RUWAN KASHE GOBARA! 60

0 295

_60_

Juya masa baya tayi cikeda kunya domin ba karamin kunya yasata taji ba,hannunshi mai mutukar laushi taji yasaka ya kamo nata ahankali,
“Zan samu ruwan zafin?” Ta jiyo muryarshi mai dadi yana yi mata magana,
“Ehh” tabashi amsa a tausashe,tashi yayi yasaka hannuwanshi ya zagayeta,gaba daya jinta take yi acikin jikinshi wanda har ba zata iya wani kwakkwaran motsi ba sakamakon yadda ya matseta ajikinshi,
“Ba kayi salla ba fa abban sadiq” tafadi ahankali kamar me yin rada’, sakinta yayi ahankali ya koma ya kwanta, ba tare data waiwayo ba ta juya ta fice daga cikin dakin ta nufi kitchen,
Ashana ta dauka ta kunna risho ta dora masa ruwan zafin,
“Agaskiya abban sadiq baka da kunya ko kadan wallahi”
Tafadi hakan tana murmushi, tana nan atsaye har ruwan ya tafasa ta juye acikin dan karamin bokiti ta dauka ta nufi cikin dakinta,
Akwance ta kuma samun lamido yasaka hannuwanshi ya zagaye sadig kanshi kuma akan pillow,
“Abban sadiq badai wani baccin ka sake komawa ba?” Ta tambayi kanta acikin zuciyarta,
Toilet ta shiga ta hada masa ruwan wankan ta fito, atsaye ta sameshi yagama cire kayan jikinshi ya rage daga shi sai gajeren wando dark blue,
Kanta akasa ta wuceshi ta koma falo ta kwanta akan doguwar kujera, shidai lamido kallonta kawai yake yi saboda yanda take jin kunyarshi abin yana burgeshi kuma yana kara wutar kaunarta acikin zuciyarsa,
Toilet ya shiga yayi wanka ya fito yazo ya shimfida abin salla,
Zama yayi yai addu’o’i bayan ya idar da sallar, kan gadon ya koma ya rungume sadiq ya koma wani baccin.
Wurin 7:30 ikhlas ta shiga dakin har lokacin dai bacci lamido suke yi shida sadiq, sadadawa tayi ta shiga toilet tayi wanka ta fito ta shirya ta saka doguwar riga ta atamfa kalar yeluwa ta dauki turare ta fesa,
Falo ta sake komawa ta zauna nan wayarta tafara neman agaji, tana dubawa taga yaya Hussain ne dan haka ta daga cikeda murna, gaisawa kawai suka yi ya hadata da abdallah suka fara hira,
Sun dade suna hira sannan suka yi sallama ta kashe wayar,
Kukan sadiq da tafara jiyowa ne yasata tashi ta nufi dakin, tana shiga taga lamido ya tashi yana shirin daukar sadiq din,
“Ina kika tafi kika bar yaro yana kuka?” Ya jefo mata wannan tambayar yana mai kallonta domin ba karamin kyau tayi masa ba, kwalliyarta ta tafi dashi dari bisa dari,
“Ina falo ne” ta bashi amsa tareda mika hannu ta amshi sadiq din,
“Abban sadiq ina kwana?” Tace dashi ahankali,
“Lafiya lau” ya amsa mata gamida kwanciya ya juya mata baya, falo ta fita ta zauna tafara feeding din sadiq,murmushi lamido yayi ya sake kwanciya yana mamakin ikhlas ganin har yanzu bata daina boye mishi abincin sadiq ba shi ya rasa wacce irin kunya gareta.
Sai da ta tabbatar da ya koshi sannan ta kwantar dashi taje ta dora ruwan zafi tazo tafara yi masa wanka,tana fara yi masa wankan yahau kuka,
Kawai sai ganin lamido tayi ya fito daga dakinta da sauri kamar wanda zai tashi sama,
“Wai kukan me wannan yaron yake yine?” Yafada cikin kunar rai domin yanzu a duniya idan akwai abinda ya fi tsana to kukan sadiq ne, yana mutukar kaunar yaron har cikin ranshi, yanda yake jin son yaron aranshi ji yake ko dan cikinshi ba lallai ya soshi haka ba,
“Wanka fa kawai ake yi masa shine yaketa wannan ihun” ikhlas ta bashi amsa cikeda mamakin lamido saboda lamarinshi yanzu mamaki yake bata kwata kwata bashida sauki indai akan sadiq ne,
“Kinga yi masa ahankali” kusa da bahon wankan sadiq din yaje ya tsaya yana kallonsu, shima sadiq din yana ganin lamido ya sake tsaga kuka yana son lamido ya daukeshi,
Ita dai ikhlas abin mamaki yake bata saboda yanda sadiq ya gane lamido,domin ko goyanshi tayi to yana ganin lamido zai fara mutsu mutsu yana kuka ala dole sai yaje wurinshi,
Hanzartawa tayi ta gama yi masa wankan ta sakashi cikin towel ta mikawa lamido shi, ai yana karbarshi taji sadiq yayi shiru ya daina kukan kamar ba shine da yaketa tsaga kuka ba kamar zai kashe musu dodon kunne,ita dai bata san irin soyayyar dake tsakanin lamido da sadiq ba wannan tabarwa Allah domin shine kadai yasan hakan,
Juyawa da sadiq lamido yayi zuwa cikin dakinta ya zauna a bakin gado ya dauki man shafawar sadiq yafara shafa masa yanayi yana yi masa wasa,
“Kaine sadiq? Kasan sunanka?… Saddiquna ko”
Cikin dakin ikhlas ta bisu ta samesu sunata aikin dariya,
“Dauko kayanshi asaka masa” Yace da ita,
Wurin kayan sadiq taje ta dauko masa bakar riga da brown din wando ta dauko safa da hula farare tazo ta karbeshi,
Da kuka tasamu ta shirya shi ta mikawa lamido shi, juyawa tayi zata fita har takai bakin kofa taji muryar lamido yana yi mata magana,
“Ina zakije?”
“Falo” ta bashi amsa,
“Me zakiyi?”
“Zama zanyi” ta mayar masa da amsa,
“To dawo nan ki zauna” yafada bayan ya juya ya rungume sadiq, juyowa tayi ta dawo cikin dakin taja stool din mudubi ta zauna tana kallon Lamido da sadiq sannan tana sauraron shirmen da suke yi sadiq yanata kyakyata dariya,
Bacci sadiq din ya koma dan haka lamido ya kwantar dashi ya juyo yana kallon ikhlas wacce ke zaune ta sunkuyar da kanta tana wasa da zoben dake hannunta wanda sam bata san a inda ta sameshi ba,
“Kinga” ya fadi ahankali, dagowa tayi ta kalleshi amma sai tayi saurin sunkuyar da kanta ta saukar da kwayar idanuwanta kasa, ita ta kasa ganewa lamido domin gaba daya yanzu ya sauya mata ya koma wani kala na daban. Tashi tayi ta matsa inda yake ta zauna a dan nesa dashi,
“Gani” tafadi ahankali,
“Ahakan zan fada miki maganar? Kalli fa yanda kika yi nesa dani sai kace wani abin zan yi miki”
“Kayi hakuri abban sadiq ba haka bane ina sone naje na dora mana breakfast..” Ta bashi amsa wanda har lokacin idanuwanta a kasa suke ta kasa kallonshi,
“Kibar wannan breakfast din kizo kiji abinda zan fada miki”
“Abban sadiq ka fada min ina daga nan ai zanji..”
“Shikenan idan ba zaki zo ba tashi ki tafi”
Ganin kamar ranshi ya dan baci ya sanyata matsawa kusa dashi,
“Kayi hakuri gani..!”
Juyawa yayi ya kalleta har lokacin kanta yana kasa tana wasa da yan yatsunta.

WhatsApp: 08161892123

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.