RUWAN KASHE GOBARA! 40

0 200

_40_

Yayi murna sosai kuma yayi farin ciki ya kashe kudi domin hidimar suna, ranar suna aka sanya min suna ikhlas wannan shine sunan da mahaifiyata ta zabar min,
Nan fa yakumbo ta shiga maganganu saboda ba asaka sunata ba wannan dalilin ne yasata sake tsanar mahaifiyata da yayanta,makaranta ma da aka saka su Hussain ata kudi haka ta tada sababi tasaka abba adaki ta zazzageshi tace lallai lallai aciresu domin bazata zuba ido tana ganinsa yana watsa kudinsa ba alhalin ba gama haihuwa yayiba, ga Nafi nan itama haihuwa zata yiyyi nan gaba, da yake dane mai biyayya sai yabi maganarta domin baya yi mata musu.
Makirci da manakisa babu wacce ammi bata ganiba, ga sharri kala kala, ranar da bazan manta ba itace lokacin ina yar shekara biyar,
Yayuna sun tafi makaranta sai ammi tafita ta dora mana abinci tana girkin yakumbo da Nafi suka fito suketa zaginta amma bata ko daga ido ta kallesu ba har takusa kammala aikinta,
Tagama abincin kenan tazuba min ina ci, Nafi ta debo dakakken barkono ta watso ma ammi wannan yayi daidai da shigowar su hussain daga makaranta, ai hussain na ganin haka ya daka tsalle ya ballo reshen bishiyar umbrella din dake tsakar gidanmu ya nufi yakumbo da Nafi,
Yana zuwa ya hau jibgarsu dayake shi mutumne mai zafin rai da zuciya, duka sai da yayi musu lilis dakyar suka gudu daki,
Shikam hassan kallo ya tsaya yi saboda sam bashida fada, wannan dukan da hussain yayiwa su yakumbo shine sanadin da yasa yakumbo ta tursasa abba ya saki ammi kuma tace bazata bar su hussain ba sai dai tatafi da tsiyarta,
Nice kadai aka barni agidan domin abba yana mutukar sona yana ji dani saboda ina jin acikin magungunan da su yakumbo keyi basu samu wanda zai rabashi dani ba,
Fada maka irin bakar wahalar dana sha ahannun matar uba da yakumbo abin kamar bata bakine domin nasha wahala sai dai suna yin hakanne idan abba baya nan amma idan yana nan nuna min so suke yi,
Ahaka nayi primary private nagama har nayi secondary nanma na kammala lokacin nazama budurwa sosai ga gata da abbana yake nuna min domin lokacin ya shiga siyasa kuma yayi suna sannan ya samu karbuwa,
Dakina daban abba ya shirya min ya saka min kayan kyale kyale irin wanda duk wata budurwa zata bukata,
Shekarata daya da gama secondary abba ya kaini aikin hajji, acan na hadu da wani saurayi kamal Wanda dan gidan wani senator ne a abuja,
Muna dawowa gida kamal yafara zuwa wurina, hidima da kashe kudi yana yimin sosai, irin hirar da naji Nafi da yakumbo suna yi domin ganin sun cutar da abba ta hanyar zuba masa garin magani yasa nafara girkawa abbana abincinshi dakaina, nice nake dafa duk wani abu wanda zai ci,
Haduwarmu da kamal baifi da wata uku ba senator yazo gidanmu yakawo kudin aurena naira dubu dari biyar da kujerar hajji,
Ai wannan abu ba karamin daga hankalinsu Nafi yayiba take suka shiga kulle kullensu nikam ban san abinda ke faruwa ba,
Ranar lahdi da daddare lokacin abba yatafi abuja hajiya Nafi ta shigo har dakina tace zobene na azurfa aka kawo tallarsa wata kawarta data dawo daga dubai nima gashi ta dauka min idan abbana yadawo sai yabada kudin,
Batare da tunanin komai ba nakarba na ajiye akan mudubina, kin tafiya tayi tace nasaka tagani,
Dauka nayi nasaka dama daga wanka nafito, nadauko Pakistan dina riga da wando nasaka take naji wani irin nannauyan bacci yana daukana nan nakwanta awurin, tsakar dare natashi nafice nabar gida shikenan ban sake sanin inda hankalina yake ba,
Koda gari yawaye aka nemeni aka rasa, abba ma lokacin da yadawo ya tarar ana nemana hankalinsa ba karamin tashi yayiba,
Nan yabaza mutane nemana gidan radio da jaridu da gidajen tv duk cikiyata ake an manna hotuna na, abbana har cewa yayi duk wanda ya samoni zai bashi miliyan biyu amma shiru,
Adakina aka samu wata wasika wai nice na rubuta acewar su Nafi,
_Zuwa ga abbana abin sona, abba nasan zaka yi mamakin ganin wannan wasikar tawa to ba abin mamaki bane na rubutata ne domin nasanar dakai cewar natafi zan shiga duniya yawon karuwanci domin ta wannan hanyar ce kadai da zan iya rama abinda kayiwa mahaifiyata, zanje na iyo cikin shege nadawo gidanka domin ina son mutane su tsaneka sudaina yinka._
_Nabarka lafiya,_
_Daga yarka ikhlas_
Lokacin da abbana yaga wannan wasikar ba karamin bakin ciki yayiba amma sai su Nafi suka fita daga zargi bai zargesu ba saboda wasikar da yagani.
Labarin taci gaba da bashi har izuwa yau ta kare labarin tana kuka,
“To tayaya da mutuncinka zaka auri wacce tayi cikin shege ta haihu”
Murmushi sadeeq yayi yace,
“Ikhlas kenan, wannan bazai zama dalilin da zai saka naki aurenki ba, saboda kaddara ce ta afka miki bawai da ganganci kikayi ba, ni nayi alqawarin zan aureki ahaka nan bada dadewa ba, insha Allahu nan da wata biyu kina gidana a matsayin matata, sai dai na manta ban fada miki ba inada iyali, sunanta Suhaima da yaranmu Hudu, haydar, faruk, sayyid da kanwarsu Aysha,”
Murmushin karfin hali tayi tace “Allah ya rayasu”
“Amin, ni dan yolane mahaifina babban alkaline a yola, ina da yayu biyu daya mace daya namiji sannan inada junior brother guda daya”
Daga kai tayi alamar gamsuwa,
“Yakamata muje na mayar daku gida tunda yamma tayi kar ammi tayi fada”
Murmushi tayi ta mike tana kokarin nannade dardumar da suka zauna akai, shine yaje ya kamo hannun abdallah daga wurin da suke wasa shida yara,
Sai da ya biya dasu ta supermarket yayi musu siyayya sannan ya mayar dasu gida.

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.