RUWAN KASHE GOBARA! 48

0 172

_48_

Cikin sauri ya isa kanta yana leka fuskarta,
“Ikhlas,ikhlas..” Hajiya ta kira sunanta cikin tashin hankali,
Ko motsi batayi ba ganin haka yasa lamido gigicewa,
Hannunshi yakai ya juyo fuskarta numfashinta gaba daya ya dauke,
Mikewa yayi tsaye ya zaro wayarsa yafara kiran dr,
Ruwan sanyi hajiya ta dauko tafara sheka mata amma shiru,
Suna nan tsaye har dr yazo,
“Ashigar da ita cikin daki” dr ya fada yana kallonsu,
“To ni ai ba iya daukarta zanyi ba” hajiya tafada adiririce, daukarta lamido yayi yai hanyar dakinta da ita, akan gadonta ya shimfidar da ita ya juyo yana kallon dr,
“Yarinyar nan cikin nan yana bata wahala abin tausayi” lamido yafada acikin ranshi,
Dubata dr yayi ya daura mata ruwa ya rubuta magunguna ya juyo yana kallon Lamido “meyasa bata cin abinci? Arinka bata abinci tana ci sannan ta rage damuwar da take damunta” likita yafada tare da fita,
“Ikhlas amma kina shan karin ruwa” hajiya tafadi tana kokarin zama akusa da ita,
“To ya za ayi hajiya sai hakuri kawai” lamido yabata amsa ya fita,
Chemist yaje ya siyo magungunan ya dawo, har lokacin ikhlas bata iya bude koda idanuwanta ba, zama yayi a falo yana jiran ta tashi,
Tafi awa daya tana bacci kafin ta tashi lokacin ruwan da aka daura mata ya kare,
“Sannu ikhlas, dan Allah ki cire damuwa aranki kinji” hajiya tace da ita,
Daga kai tayi ta shiga toilet tafito jiri na daukarta, komawa tayi ta kwanta tana haki kamar wacce tayi tseren gudu,
Tashi Lamido yayi yayiwa hajiya sallama ya tafi,
Zuciyarsa cike fal da tausayin abar sonshi ji yake kamar ya cire mata ciwon ya dawo dashi jikinsa,
Lokacin da yaje gida fadila na zaune afalo tayi tagumi ta zubawa kofa ido tana ganinshi ta mike tsaye idonta jajur alamun tasha kuka ta more,
“Fadila lafiya kike zaune anan?” Ya tambayeta cikin kulawa,
Maimakon ta bashi amsa sai kawai ta fashe da wani kukan, janta jikinsa yayi ya rungumeta, ahankali yake tafiya da ita tana jikinsa yana rarrashinta har zuwa cikin dakinta,
Agogon bangon dakin ya kalla karfe 11:30,zaunar da ita yayi agefen gadon ya sunkuya agabanta ya kamo hannayenta yafara rarrashinta,
“My fadila kiyi hakuri pls, karki yi fushi da mijinki kinji..” Yafada cikin sigar lallashi,
Mantar da ita bacin ran da take ciki yayi ta hanyar nuna mata soyayya, sai da ya tabbatar da yabata kyakkyawar kulawa sannan ya tashi ya fice daga cikin dakin ya tafi nashi,
Bathroom ya shiga yayi wanka ya fito ya kwanta nan kuma tunanin ikhlas ya addabeshi, juyi ya rinka yi har ya samu bacci ya daukeshi,
Washe gari ko breakfast baiyi ba ya fice ya tafi dubo ikhlas, lokacin da yaje ya ganta yasamu ta dan warware alamun sauki ya samu tana zaune afalo tana cin wainar shinkafa da miya,
Da sallama ya shiga cikin falon ya zauna akan kujera,
“Sannu da zuwa, ina kwana?” Tafada ahankali duk kunya ta kamata ta kasa sakewa taci wainar,
“Yajiki?” Ya tambayeta batare da ya kalleta ba,
“Da sauki” tabashi amsa ahankali,
Babu wanda ya sake magana acikinsu har hajiya ta fito daga cikin kitchen tana dauke da filet mai dauke da waina da miya aciki,
“Barka da zuwa, ga waina”
“Hajiya ina kwana? Ya mai jiki? Allah ya bata lafiya”
“Ah jiki yayi sauki, amin amin, ga waina”
Daukar filet din yayi yafara cin wainar yana sauraren maganar da hajiya take yiwa ikhlas,
“Ki dauko maganin kisha sarkin yan kin magani” hajiya tace da ikhlas cikin fada,
Dakyar ta mike ta shiga daki ta fito rike da ledar maganin tazo ta zauna sai yayyatsina fuska take yi da haka ta samu tasha maganin,
Lamido ya dan jima agidan kafin ya tafi ta gidan suhaima ya biya yaga yara sannan ya fito ya nufi gidan baffa acan ya kwashe lokuta masu yawa sai yamma sannan yabar gidan ya nufi gidansa.
Kasancewar yau girkin ihsan ne ya sanyashi samunta acikin falo tana zaune zaman jiranshi,
Kallonta yayi tasha kwalliya tayi kyau amma sai cika take tana batsewa,
“Darling yanzu ka kyauta kenan? Tun safe kabar gidan nan baka tashi dawowa ba sai yanzu” tafada tana zumburo masa baki,
“My ihsan ikhlas ce bata da lafiya shine naje na dubota”
Harararshi tayi ta dauke kanta, “kuma shine zaka tafi kaje ka zauna”
Murmushi yayi yakamo hannunta yana kallonta ya fuskanci daga fadila har ihsan din duk kishi suke da ikhlas, shi kansa baisan wanne irin zama zasuyi ba su ukun idan ya auri ikhlas,
“Ai dubiya ce ihsan kuma kinga yanzu babu wanda zai lura da ita sai ni”
Dagowa tayi ta kalleshi, “shikenan Allah ya bata lafiya” hannunshi ta rike ta rakashi dakinshi sannan ta fito.

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.