RUWAN KASHE GOBARA! 37

0 157

_37_

Haka yaci gaba da hakuri yana zaune da ita gashi kullum cikin cin take away suke domin girkinma batayi,
Wannan dalilin yasa suka fara yar tsama, kamar kullum yauma shiryawa yayi cikin kananan kaya blue din t shirt da black din trouser yayi kyau sosai kamar wani dan indiya turaren black valvet ya dauka ya feshe jikinsa dashi, bai ko kalli inda fadila take ba ya dauki jakarshi yayi gaba,
Baki ta taba ta sake gyara kwanciyarta caraf idonta ya sauka akan wani hoto wanda ke boye abayan akwatunan kayan lamido, tashi tayi taje ta dauko hoton, hoton macene amma kuma hoton wani iri domin an zana matar kamar irin mutanen da dinnan, cillar da hoton tayi ta koma tayi kwanciyarta,
Lamido tunda ya fita bai dawo ba sai bayan sallar azahar yana shiga daki yaga hoton pretty akasa can akan katifa kuma fadila ce ke kwance tana bacci,
“Kai!” Yafada dakarfi,
“Fadila, waye yasaki fito min da wannan hoton? Iye?”
Firgigit fadila tayi ta tashi tana zare idanu tana kallonsa,
“Abayan can naganshi” tafada cikeda rashin damuwa,
“To shine zaki dauko min ki yarshi anan saboda baki san muhimmancin sa ba ko? To bari kiji wannan hoton yafi komai muhummanci acikin rayuwata, ina tsananin kaunarsa kuma ina sonsa karki kuskura ki sake taba min shi idan ba haka ba ranki zai iya baci..”
Daukar hoton yayi yana gogeshi da gefen rigarsa yaje ya mayar dashi wurin da yake dafarko a ajiye, duk fadila na zaune tana kallonsa, fita yayi daga dakin hakan yasata komawa tayi kwanciyarta tana taba baki
“Akan wannan banzan hoton zaka wani zo kana yimin fada, mtswww”
Tafada tareda jan tsaki ta sake gyara kwanciyarta.
*
Ikhlas taci gaba da rainon danta abdallah wanda ahalin yanzu har ya cika shekaru biyu daidai, wayo kuwa awurinsa kamar ba dan fari ba gashi tabarakalla kyakkyawan gaske,
Kamar yadda yayanta hussain yayi alqawari cewar zai zamewa abdallah uba to hakika yacika alqawarin domin daga ita har abdallah babu abinda suka nema suka rasa, gatan da abdallah yake samu kuwa wani mai ubanma baya samun rabinshi,
Rayuwarta kam yanzu sai godiya kuma tayi sa’a Allah ya dauke mata damuwar datake fama da ita ada, yanzu zuciyarta fes take.
Yau kam takama ranar laraba wanda bikin yayunta saura kwana 5 agudanar dashi, gida sai shirye shirye ake tayi, kwance take tana baccin rana,
Abdallah ne ya garzayo da gudu yazo ya dale jikinta yana jijjigata,
“Anty ki tashi muje ki siyo min kayan”
Tashi tayi tana rungume dashi ajikinta,
“Ohh abdallah badai zaka barni nayi baccin nan ba saida ka tasheni”
Shiryawa tayi shima ta shiryashi suka yiwa ammi sallama suka fita,taxi ta tsarar musu suka shiga suka nufi shopping complex,
Suna shiga layin kayan yara ta wuce domin zabowa abdalla kaya, hadaddun riga da wando ta zabo masa kala biyar ta koma wurin takalma tafara zaba,
“Anty turare fa?” Ya tambayeta yana nuna mata,
“Jeka ka zabo wanda kakeso guda daya to”
Dagudu ya kwasa ya tafi wurin turarurrukan, wani mutum yagani atsaye awurin turarukan shima yana dubawa,
Rungume mutumin yayi tabaya kamar Wanda ya sanshi yana cewa,
“Uncle nima zabar min guda daya antyna zata siya min”
Cikeda mamaki mutumin ya jiyo yana kallon abdallah,
“Wow, boy ina antyn naka?”
“Tana can tana zaba min kayan da zansa abikin uncle hussain da uncle hassan”
Kama hannunshi mutumin yayi ya dauka masa turaruka guda uku manya masu tsada,
Suna tafe suna hira har suka karasa wurinda ikhlas take,
Dagowa tayi tana kallon abdallah da mutumin,
“Abdallah a ina ka tsayane?”
“Agun uncle” yabata amsa yana nuna mata mutumin,
“Uncle…” Tafada cikin mamaki, kallon mutumin tayi farine dogo mai kyakkyawar fuska,
“Barka da yamma anty”
Yace da ita yana murmushi,
“Yawwa” tafada ahankali tana kamo hannun abdallah,
“Ya zaki kwace kanin naki bazaki barmin shiba?”
Murmushi tayi “Kanina ko Dana?”
“Haba anty ai duk son girmanki baki haifi wannan yaron ba?”
“Ko saboda me?”
“Saboda bakuyi kama ba ko kadan, kamarsa daban taki daban”
“Wannan shine kadai dalilin? Dama dolene yaro sai yayi kama da babarshi?”
“Kwarai kuwa”
“To kuma idan babanshi ya dauko fa?”
“Duk da haka dai baki haifi wannan yaron ba, ke yarinyace wacce ko auren fari ba ayi miki ba, ina tunanin ma yar makaranta ce”
Murmushi tayi tabishi da kallo,”to na yarda bani na haifeshi ba”
“Kin kosa da mahawarar kenan?”
“Hmm ba kosawa nayi ba, kawai dai nabar maka musunne na dauke ladan”
Jan hannun abdallah tayi domin subar wurin amma mutumin yayi caraf ya rike abdallah,
“Ya zaki rabamu bayan kin ganmu tare?” Sakar masa abdallah tayi takara gaba, tana tafe suna binta abaya ya dauki abdalla ya rikeshi akafadarsa,
Wurin biyan kudi taje ta cicciro kayan wanda duk na abdallahn ne babu nata,
Lissafi aka yi mata dubu 10,kafin tayi yunkurin biya har wannan mutumin ya biya,
Kasa magana tayi ta dauki kayan tafita ta tsaya awaje tana jiran fitowarsu, suna fitowa tafara yiwa mutumin godiya,
“Nagode madalla Allah ya saka da alkairi”
“Amin, shiga mota muje?”
“Ina zamuje?” Ta tambayeshi cikin mamaki,
“Anty gida, uncle zai kaimu gida”
Binsu tayi ta shiga motar amma abaya ta zauna bata shiga gaba ba sai dai amma sai kallonta ta mudubi yake yi duk motsin datayi sai taga sun hada ido ta cikin mirror.

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.