RUWAN KASHE GOBARA! 52

0 166

_52_

Daukar jaririn lamido yayi yai masa addu’a ya mikawa hajiya shi ya juya ya fita,
Ba afito da ikhlas ba sai bayan awa daya sai alokacin su innah suka shiga ganinta, tayi jugum tana tunanin marigayi,
Sannu dukkaninsu suka hau yi mata har lamido ya shigo,
Dagowa tayi ta kalleshi jin ko sannu bai yi mata ba sai ma karbar jaririn da yayi ya rungume yana fara,a ita ta rasa gane kan wannan iko irin na lamido.
Zuwa dare aka sallamesu, kai tsaye gidan innah suka wuce, dakin kusa da na innah anan aka sakawa ikhlas kayanta dana jaririnta,
Komai wanda zasu bukata an siyo, lamido yana ajiyesu ya juya yanufi gidanshi acan yaje yana yiwa su fadila maganar haihuwar ikhlas,jin ya damesu da maganar yasasu jin haushi kowacce tasha kunu taki kulashi.
Tunda aka yi haihuwar yake zirga zirga har suna yazo, ana igobe suna yaje gidan, lokacin yan uwan ikhlas sun zazzo su matan yayunta dasu ammi da sauran matan gidan,
Afalo yasamu baffa da ikhlas suna maganar sunan da za asakawa yaron,
“Yawwa lamido dama kai muke jira na tambayeta sunan da za asakawa yaron tace abari kazo kaine babanshi” baffa yafada cikeda jin dadi,
Zama lamido yayi yana kallonta sai ciccije lebe take kamar marar lafiya,
“Baffa sunanshi Abubakar Saddiq sunan mahaifinshi”
“Yawwa to bakinku yazo daya da ita domin itama haka tace amma tace abari kazo aji”
Mikewa baffa yayi ya fita hakan yasa lamido matsawa inda take,
“Baki da lafiya ne?”
Kai ta daga masa
“Meyake damunki?”
“Ciwon ciki”
“Ko zamuje asibiti?”
Girgiza kai tayi alamun a,a,wucewa yayi ya fita ita kuma ta koma daki ta kwanta amma kuma ciwon sai karuwa yake ganin haka yasata daukar wayarta ta karbi wayar hajiya ta kwafi no din lamido ta kira,
Yana driving ta kirashi, sabuwar no yagani dan haka ya share, sai da ta kirashi sau uku baiyi picking ba, ganin haka yasata tura masa text massage,
Jin shigowar massage wayarshi yasashi dauka ya duba,
_Abban sadiq kazo ka kaini asibitin har yanzu cikin nawa bai daina ciwo ba._
Shine abinda yaga an rubuta, yana ganin sakon ya rude, da saurinshi ya koma gidan, yana zuwa ta fito suka tafi,
Asibitin data haihu ya kaita acan aka dubata aka bata magani suka dawo gida.
Washe gari da safe aka yi suna duk da cewar basuyi wani gayya ba amma dangi sun taru, matan lamido kuwa dakyar suka zo gidan sunan amma sai kumbure kumbure suke yi, haka taron sunan ya tashi lafiya lafiya.
Gidan yayi mata mutukar dadi saboda duk inda ta waiga danginta take gani tako ina,
Karfe 8:30 nadare suna zazzaune adakinta itada yan uwanta taji wayarta tafara ruri tana dubawa taga *ABBAN SADIQ* kamar yadda ta rubuta, ahankali ta daga wayar,
“Kawo min sadiq zan ganshi” taji yafada tun kafin ta yi magana,
“To amma yanzu wanka ake yi masa Bari ashiryashi sai na kawoshi” tabashi amsa tana satar kallon hajiya wacce take nannade sadiq a towel bayan tagama yi masa wanka da ruwa mai dumi,
“Waye yake nemansa?” Hajiya ta tambayeta tana jawo kayan kwalliyar sadiq din,
“Abbanshi ne” ikhlas tabata amsa,
Shiryashi akayi cikin kayan sanyi ikhlas ta daukeshi ta fita,
Yana zaune shi kadai acikin falon yasha kananan kaya wadanda suka yi mutukar amsarshi, brown din trouser da blue din t shirt mai gajeren hannu,
“Sannu da zuwa” tafada tana kokarin mika masa sadiq,
“Oyoyo saddiqu na” yafada batare da ya amsa mata ba ya karbi sadiq din,
“My boy ya ka wuni?” Yafada yana kamo yan yatsun jaririn yana sawa abakinshi,
Tsayawa tayi kawai tana kallonshi yanda ya daddage yana yiwa sadiq magana maganar da bai saniba,
Atishawa sadiq yafara jerewa har sai da yayi guda hudu,
“Alhamdulillah, sorry my boy,mura kake yi ko? Ni dama nasan dole kayi mura saboda kankarar da aka rinka dura maka lokacin da kana cikin ciki gashi yanzu ka fito duniyar ma amma baka huta ba sai wankan dare ake yi maka”
Dagowa yayi ya kalli ikhlas “dan Allah adaina yiwa yaron nan wanka da daddare”
“To” ta amsa masa atakaice,
Agogo ya kalla karfe tara daidai nadare,
“My boy inje in tafi ko? Sai da safe bye bye”
Mika mata shi yayi ya tashi ya fita, binsa da kallo ikhlas tayi,
“Ikon Allah baya karewa” tafada acikin zuciyarta,
Cikin dakinta ta koma inda yan uwanta suke zazzaune sunata shan hira,
“Sai yanzu yatafi?” Ammi ta tambayeta,
“Ehh dama danshi yazo gani” tafada tana kwantar da sadiq, kwanciyar itama tayi domin yin baccin.
Washe gari wurin misalin karfe 10 lamido yaje gidan daidai lokacin ana yiwa sadiq wanka sai kwala kuka yake yi,
Tunda ya shiga falo yake jiyo kukanshi nan yafara jin kukan har cikin ransa, kasa hakuri yayi ya leka dakin, hajiya yagani tana yiwa sadiq wanka ita kuma ikhlas tafito kenan itama daga wankan, da sauri taja baya ta koma cikin toilet din domin daga ita sai daurin kirji kanta babu dankwali kuma bata yafa komai ba,
“Hajiya meya sameshi yake kuka?”
“Wai wanka ake yi shine yayi kamar zai tsaga gidan nan dan ihu” hajiya ta bashi amsa,
Karbarshi yayi bayan hajiya ta nadeshi acikin towel,
“To ya isa zo muje” sabashi yayi akafada ya fita dashi yana jijjigashi.

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.