RUWAN KASHE GOBARA! 41

0 157

_41_

Tun daga lokacin Abubakar sadiq ya mayar da gidansu ikhlas gida domin kullum sai yazo, yanzu agidan babu wanda bai sanshi ba, abdallah kuwa tamkar dan cikinsa domin kullum suna tare,
Ita kanta ikhlas din yanzu ta sake dashi ta amince masa duk da dai bataji tana tsananin sonshi ba amma zata aure shi domin halaccin da yayi mata,
Tamfatsetsiyar waya mai tsada ya siyo mata gashi duk abinda zata bukata yana siyowa ya kawo mata, nanfa yafara neman aurenta gadan gadan,
Ganin ba wani auren saurayi bane yasa su ammi yanke ranar auren sati uku, nanfa aka shiga shirye shiryen biki domin a yola zata zauna sannan yace bazai hada musu gida da matarshi ba kowa gidansa daban,
Yayunta sunyi rawar gani sosai wurin siya mata furniture’s masu tsada hadaddu kirar royal,gyara kuwa na amare tashashi domin indai gyarane to gidan ta taras, gyaran jikin da akayi mata hatta fatarta sai da ta sauya tayi laushi lubus kamar ta jarirai,
Abubakar sadiq ya dage sosai wurin yi mata kayan lefe masu tsada komai irin wanda ake yiwa budurwa yayi mata,
Ranar juma’a da misalin karfe 2 na rana aka daurawa Abubakar da ikhlas aure acikin garin borno,
Aranar aka tafi da ita yola domin kaita gidanta, kuka itada abdallah dakyar aka rabasu domin Hussain yace ba zata tafi dashi ba sai dai ya rinka zuwar mata hutu.
Hanyar birnin yola aka dauka da ita tana tukunkune cikin katon mayafi sai kuka take yi aranta kuma tana jin girman Abubakar sadiq da kimarsa tana kara karuwa acikin zuciyarta domin yayi mata komai ya rufa mata asiri ya sota ya nuna mata kauna hakika ya zamar mata wajibi ta zauna dashi da gaskiya kuma ta kyautata masa,
Sai daf da sallar magrib suka samu suka shiga garin yola, kai tsaye gidanta dake unguwar senate roads aka dauka da ita domin ko sallar la’asar basu samu sunyi ba,
Suna zuwa gida ya cika da hayaniya dakinta kuwa jama’ar ta isa, sai dai abinda yake tayarwa da ikhlas hankali shine faduwar gaban datake tayi koda wanne lokaci,
Daurewa tayi tafita inda sadiq ke tsaye yana jiranta bayan sun gama waya,yana tsaye a bayan dakunanta yasha shadda ruwan kasa mai masifar kyau,
Hannunta yakama suka tasamma dakinsa,
“Muje kiyi salla ko?” Yace da ita yana duban fuskarta, kai ta daga suka shiga dakin nasa wanda ya tsaru mutuka,
Yana zaune yana kallonta tayi sallar ta idar,
“Yanzu kije kiyi wanka kici abinci ki kwanta ki huta, gobe idan Allah ya kaimu gidanmu za a kaiku domin acan za ayi wunin biki sannan da yamma idan brother na yadawo akwai walima wacce za agabatar a Mubarak hotel”,
Batare da tayi magana ba kawai ta mike zata fita, hannunta ya kamo wanda yasha kunshin jan lalle da baki wanda ba karamin kyau yayi mata ba, kyau kam ikhlas tayishi babu wanda zai ganta yace ba budurwa bace,
“Kunshin yayi kyau my..” Yafada yana sinsinar hannunta,
“Nagode” ta bashi amsa atakaice,
Dakyar ya saketa tafita ta koma dakinta Wanda yake cike da yan rakiya domin duk yan gidansu babu wanda baizo ba in banda ammi amma hatta matan Hussain da hassan duk sunzo,
Wanka ta shiga ta fito saboda jinta take agajiye sosai, tana gefen gado tana Shafa mai hajiya kakarta ta dubeta,
“Yarnan banga kinci komai bafa, ina jin rabonki da abinci yau kwana biyu kenan”
“Kibarta hajiya ai dura za muyi mata wallahi idan ta gama shiryawa” shamsiyya matar hassan tafada tana dariya,
“Angon zamu kira kawai yayi mata durar” farida matar Hussain ta cafke zancen, ita dai ikhlas tana zaune tana jinsu bata tanka ba domin ita kadai tasan irin faduwar gabar datake addabarta.
*
Zaman Lamido da fadila akasar Kenya haka yayita tafiya yau da dadi gobe babu amma kasancewar ita fadilan tana mutukar sonshi yasata fara dan gyara halinta tana yin abinda yake so,
Yau tunda suka tashi daga barci yafara yi mata albishir din gobe zasu tafi Nigeria amma bazai dawo da itaba shi kadai zai dawo,
Duk da haka tayi murna amma tasan zatayi missing dinshi hakan yasata langabe kai,
“My Lamido zanyi missing dinka idan ka dawo kabarni”
Hannunta ya rike yana kallon kyakkyawar fuskarta,
“Karki damu my fadila just three months kawai zanyi nadawo shikenan nagama, zamu kasance har abada tare”
Kiss tayi masa agoshi ta tashi ta shiga toilet,shiryawa sukayi suka fita domin yin siyayya, kaya sosai fadila ta dibarwa yan gidansu da kawayenta,
Shikam Lamido ihsan ya saiwa kayan shakatawa itada prettyn sa, sai ko brother dinshi da ya siyawa agogon silver mai kyau,
Kasancewar jirgin karfe bakwai suka bi yasasu sauka da wuri domin karfe 10 daidai na agogon Nigeria suka sauka, bash ne yaje daukosu, nan Lamido yafara tambayar bash tun acikin mota,
“Bash ya alkawarinmu? Ka samo min pretty din?”
Murtuke fuska fadila tayi jin an ambaci mace amma hakan bai damu lamido ba saima ci gaba da yayi da tambayar bash,
“Nifa wlhi nama manta da wata pretty dinka” bash yafada yana driving,
Tsaki Lamido yaja yashafa sumar kansa,
“Insha Allahu kuwa sai na nemota da kaina”
“Yafi maka dai” bash yabashi amsa,
Lamido bai sake magana ba har suka je gidansa, ihsan suka samu ta shirya musu kayan tarba kala kala iri iri amma kuma tsakaninta da fadila babu kallon arziki sai hararar juna suke yi kamar zasu kwancame da dambe,
Jikin Lamido ihsan taje ta shige tana murna,
“I missed you my Lamido..” Ihsan tafada tana rungume dashi,
“Me too my ihsan, ya studies?” Ya tambayeta yana shafar kumatunta,
“Kaga mai mata biyu angon fadila da ihsan dan gatan baffa” bash yafada cikin zolaya,
“Akwai ta ukun ma tana nan zuwa” Lamido yace dashi bayan ya zauna akan kujera,
Abincin da ihsan ta shirya musu ta fara zuzzuba musu, babu laifi tayi kokari kuma abincin yayi dadi amma fadila kamar adole take ci saboda sai wani yatsine yatsinen fuska take yi, ita kam ihsan bata kara bin ta kanta ba tana can jikin Lamido ta lafe sai ciyar da junansu abinci suke, abin nasu gwanin sha’awa shi kansa Lamido yana tsintar kansa cikin farin ciki idan ya kalli ihsan da fadila saboda dukkaninsu kyawawa ne na karshe hakika yasan ya yi sa’ar mata masu kyau presentable yanzu burinsa dayane ya mallaki pretty dinshi a matsayin mata.

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.