RUWAN KASHE GOBARA! 32

0 175

_32_

Koda innah taganshi ahaka gigicewa tayi domination ba karamin kumbura idanuwanshi suka yi ba sakamakon kukan da ya kwana yana yi,
“Lamido meya sameka?” Tafada agigice,
“Innah ciwon ido nake” yabata amsa yana mai sake runtse idonshi saboda baya son taga hawayen da yake boyewa domin kwalla ta taru acikin idonsa,
“Kaje ka nemo magani maza”
“To innah”
Breakfast yadan cakula yasha ruwan tea empty yatashi saboda baya son hankalin innah ya tashi yasan muddin taga baici abinci ba to zata shiga damuwa,
Bakin face yasaka a fuskarshi ya rufe idanuwanshi ya dauki daya daga cikin motocin baffa ya fita,
Cikin gari ya shiga yaje ya tsaya agefen kasuwa daidai plaza dinnan da yayiwa mahaukaciyar nan fyade,
Kallon barandar da yaganta azaune yafara yi kwalla tana ciko idonsa, ya dauki lokaci mai tsawo acikin motar zaune yana kallon wurin kamar wani tababbe,
Jan motar yayi yanufi gida, abakin gate din gidan suka yi kicibus da bash yazo gidan,
Fitowa yayi ya rufe motar yanufi bash din,
“On top wannan face din fa sai kace sabon makaho”
Dan murmushi Lamido yayi ya mika ma bash hannu yana cewa,
“Ciwon ido nake yi kasan kuma zan iya shafawa wasu shiyasa na rufe”
“Ko kuma ka kwana kana kuka ba” bash yafada yana kallonshi
“Apolo nake yi”
“To Allah yabada lafiya, yanzu dai ga invitation cards can na bugo na rarraba suma amaren na kai musu nasu”
Shiru Lamido yayi shifa yama dade da mantawa da fadila da ihsan din domin rabonshi dasu tun yana sch a yola,
“Shikenan tunda ka gama rabawa, Allah ya saka da alkairi ni yanzu zazzabi nake ji zan shiga ciki”
“Allah yabaka lafiya domin gobe ne daurin aure fa kuma akwai dinner, akwai ladies night, akwai Polo day, akwai…”
“Dan Allah ya isa haka Allah ya kaimu goben” Lamido ya katseshi tareda yin gaba yabar shi awurin,dakinsa yakoma ya kwanta bayan yasakawa kofar key, lulluba yayi da bargo sakamakon zazzabin da yake ta rinjayarsa babu dadewa zazzabi mai zafi ya rufeshi tuni yafara suratai marassa dalili kamar yanda ya saba duk lokacin da yake zazzabi.
Shirye shiryen biki kam ya gama kankama sosai bash sai rabon katin gayyata yake yi amma duk wanda ya bawa katin indai abokinsu ne sai yayi mamakin jin cewa on top ne wai zaiyi aure kuma aurenma fadila da ihsan zai aura saboda duk sch dinsu kowa yasan soyayyarsa da yan matan biyu sukuma duk inda suka hadu sai sunyi fada akansa kwata kwata jininsu bai haduba gashi kuma zasu zama kishiyoyin gaske da rabon miji daya zasu aura.
Amare kam kowacce ta damu bash da tambayar ina lamido yake domin dukkaninsu suna son ganinsa,shidai bash kawai ce musu yake yana nan zuwa sabgogine suka yi masa yawa.
Kamar jiya Lamido yauma baiyi bacci ba gashi bashida lafiya zazzabine ajikinsa mai zafi, ganin zai mutu shi kadai adaki yasashi tashi ya tasamma bangaren innah, lokacin da yaje sashen nata acike yake da baki yan uwa,
Dakinta ya shiga ya sameta da yan uwanta sai hira ake yi kamar ba dare ba,innah na ganinsa tasan bashida lafiya, hannunsa ta kama ta fita dashi zuwa sashen baffa yan uwa sai tsokanarsa ake yi suna fadin,
“Kaga angon mata biyu alokaci daya, ayyuri yuri yuriririiiiiiiikiii..!”
Bai iya cemusu komai ba har suka fice,
“Lamido jikinne ko? Sannu”
Falon Baffa ta kaishi lokacin baffan yana zaune yana lissafa katan katan din goro da alawar da aka siyo yana warware na kowanne gida wanda za akai gidan amaren,
“Baffa kaga Lamido bashida lafiya” inna tafada tana zaunar dashi akan doguwar kujera,
“Assha sannu Lamido, um kawo masa abinci yaci sai yasha magani”
Cikin sauri innah ta nufi dining table ta zubo masa tuwo da miyar kubiya ta kawo, tashi yayi ya karbi tuwon yaci lauma biyar ya ajiye yasha paracetamol ya koma ya kwanta mintuna kadan bacci ya daukeshi.
Tunda yafara baccin nan bai tashi ba sai karfe 3:30 nadare, dakinsa ya koma ya yi wanka ya sake kwanciya sakamakon daren jiya baiyi bacciba yasa baccin saurin sake saceshi daga nan kuma bai farka ba sai da asuba,
Bayan dawowarsa daga masallaci ma kwanciyar ya sake yi dama tun jiya wayoyinsa duk ya kashesu saboda baya son damu,
Yana tsaka da bacci yaji ana tashinsa, tsaki yayi yadan juya kadan yatashi, yayanshi yagani rikeda kayan da zai saka,
“Haba Broz ya ina baccina kawai zaka zo ka katse min”
“Tashi Broz kayi wanka ka shirya ai daurin auren naka ya kusa, kaga na farkon a Numan za adaura na biyun kuma anan cikin Yola, to yanzu Numan zamu fara zuwa, ga kayanka wanda zaka sa”
Tashi yayi yana cije lebe ya shiga bathroom yayi wanka ya fito lokacin har Broz din nashi ya fita, agaban mirror ya tsaya yana kallon fuskarshi har yanzu akwai kumburi a idonshi ga ja, mai ya shafa yasha turare yasaka farar shaddar da yayanshi ya ajiye masa wacce tasha dinki, anan ya fito a angonshi sak, hular ma farace haka takalmin duk farare ne agogon hannunshi ne kawai na azurfa mai kyau, bakin face yasaka afuskarshi saboda tsaro.

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.