RUWAN KASHE GOBARA! 43

0 106

_43_

Dagowa Lamido yayi yana kallonsa,
“Lamido kuka? Kuka fa kake kamar karamin yaro,meya faru?”
Rungume bash yayi yafashe da kuka “bash narasata,wallahi narasata har abada”
“Wacece? Taya akayi kasan ka rasata? Haba Lamido be a man mana amma ka zauna kana kuka kamar wani mace”
Hawayen fuskarsa yafara sharewa yana kallon bash,
“Lamido wa ka rasa?”
Shiru Lamido yayi domin baya son ya sanarwa da bash abinda yafaru, tambayar duniya bash yayi masa amma yaki fada masa gaskiyar abinda ya faru,
“Bash duk burina yanzu ya wargaje, shirina duk yagama baci, banida burin da ya wuce sai na pretty ashe ba rabona bace” yafada muryarsa adashe saboda kukan da yayi,
“Kayi hakuri Lamido, dan Allah kabar kukan nan, nayi maka alkawari zan tayaka burinka ya cika”
Kallon bash yayi yana murmushi mai ciwo,
“Bash ba zaka gane bane, muje ka ajiyeni agida”
Exchanging din wurin zama suka yi bash yafara driving yana jin tausayin Lamido,
Gidansa ya kaishi ya ajiyeshi yatafi, a falo ya iske ihsan tana kwance tana kallo, ita kuma fadila ta tafi ganin gida,
Tasowa ihsan tayi ta kamashi zuwa dakinsa kwanciya yayi ya rike kansa wanda ke faman yi masa zugi,
Wuni yayi a kwance ranar bai tashi ba sai dai idan zaiyi salla, ihsan duk tabi ta shiga damuwa domin tana tsananin sonshi jin ciwon take har cikin ranta,
Kayansa yasata ta shirya masa domin tafiyar wuri yake son yayi.
*
Abangaren ikhlas amarya kuwa tunda aka tashi daga walimar bikinta taji wani zazzabi yana shamayarta dan haka ana tashi Abubakar sadiq ya kama hannunta aka nufi gidanta da ita, suna zuwa yan uwanta suka fara yi mata sallama domin komawa borno,
Kuka kam ta shashi kamar ranta zai fita, dakyar sadiq ya iya rarrashinta ya samo mata abinci taci ta kwanta,
Kwananta biyu tana zazzabi Kafin ta samu ta warware, duk wata kulawa wacce mace take bukata awurin miji to sadiq yana bata ita gashi kwana bakwai zaiyi mata saboda itama bata taba aureba,
Babu laifi ta dan sake dashi saboda mutumne mai raha da faran faran, har ya gama yi mata kwana bakwai dinta ya koma gidan uwargidansa bai gundireta saboda yanda yake tarairayarta yana bata kulawa, kuma aranar ya kawo mata yaranshi domin su tayata zama ko zasu samu damar dauke mata kewar rashinsa,
Tana kitchen tana aiki ya shigo ahankali ya sadado yazo ya rufe mata fuskarta, murmushi tayi ta zame hannunshi tana dariya,
“Ai naganeka”
Juyo da ita yayi yana murmushi,
“Bawani nan”
“Sannu da zuwa, mu karasa falon”
Hannunta ya kama suka fita yana cewa “hotunan bikin nakawo miki an wankosu”
Zama tayi agefensa yafara zaro mata hotunan tana gani,
“Woww handsome” tafada ahankali daidai lokacin da tazo kan hoton Lamido kaninshi,
“Wannan hadadden gayen fa? Waye?” Ta tambayeshi tana kallonsa,
“Brother nane jiya ya koma kenya amma ya kusa dawowa ma gaba daya, ya akayi?”
“Gaskiya yafika kyau wallahi, nidai ban yarda ba kodai exchange za ayi? Tafada cikin tsokana,
“Ehh ayi nabar masa dama ai shine karami amma idan kin shirya zama da kishiyoyi saboda matanshi biyu kinga zaki zama ta uku sannan kuma zai karo ta hudu nan gaba”
Zubawa hoton ido tayi gabanta yana faduwa aranta tana yaba kyau irin na lamido gashi dan gayu na karshe,
“Dagaske matanshi biyu?” Ta tambayeshi,
“Wallahi dagaske”
“Um mudai ba haka muka so ba kanin miji yafi miji kyau, gashi wannan hausar tayi tasiri akanmu kanin mijinmu yafi mijinmu kyau”
Murmushi sadiq yayi yaja hannunta yana cewa, “bawani kyau da yafini kawai dai yafini rashin ji”
Tun daga lokacin ta shiga tsokanarshi cewar kaninshi yafishi kyau ita da tasan da wannan kanin nashi da tafasa auren shi ta auri kanin, murmushi kawai yake yi idan yaji ta fadi haka sai yace ai yanzun ma yaci girma ya barwa kanin nashi, kullum haka suke rayuwarsu cikin nishadi da girmama juna,abdallah kuwa kullum tana makale awaya dashi suna hira domin ba karamin missing dinshi tayi ba.
*
Da damuwa mai mutukar yawa Lamido yakoma kenya amma yakasa fadawa kowa damuwarsa, yana komawa yakoma harkar shaye shayen da yadaina, gashi wani irin ciwon kai yake fama dashi dolensa sai da ya ziyarci asibiti, koda likita ya dubashi jininsa yayi mugun hawa saboda damuwa da bacin ran dake addabarsa,
Yanke mu’amalarsa yayi da kowa domin tunda ya dawo baiyi waya da gida ba domin hatta bash sau daya suka yi waya ya cire sim din ya ajiye wayar, matanshi ne ma wani lokacin yana chtn dasu ta facebook idan ya bude system dinsa.
Haka rayuwa taci gaba da tafiyar masa cikin kunci da bacin rai har lokacin zana jarabawarsa ta karshe tayi, kullum cikin shan abun maye yake neman mata kuwa kamar beyi aure ba.

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.