RUWAN KASHE GOBARA! 51

0 160

_51_

Fita lamido yayi sai alokacin ya tuna da cewar ashe fa yabar Xahar dasu sayyid a mota,
Bata rai xahar tayi ta hade fuska ita adole taji haushin zaman da lamido yayi, bai ko kalleta ba ya shiga motar ya tayar yafara tuki,
“Haba Lamido kuma sai katafi kabarmu munata zaman jiranka alhalin ga zafin rana” xahar tace dashi kamar zata sa kuka,
Batare da ya kalleta ba yace,
“Ai da sai ku kunna ac”
Babu wanda ya sake magana acikinsu har suka tasamma supermarket din sai dai amma ita xahar sam bata ji dadin amsar da ya bata ba, shiru tayi ta kyaleshi saboda ta fuskanci shima yanaji da wulakanci,
Packing yayi a harabar supermarket din suka firfito suka shiga yana dauke da aysha akan kafadarshi kasancewar itace karama,
Cewa yaran yayi kowa ya dauki abinda yake so nan suka je suka ciko karamin basket da kayan ciye ciye,
Yana son ya daukawa iklas kayan zaki amma yana tsoron kar yaje ko masu ciki basa sha, wayarshi ya ciro yafara kiran dr yana dagawa ya tambayeshi,
“Dr dama tambayarka zanyi masu ciki suna shan zakine?”
Daga can bangaren dr yafara bashi amsa,
“Lamido mudai asonmu kar susha saboda idan sunzo haihuwa to dole ne sai sun zubar da wannan zakin”
“Ok to dr amma kamar ice cream fa?” Lamido ya sake tambayarsa,
“Ehh amma kar asha dayawa saboda shi ciki zafine dashi ta ciki to amma ba ason arinka shan sanyin da yawa gudun kada yaron ya samu matsala”
“Ok thank you dr”
Kashe wayar yayi yaje ya dauko ice cream kwaya daya karamar roba,
Wurin biyan kudi yaje shida yaran aka fara lissafi nan yaga ita xahar bata dauki komai ba saboda kunya, da kanshi yaje ya dauko wani turare dan 5000 yazo ya biya ya bata, nanfa dadi ya rufeta ganin lamido ya fara damuwa da ita,
Gida ya koma dasu ya ajiyesu ya juya ya nufi gidan ikhlas tana nan zaune daga ita sai zani iya kirji da hijab da alama daga wanka ta fito,
Da sallama ya shiga ya mika mata robar ice cream din,
Kallo tabishi dashi sannan ta sake kallon yar mitsitsiyar robar ice cream din da ya bata,
“Wannan ne ice cream din?” Ta tambayeshi cikin karfin hali,
“Ehh shine idan kuma kin raina ki bani kayana” yafada bayan ya juya ya fara tafiya,
“Ni ba rainawa nayi ba amma abinne da mamaki kamar wanda aka bawa sadaka?”
“Wannan dinma sai da na kira dr na tambayeshi badan haka ba da bazan kawo miki ba” yafada tareda karasa ficewa,
“Uhm kaji masu d’a komai kace d’anka komai d’anka” tafada aranta tareda bude robar ice cream din tafara diba tana sha.
Lamido kam wannan yar maganar da sukayi da ikhlas shine yasake tayar masa da dafin ciwon sonta,
Driving yake yana nishadi har ya karasa gida, ko agidan ma saida su ihsan da fadila suka gane yana cikin farin ciki.
Kullum yana hanyar gidan ikhlas gashi yafara service sai dai bai fiya fitaba koda yaushe yana gida,
Yau sam bai leka ikhlas ba tun safe har dare dan haka yana yin sallar isha ya tashi ya fita lokacin da yaje gidan kamar kullum ita da hajiya ya samu a tsakar gida sun shinfida tabarma ikhlas na kwance tana shan kankarar pure water ita kuma hajiya tana zaune,
Zama yayi suka fara gaisawa da hajiya yana kallon ikhlas,
“Meye wannan kike sha?”
Shiru tayi bata amsa masa ba ganin haka yasashi juyawa ga hajiya,
“Hajiya me naga tana sha?”
“Kankara mana, ai na hanata shan kankarar nan amma ikhlas taki ji ina jin so take ta haifo yaro mai limoniya, kullum cikin yi mata fada nake amma bata dauka”
Tashi yayi yaje ya mika mata hannu “bani nan”
Mika masa tayi tafara kokarin tashi zaune,
“Nifa dan bakuji zafin da nake jin cikina yana yimin bane” tafada tana kumburo baki,
“Fridge din ma daukeshi zanyi inyaso naga abinda zaki sha, ke kullum bakya jin magana daga an hanaki wancan sai ki koma wancan ki bari idan kika haihu sai ki zamar da kankarar abincinki kiga idan zamu yi miki magana”
Shiru tayi masa har ya karaci fadanshi ya tafi domin ta fuskanci shi ta lafiyar jaririnshi kawai yake bata ita ba, tun da ya hanata shan kankara suka shiga yar tsama dashi amma kullum yana zuwa gidan fiyeda sau biyu,
Watan cikinta tara da kwana biyu tafara nakuda nan hajiya ta kira lamido yazo suka tafi asibiti, duk hankalinshi ya gama tashi saboda ganin yanda ikhlas take yi,
Suna zuwa aka Shiga dakin haihuwa da ita, awarsu biyu da zuwa ta haihu amma kuma sai dai ta zubar da jini da yawa dan haka aka fara tunanin kara mata,
Ko jaririn bai tambaya ba ta lafiyar ikhlas yake yi,lab sukaje da dr din aka gwada jininsa aka diba domin karawa ikhlas,
Suna nan tsaye shida hajiya da innah aka fito musu da jaririn wanda yake fari sol mai kamada mahaifinshi sak,
Ai innah naganin jaririn sai ta fashe da kuka shi kansa lamido sai da yayi kwalla.

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.