RUWAN KASHE GOBARA! 34

0 172

_34_

Washe gari tunda safe Lamido ya fita, bakin wannan plaza din ya je ya tsaya amma yauma babu ita babu alamunta yau kam har cikin kasuwar ya shiga ya na dan duddubawa ko zai ganta amma shiru, kangon da yayi mata fyade aciki kuwa tuni an gineshi an mayar da shi shaguna,
Yajima yana kekkewayawa yana yawo amma maimakon yaganta ma sai sabbin mahaukata yake gani maza, glass din motar tashi ya sauke yafara mika musu kudi yan dari bibbiyu sababbi,
Gida ya koma ya shiga daki ya kulle kansa har azahar tayi yana nan akulle sai da bash yazo tukunna ya samu ya bude kofar bash ya shigo yana kallonsa kallon kurulla,
“Wai kai meke damunka, sai ka shigo daki ka rufe wayoyinka duk akashe mutum bazai sameka ba”
“Bana son adameni ne, bana son hayaniya i don’t want any hustle and bastle”
“Suwaye zasu damekan, mu ko matanka?”
“Duk wanda kaga ya dace”
Kafin bash ya sake magana innah ta shigo dauke da flask din abinci da kunun shinkafa awani jug,
Fulatanci ta hau yi masa,
“Lamido meyake damunka ne baka son cin abinci, dan Allah ka karba kaci kaji”
“Innah zanci”
“Yawwa Lamido shiyasa ma idan ankawo amaren naka zan fada musu baka son cin abinci sai suna yi maka dure”
Dukkaninsu dariya suka saka banda Lamido wanda murmushi kawai yayi,
Ba don yaso ba haka ya dauki abincin ya danci shida bash suna gamawa suka fita salla ahanyarsu ta dawowa bash yake sanar dashi cewar ihsan itama yau za akawota amfasa goben,
Baice komai ba yawuce dakinsa domin yanzu idan akwai abinda yake kauna arayuwarsa to zaman dakine baya ga wannan baya bukatar komai.
   Misalin karfe 9 nadare aka kai masa amarensa gidansa dake unguwar governor road, shikam yana gida akwance yana dan jin zazzabi sama sama dama ko kayansa ma sai bash ne ya hada masa yakai can gidansa ya saka masa a dakinsa,
Yana kwance yana aikin nasa na tunani bash ya shigo,
“Wai dama baka shirya ba?” Dan Allah on top kai muke jira”
Batare da yayi magana ba ya mike ya shiga toilet yayi wanka ya fito har lokacin bash yana tsaye yana jiransa, mai ya dan shafa ya gyara sumarshi da sajensa yasaka wani farin lallausan yadi mai kyau wanda yake kamar tissue marar kauri domin har ana iya hango farar singiletin daya saka aciki jar hula yasaka,
Turarensa mai mutukar dadi ya fesa na azhaar, jan hannunsa bash yayi suka fita, wurin innah ya shiga yayi mata sallama ya fito yashiga wurin baffanshi shima yayi masa sallama ya fito,
Cincirindon abokansu yagani wadanda zasu rakashi, yake ya rinka yi yana basu hannu suna gaisawa kowa sai murna yake tayashi,
Motar bash ya shiga suka dauki hanya anan yake fadawa bash cewar suna kaishi kawai su tafi baya bukatar su shigar dashi domin kanshi ciwo yake yi,
Bash bai ki ba suna zuwa gidan ya saukeshi yaje wurin abokan nasu yana yi musu jawabi,
Gidan kawai Lamido yake bi da kallo Wanda yake katon gaske yasha fenti pink pink milk milk, farfajiyar gidan ma badai girma ba gashi anyi shuke shuke, hasken wutar lantarki ya haskake ko ina,
Cikin gidan ya tasamma wanda yake babban falo ne na gaske wato general falo, sai kuma corridors wanda kowacce tana dashi tanan zaka bi kaje sashenta, shikuma nasa sashen yana ta opposite dasu amma kuma gidan sashe hudune hakan yasashi dan murmushi domin daya sashen sashen pretty dinshi ne sai dai yana jin tausayinta na zama da zatayi da kishiyoyi hakan zai kawo nakasu acikin kyakkyawar rayuwar da ya shirya bata.
Dakinsa yanufa wanda ajiki aka rubuta _master room_ ahankali ya bude ya shiga, dakin katone sosai yasha sha funutures masu tsada kirar Royal, komai na dakin ya dace dashi,
Kan gadonshi ya karasa ya zauna yana bin dakin da kallo, tashi yayi yaje ya rufe kofar da key yadawo kan gadon yayi tagumi yana tunanin da ace pretty dinshi aka kawo mishi gidan nan ai da yanzu yana tare da ita yana bata kulawa, yana shayar da ita ruwan soyayyarshi mai mutukar tsada,
Runtse idonshi yayi sai ga hawaye sharrr suna bin kumatunshi,
Hangosu kawai yake shida pretty acikin wani yanayi, kuka ya fara yi ka’in da na’in yama manta da cewar amarensa na can suna zaman jiransa,
Shiru shiru bai shigo ba gashi kuma kowacce sai kiran wayarsa take akashe nan duk hankulansu ya tashi,musamman ma fadila,
Agogo ta kalla karfe 12:30 nadare, wayarta ta dauka tana kuka takira babanta yana dagawa tace ita tsoro takeji har yanzu ita kadai ce agidan Lamido bai shigo ba, lallaminta babanta yayi yace bari yakira baffan lamidon,
Wayar ta kashe tana kuka, babanta suna gama waya da ita baffa ya kira yace har yanzu fa ango baije gidan ba yabar yarinya ita kadai acan,
Mamaki baffa yayi to ya akayi haka tunda 9 Lamido yayi musu sallama ya tafi, bai gama wannan mamakin ba Baban ihsan shima ya kirashi domin itama tayi waya gida tana kuka wai Lamido bai zo gidan ba, dole tasa baffa fita adaren ya dauki mota ya nufi gidan Lamido addu’arshi daya Allah yasa dai Lamido ba club yatafi ba ko gurin shashancinsa tunda ya kula kamar bai so wannan auren da akayi masa ba,
Wayar bash yake ta kira amma bai daga ba sai da ya kirashi wurin sau 10 sannan ya daga cikin magagin bacci,
“Baffa..”
“Kai bashir kuna ina ne?”
“Baffa ni ina gida Lamido kuma yana gidansa tun 9 na kaishi natafi”
“Ka tabbata?”
“Ehh Baffa”
Kashe wayar baffa yayi ya nufi gidan lamidon yana zuwa watchman ya bude masa ya shiga, gidan shiru tsit kamar babu kowa gashi babu hayaniya asalima unguwar sabuwar unguwace lallai dole amaren su shiga damuwa.

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.