RUWAN KASHE GOBARA! 55

0 156

_55_

Lamido na cikin dakinshi duk farin ciki yagama lullubeshi, wai yau shine ya zama mallakin pretty bayan ya jima da fitar da rai da samunta,
Wanka ya shiga yayi ya fito yafara shiryawa, yana tsaka da taje sumar kanshi ihsan ta shiga cikin dakin tana dan ciccin magani,
“Sai ina?” Tafada tana kallonshi,
“Zanje unguwa ne?” Yabata amsa,
“Yaushe amaryar tamu zata tare ne?” Ta sake tambayarsa,
“Sai nan da three months domin ina son sadiq ya danyi wayo kafin lokacin”
Tabe bakinta tayi ta juya ta fita tana murna aranta kuma fata take Allah yasa auren ya mutu kafin ta tare din,
Kananan kaya lamido yasha, jan wando da bakar t shirt an rubuta polo, jan takalmi sau ciki ya saka ya fito yana ta faman kamshin turare, yau ko abinci yakasa ci saboda tsabar murna,
Lokacin da ya fito su fadila suna zaune a falo suna kallo,
“Ni na fita” yafada gamida saka kai ya fice,
Babu wacce ta tanka masa har ya fice daga falon,
“Wurinta fa zai tafi” inji fadila,
“Nasani ai, yayita zuwa” ihsan tafada cikin jin haushi, nan suka cigaba da tattauna maganar kowaccensu ranta babu dadi.
Lamido na fita wurin bash ya wuce, akofar gidansu ya sameshi yana zaune akarkashin wata bishiya,
“Kaga sabon ango” bash yafada cikeda tsokana tareda mikawa lamido hannu,
Hannun bash ya kama yana murmushi “bash kaga wani ikon Allah ko? Wai ashe dai da rabon pretty matata tace..”
Kallonshi bash yayi cikeda mamaki “on top kar dai kace min dama itace matar da yayanka ya aura?”
“Wallahi bash itace, ai ban taba shiga tashin hankali da damuwa ba kamar wannan lokacin,ko kasan har bp dina sai da ya hau”
“Amma lamido meyasa kaki fada, meyasa kabar wannan sirrin acikin ranka kai kadai bayan kasan dan uwanka zai iya mallaka maka dukkan abinda ya mallaka,meyasa kaso cutar kanka? Meyasa za kayiwa kanka illa?” Bash yafada cikeda tausayin abokinshi,
“Bash sanin Broz zai iya mallaka min duk abinda ya mallaka shiyasa nayi shiru saboda bana son na shiga hakkinsa domin ban san irin son da shima yake yiwa ikhlas ba, sannan ka sani alokacin da na matsa sai na aureta to da zan iya mutuwa tunda gashi harda rabon yaro atsakaninsu,nasan ina son ikhlas soyayyar da bazan iya taba kwatantawa wata ya mace ba, to amma bana son kuma na takurawa dan uwana, dayake akwai rabon aure a tsakaninmu kaga sai Allah ya karbi rayuwarsa alokacin da bamu shirya rabuwa dashi ba nikuma sai Allah ya mallaka min ita alokacin da ban taba tsammani ba, lallai Allah ya cika mai hikima domin shine yake bawa mutum abinda yake so amma ba alokacin dashi mutumin yake soba”
Kwallace ta ciko masa ido yasa hannu ya goge yana murmushi,
“Ina tayaka murna on top Allah ya baku zaman lafiya” bash ya fada yana dafa kafadarsa,
“Amin bash nagode, bari nawuce”
“A’a mu wuce dai dan nima binka zanyi”
Tare suka shiga mota suka fita suka nufi gidan kallon ball.
Sai da akayi sallar magrib sannan Lamido ya nufi gidan baffa,
Dakin innah ya fara shiga suka gaisa sannan ya fito ya shiga dakin ikhlas, tana zaune ta goya sadiq tana goge kayan sawarshi ga waya a makale a kunnenta tanayi,
“Abdallah nace naji… Yawwa bawan Allah maza kagaida yaya Hussain kaji”
Sai da lamido yaji gabanshi yafadi rass wanda bai san dalili ba, wayar ta katse ta dago tana kallonshi,
“Abban sadiq sannu da zuwa” tafada cikin muryarta mai dadin gaske,
“Yawwa,sadiq bacci yake yi?” Ya fada yana shirin zama agefen gadonta,
“A’a idonshi biyu yanzu na goyashi” tafada ahankali,
“Miko min shi”
Tashi tayi ta sauko dashi ta mika masa, karbarshi yayi ya kwantar dashi akusa dashi ya sunkuya ya fara yi masa wasa, daga shi har sadiq din sai dariya suke faman kyakyatawa kamar wasu sabbin kamu,
Tana zaune tana gugarta tana sauraren lamido da sadiq, domin wani lokacin sai taji lamidon yana yiwa sadiq din magana sai kace babba,
“Saddiqu na bari naje salla ko? Ko zaka rakani?, yawwa saddiqu na yi zamanka naje na dawo, bye bye”
Mikewa yayi ya mika mata shi, “ungoshi naje nadawo”
Karbarshi tayi tabishi da kallo har yafice, murmushi tayi aranta tana raya cewa shima lamido har yau akwai kuruciya atare dashi saboda abubuwan da yake yi idan ya dauki sadiq,
Tana nan zaune tasamu ta kammala gugar ta kwantar da sadiq ta fara sallar isha, ko raka’a biyu bata kaiba taji sadiq ya fara kuka, sallarta taci gaba dayi, tana kaiwa raka’a ta uku lamido ya shigo,
“Sadiq meya sameka?” Jin bai daina kuka ba yasa lamido kallar wurin da take sallar,
“Kinga yi sallama ki yi feeding din yaron nan idan yayi shiru sai kiyi sallar..”
Sallarta taci gaba dayi shikuma sadiq sai kuka yake tsalawa, haushi ne ya kama lamido domin jin kukan yaron yake har cikin ranshi, zaman tahiya tayi tai sallama ta kuma mikewa domin gabatar da shafa’i da wutri,
Tashi lamido yayi yaje ya sha gabanta, “me zakiyi? Wallahi baki isaba babu sallar da zaki sake yi har sai kin bawa yaron nan nono yasha,kina ganin yaron yana ta faman kuka amma kin kyaleshi saboda rashin tausayi”
Kallonshi ikhlas keyi cikeda mamaki, “karbeshi ki bashi yasha” yasake fada yana mika mata yaron,
“Dan Allah abban sadiq kabarni na idar wallahi yanzu idan sadiq ya kama ban san lokacin da zai koshi ba, cine dashi kamar gara..”
Hijabinta ya fusge “wallahi a’a, ki karbeshi nan da 12 nadare idan ya koshi sai kiyi sallar, may be ma tun fitata yake kukan amma kika kyaleshi dan mugunta”
Karbar sadiq din tayi ta zauna har lokacin lamido yana tsaye akanta ya zuba mata ido yana son yaga tafara feeding din sadiq.

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.