya,
Ita dai ikhlas tana zaune tana saurarensu tana cin farfesunta amma acikin ranta tana jin yan uwanta da mahaifiyarta sun gama yimata komai aduniya domin su basu koreta ba kamar yadda mahaifinta yayi mata afarko,gashi kowa sai murna yake da raha babu wanda zai ce danta bashida uba sai wanda ya sani.
Karfe 8 nadare aka sallamesu zuwa gida domin daga ita har babyn lafiyarsu lau babu wata matsala,
Suna isa gida ta samu kaya kaca kaca wanda yayunta suka siyo mata itada jaririnta alhalin kuma kafin ta haihu ma sun siyo mata wani.
Kula da ita ammi tafara yi itada abdallah har ranar radin suna anan aka radawa yaro suna abdallah, raguna biyu manya yayyunta suka siyo aka yankawa jaririn,
Komai awadace babu abinda ikhlas take nema ta rasa komai yayunta suna yi mata, irin kulawar da suke samuce tasaka yaron saurin girma, lokacin da sukayi arba’in kamar yayi wata biyu,
Ita kanta ikhlas din ta dan murmure tayi kalau fes da ita, hussain da hassan kullum cikin siyowa abdallah kayan sawa da kayan wasa suke yi daidai da rana daya basu taba kyamatarsa ba, haka sauran mutanen gidanma daga hannun wannan ya koma hannun wannan kasancewar babban gidane wuni zaiyi bata ganshi ba harma abin ya zame mata sabo,wani lokacin idan ammi tana tambayar ina abdallah sai tace,
“Ammi ni ina zan san inda yake? Kila yana kofar hajiya”
“Kullum dai ahaka kuke sai yabata agidan watarana” ammi tafada cikin wasa,
Dariya kawai ikhlas tayi,alokacin kuma barrister elmustapha ya fado mata domin rabonta dashi tun tana Zaria yanzu kuma ta sake sabon sim da sabuwar waya dan haka ta kirashi suka gaisa suka dan taba hira har yake sanar da ita ni’ima ta haihu watanni biyar da suka wuce sunan yarinyar ikhlas, murna tayi sosai tayi musu Allah ya raya, hakika ita kanta tasan elmustapha yana sonta to amma kuma ita bazata iya aurensa ba karewar so ma gashi har sunata ya sanyawa yarshi.
Rayuwarta haka taci gaba da tafiya cikin kwanciyar hankali har abdallah ya cika wata goma lokacin yana yawonsa ko ina ga dankaren surutu shiyasa ta yayeshi, gashi yaron yana tsananin sonta koda yaushe yana makale ajikinta idan kuwa bai ganta ba to tamkar marar lafiya haka zai zama shiyasa itama bata nisa dashi kullum tana manne dashi, kayan wasanshi kuwa sai kace kamfani domin su hussain kullum cikin siyo masa suke,
Lokuta da dama sai ta zubawa abdallahn ido tayi ta kallonsa,yaron kama yake yi mata da larabawa wani lokacin ma har tambayar kanta take kodai balarabe ne yayi mata fyaden domin kyawun abdallah yayi yawa hatta hasken fatarshi ba irin nata bane yafita fari sosai domin shi har wani yellow yellow yake yi,
Dafarko kafin yayi wayo tana zama ta kunshe kanta adaki tayita kuka amma tunda yayi wayo sai ta daina domin akwai lokacin da yaganta tana kukan, jikinta yaje ya fada shima yafara kuka yana kankameta,
“Anty waye ya daceci kike kuka” shine tambayar da yayita yi mata shima yana kuka, rarrashin duniyar nan tayi masa akan yayi shiru amma yaki sanadiyyar kukan da yayi har zazzabi yayi ranar, tunda taga haka sai ta hakura ta daina kukan ta fawwalawa Allah lamarinta, sannan ta rungumi danta domin soyayya take nuna masa ako ina kuma agaban kowa har hajiya tana tsokanarta tana cewa ta futsare santa bata alkunya,
Ko bacci take yi da rana haka abdallah zai zo ya shige jikinta tare zasu yi baccin idan bathroom ta shiga to kofar bathroom din zai je ya tsaya yana gadinta har tafito, iya shakuwa sun shaku sosai,
Yanzu shirye shiryen bikin hassan da hussain yayunta suka fara yi wata mai zuwa,kudi mai yawa suka bata sukace tayi siyayyar hidimar biki ita da danta.
*
Lamido lamarinsa kullum sake ta’azzara yake yi domin babu abinda ya rage acikin halayyarsa, kullum cikin shan kodin yake da kula mata ganin abin yana nema yayi yawa ya sanya baffanshi shawartar inna cewar zai yiwa Lamido aure kwanan nan amma ya tagani, itama goyon baya tayi,dan haka Baffa ya kira bash yake tambayarsa wacce yarinya ce Lamido yake so bash yace su biyune akwai fadila akwai kuma ihsan kuma duk yan matansa ne tun kafin yabar kasar,
Bin gidajensu yaran Baffa yayi duk ya nemarwa Lamido aurensu aka saka ranar biki watanni biyu kacal (kaji Lamido dan gata, mata biyu alokaci daya),shi Lamido yana can Kenya bai san abinda ke faruwaba gashi kullum sai sunyi waya da yan gida amma babu wanda ya fada masa shirin da akeyi akansa ko bash bai sanar masa ba,
Sai da Baffa yagama komai harta gidan da matan zasu zauna Baffa ya samar masa an hada lefe na alfarma ankai biki ya taso gadan gadan sannan Baffa yace masa idan yagama exam yadawo gida lokacin shekararsa biyu babu watanni 3 acan,
Shi bai san ko menene ba dan haka yafara murna yahau shirin dawowa gida, pretty dinshi yaje yayiwa tsaraba ya sai mata zoben gold mai kyau ya siyo mata abin hannu shima na gold,
Aranar laraba da yamma jirginsu ya sauka a filin saukar jirage na sir ahmadu bello, yahade cikin blue din suits masu tsada wadanda suka karbeshi gashi zuwansa waje yasashi ya dada wayewa ya sake zama dan birni dan gayu _(classic guy)_,idonsa sanye da bakin gogle wanda ya sake fito da farar fuskarsa mai dauke da bakin saje akwance luf.

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.