RUWAN KASHE GOBARA! 4

0 168

_4_

 Tsinke wayar yayi yana murmushi domin daga jin irin amsar da likitan yabashi yasan za ayi nasara,
Tashi yayi da kyar ya shiga toilet yayi alwala ya fito sai alokacin yayi salla, yana zaune akan abin sallar yana tunanin wannan mahaukaciyar, baffa da inna suka shigo,
“Lamido, me kuma ya sameka? Ina fata ba shaye shayen naka da ka sababa kaje kayi ka dauko wata lalurar ba?” Mahaifinsa yafada lokacin da yake kokarin shigowa cikin dakin,
Dagowa da kansa Lamido yayi,
“Baffa zazzabine fa kawai”
“Rufe min baki yaron banza, duk kabi ka gama zubar min da mutuncina agarin nan, baka da aiki sai shan kayan maye da lalata yayan mutane”
Sunkuyar da kai Lamido yayi domin dama ya kwana da sanin zai sha fada awurin baffan,
“Baffa tunda bashi da lafiya kayi hakuri..” Mahaifiyarshi tafara magana kafin baffan ya katseta,
“Ki barni dashi Zaituna,wannan yaron bashida hankali ko kadan, bashida tunani, kullum shi kenan acikin shan abubuwan maye, to ka saurara kaji, idan kaje can turai din ya rage ga naka ka tsaya ka nutsu ko kuma sabanin haka, nidai nagama duk abinda zanyi maka a matsayina na uba,ka duba kaga jiya har 12 baka dawo gidan nan ba kana can kana yawon gantalinka, to duniya dai ta ishi kowa riga da wando, wanda bai zo bama tana nan tana jiransa”
Yana kaiwa nan ya juya ya fita daga cikin dakin cikeda takaicin halayya irinta danshi Lamido,
Inna ce ta matsa wurin lamidon ta dafa kafadarshi,
“Lamido dan Allah ka tsaya ka nutsu ka daina wannan shashancin kaji, baka koyi da dan uwanka wanda shi ya kasance nutsattse mai hankali, ka zauna kayi karatun ta nutsu kaji,Allah yayi maka albarka”
Tashi yayi ahankali batare da yace komai ba ya hau kan gadonshi ya sake kwanciya ya tukunkune acikin bargo domin wani zazzabin ne yake neman rufeshi.
*
Ahankali ta bude idanuwanta, wurin datake tafara bi da kallo, kallonta ta mayar kan jikinta,
“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un” tafada ahankali tana shafa kanta,
Ayanda taji gashin kanta acukurkude ya sanyata mikewa arazane amma babu shiri ta koma ta zauna sakamakon wani irin zugi da radadi da take ji ajikinta,
Bin ko ina take yi da kallo tana mamakin meya kawota nan,yanayin yanda wurin yake ya sanyata gane cewar tabbas wurin kasuwa ne,
Jin danshi akasanta ya sata dubawa jini tagani ajikinta sannan ga wani zafi yana ratsata,
K’arar hadarin da yake ta gudu a sararin samaniya ne yasata mikewa ahankali, kafarta babu takalmi haka ta doshi bakin titi tana dingishi, jinta take kamar sabuwar halitta kamar ba itaba,
“To nan inane? Ni kuma meya kawo ni nan? Kodai mafarki nake?” Wadannan tambayoyin ta jerowa kanta amma bata da wanda zai bata amsar tambayoyinta.
Titi ta mike sambal tabi tana tafiya ahankali batare da tasan inda zataje ba.

WhatsApp: 08161892123

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.