RUWAN KASHE GOBARA! 47

0 136

_47_

Murmushi Xahar tayi taje ta dauko masa ruwa ta ajiye tana dan kakkawar da fuskarta alamun jin kunya,
Ya dan jima agidan kafin ya fito yayiwa suhaima sallama ya tafi, nan Xahar tafara santin kyawunsa tana fadawa yayarta, murmushi suhaima tayi tace,
“Ke kuwa Xahar me zakiyi dashi matanshi fa biyu sannan baya ji duk gidansu marigayi babu marar ji kamarsa neman mata, shaye shaye, duk halinsa babu na dauka”
“Kai anty wallahi nidai ya tafi dani yanada kyau sannan babu wanda ma zai ganshi yayi tunanin yayi aure balle har ace yanada mata biyu”
“Dan kyau kam Lamido yanada kyau domin duk cikin yayan innah yafi kowa kyau matsalarshi kawai baya ji tun kafin ayi masa aure yake bibiyar mata ke wannan dalilinne ma yasa akayi masa aure har mata biyu”
Mikewa Xahar tayi”nidai wallahi naganshi nayaba so babu ruwana da wani halinshi”
Daki ta wuce bata jira amsar da suhaimat zata bata ba.
Gida Lamido ya koma yaje ya zauna ya huta Sati dayan nan da baiyi aski ba har gashi ya dan taru a fuskarsa,
Zama yayi a tsakiyar matanshi kowacce tana bashi kulawa, yana nan tare dasu har dare sai alokacin yafita domin zuwa ganin ikhlas,
Tana kwance asaman kujera tana tunanin mijinta Lamido ya shiga cikin falon,
“Assalamu alaikum” yafada acan kasan makoshinsa,
Dagowa tayi tana amsa sallamar ahankali,
Zama yayi acan nesa da ita,
“Sannu da zuwa” tafada tana kokarin tashi zaune,
“Yawwa ya jiki?” Ya fada yana kallon screen din wayarsa,
“Da sauki” ta bashi amsa,
“Hello bash ina kajene? Ok mu hadu to” ta jiyoshi yana waya,
Yana nan zaune har hajiya tafito suka gaisa ya mike yafita yana yiwa hajiya sallama, tun daga ranar gidan ya zame masa wurin zuwa domin kullum sau hudu yake zuwa idan kuma bai samu dama ba yazo sau uku, bashida buri illa na yaga ikhlas ta samu lafiya kuma ta haihu lafiya,
Kullum cikin siya mata kayan makulashe yake da sauran kayan bukata wannan dalilinne ma yasa matanshi suka fara saka ido akai domin kullum ahanyar zuwa wurin ikhlas yake, yanzunma shiryawa yake yana kokarin fita fadila ta shigo dakin tana kallonshi,
“My Lamido ina zakaje?” Tafada a zuciye,
“Zanje nagano ikhlas ne” yafada cikin rashin damuwa,
“Amma naga dazun nan da yamma ka fita kace ganinta zakaje yanzu kuma kazo kana cewa sake zuwa ganinta zakayi, agaskiya mu mun kasa gane abinda kake nufi saboda kullum baka da wata magana sai tata, idan tausaya mata kake yi ai ba ita kadai aka mutu aka bari ba, ga anty suhaima nan asalima ita tafi cancanta daka tausayawa saboda ya tafi ya barta da marayu har guda hudu..” Ta karashe maganar zatayi kuka,
Tunda tafara maganar kallonta kawai yake har ta gama, batare da yace da ita komai ba ya juya ya fice, wani takaicine ya lullube fadila domin shi dama Lamido matsalarshi kenan sai kayi masa magana idan bata gamsheshi ba ko tanka maka bazai yi ba sai yayi banza dakai ko kuma yatashi yabar maka wurin,
Fita tayi tana kuka ta nufi dakinta tana sharar hawaye.
Kai tsaye gidan Lamido ya shiga tun daga kofar falon yake jiyo sautin radiyo ana sauraren wa’azi,
Shiga yayi ya iske hajiya sai bambami take yiwa ikhlas kan ta tashi taci abinci amma taki,
“Yawwa gwanda da kazo ni ina jin nakusa tafiya nabar gidan nan saboda yarinyar nan bata jin magana bata son cin abinci ko kadan alhalin mace mai ciki sai da abinci” hajiya tace dashi,
“Hajiya dauko abincin zata ci” yabata amsa tashi hajiya tayi ta fita tana fita ya karasa inda take,
“Tashi kici abincin nan, meyasa ke bakya gudarwa kanki matsala ne? So kike cikin jikinki ya samu matsala? To wallahi idan kika bari cikin nan ya samu matsala bazan yarda ba” yafada cikin kufula,
Kallon mamaki tabishi dashi tab irin wannan fada haka sai kace shi yayi cikin, to inaga kuma idan cikin nashine kenan Allah ne kadai yasan dokokin da zai kafa,
Hajiya ce ta dawo dauke da filet tazubo shinkafa ta da miya, zama yayi ya tisata agaba tafara cin abincin har taci rabi amma sam bata jin dadinsa,
Wani amai ne ya taho mata batare data shiryaba take ta amayar da abinda ke cikinta gaba daya,
Cikin tashin hankali Lamido yake kallonta har ta gama jirine ya dauketa ta fadi sharafff,
Cikin sauri ya isa kanta yana leka fuskarta.

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.