RUWAN KASHE GOBARA! 61

0 381

_61_

 Murmushi ya danyi ya saka hannunshi ya dago da fuskarta,
“Kalleni..!” Yafadi ahankali, kasa kallonshi tayi ta lumshe idanuwanta,
“Ki kalleni…” Ya sake fada yana kallon kyakkyawar fuskarta,
Dan yatsanshi yasa akan lips dinta yana zagayawa,
“Kinyi kyau sai dai matsalar baki saka jan baki ba why?”
“Babu komai..” Ta bashi amsa,
“Ki rinka saka jan baki zaki fi kyau”
“To” ta bashi amsa har lokacin ta kasa kallon fuskarshi,
Sake matsawa jikinta yayi nan hancinshi yasoma aika masa da fitinannen kamshin dake tashi daga jikinta,
“Wanne turare kike sakawa?” Ya tambayeta yana mai sake shakar kamshin jikinta,
Shiru tayi bata amsa masa ba saboda ta fuskanci ya fara kokarin wuce gona da iri,
Hannunta ya kamo ya makale cikin nashi,
“Ya kika barni inata magana ni daya ne?” Nan dinma shirun ya sake ji tayi, idonshi ya sauke akan lips dinta wadanda suka kasance jajaye duk kuwa da cewar bata saka jan baki ba,amma duk da haka sunyi mutukar jan hankalinshi,
Babu zato taji yayi hugging dinta yafara kissing din bakinta, sunsunkuyar da kanta ta fara yi,gaba daya ta rasa yadda zata yi saboda kissing dinta yake yi ta kowanne sashe dake kan fuskarta zuwa wuyanta,
“Ki rinka saka jan baki da jagira…,ina son irin wannan kwalliyar ciki harda saka wannan abun na saman ido da kumatu,da irin wannan zane zanen da kuke yi a kafa me baki da red…!” Taji yana rada mata acikin kunnenta,
“Kinji..!” Ya sake rada mata, kai ta daga alamun ehh amma ta kasa magana dalilin yagama saukar mata da kasala,
“Kunyata kike ji ne?”
Ya tambayeta bayan ya tarairayota gaba daya ya dorata ajikinshi,
“Uhm…!?” Ya sake tambayarta,
“Na kasa gane wacce irin kunya Allah ya halicceki da ita bayan kuma naji ana cewa idan mace tayi aure ta haihu to kunyarta na raguwa ba kamar lokacin da tana budurwa ba, hakane?”
Girgiza masa kai tayi alamun a’a,
“To yayane?” Ya tambayeta yana kallon idonta wanda sam taki dagasu ta kalleshi,
“Ai kunya bata karewa…” Tace dashi cikin yar karamar muryarta,
“Sai yaushe? Ya tambayeta yana sinsina wuyanta,
“Abban sadiq….” Tafada gamida rike hannunshi,
“Shhhhhh” yace da ita bayan ya dora dan yatsanshi akan lips dinta,
Dolenta tayi shiru ta rike maganar da tayi niyyar yi ta rabu dashi yaci gaba da juyata son ranshi.
Bude idonta tayi ta kalleshi yana kwance ajikinta ya rungumeta tamkar wanda zai koma cikin cikinta,
“Abban sadiq zanje na hada breakfast..” Ta fadi cikeda jin kunyarshi,
“Yunwa kike jine??” Ya tambayeta,
Girgiza masa kai tayi alamun a’a,
“To ni kinga yunwa nake ji sosai…”
Lumshe idonta tayi domin ta gane abinda yake nufi amma ita kuma bazata bari hakan ta kasance agidan surukai ba,
“Kinji abinda nace?”
“Uhm naji” ta bashi amsa,
“To ya za ayi?” Ya sake tambayarta,
“Babu” ta bashi amsa,
“Haba? Rowa zaki yimin?”
“Abban sadiq rana fa tayi wallahi kalli agogo ka gani…!” Ta fada a shagwabance,
“To idan kina son na iya hakura kidaina yimin wannan shagwabar”
Shiru tayi masa bata sake magana ba, matsawa yayi daga jikinta yaje ya rungume sadiq wanda ke kwance agefe,
Tashi tayi da dan kwalinta a hannunta ta fita tana kokarin tufke gashin kanta wuri daya ta nufi kitchen fuskarta dauke da murmushi,
“Ohh abban sadiq kenan.. Rigima taki karewa?” Ta fada acikin zuciyarta tana murmushi,
“To ni yanzu ma me zan dafa ne?” ta tambayi kanta,
Doya ta fere ta soyata da kwai tayi yar sos mai dauke da kwai da hanta aciki,
Acikin flask ta zuzzuba ta dauka ta kai falo, hijabinta ta saka ta dauki na baffa ta nufi sashensa yana zaune da jaridar weekly trust a hannunshi yana karantawa idonshi sanye da farin medical glass,
Har kasa ta tsugunna ta gaishe da baffa ta tashi zata tafi,
“Ikhlas motar Lamido nagani ne awaje?”
Ta jiyo baffa yana tambayarta, ras gabanta ya fadi,
“Ehhh baffa motarshi ce tun safe ya kawota ya ajiye”
“To idan yazo gidan ki turo min shi”
“To baffa” tafada tareda juyawa tayi gaba gabanta sai faman faduwa yake domin bata son baffa ya gano lamido agidan ya kwana.
Dakinta ta shiga ta tsaya tana kallon lamido wanda ke kwance yana bacci yana rungume da sadiq,
Ba karamin kyau taga yayi mata ba domin har acikin barcin ma sai da beautiful points dinshi suka bayyana,
Agefenshi taje ta zauna tana kallonsa akaro nafarko domin bata taba samun damar karewa siffarshi kalloba,
Tun daga kan dan yatsan shi har zuwa gashin kanshi duk sun tafi da tunaninta, hannunshi kuwa gashine zara zara ajiki,
“Handsome..” Ta fadi ahankali gamida mika hannunta ta shafo gashin hannunshi ahankali ta yadda ba zaiji ba,
Fuskar sadiq ta kalla ta kalli fuskar lamido,
“Allah wasa wasa yaron nan yana kama da abbanshi”
Karar wayar lamido ce ta katse mata zancen zucin da takeyi, mika hannu tayi ta daukota daga kan bed side drewar dinta,
Ras gabanta ya fadi saboda ganin sunan wacce take kiransa,
“Xahar wacece kuma xahar?” Ta tambayi kanta,
A saitin kanshi ta tsaya nan ya bude idonshi daya ya kalleta,
“Menene? Idan ina bacci ba atsayawa akaina”
“Waya ake yi maka” ta fada tareda mika masa wayar,
Screen din wayar ya kalla ganin xahar ce me kiran yasashi yin dan guntun tsaki ya tura wayar karkashin pillow, nan wayar taci gaba da kara domin xahar bata fasa kiranshi ba, ita dai ikhlas tana tsaye tana kallonshi,
Zaune ya tashi ya jawo wayar ya kara ajikin kunnenshi,
“Hello xahar ya akayi ne? Bacci nake fa” yayi magana ahankali,
“Sorry abban sadiq” xahar ta fada daga daya bangaren hakan da ta fadane yasashi murmushi domin sai yaji kamar ikhlas ce tayi maganar saboda itace take kiranshi da wannan sunan,
“Babu damuwa meya faru?” Ya tambayeta yana murmushi,
“Kwana biyune ban ganka ba gashi idanuwana suna bukatar ganin beautiful face dinka” xahar ta bashi amsa cikin shagwaba,
“To zan shigo anjima” yafada yana mai satar kallon ikhlas wacce ke tsaye ta zubawa fuskarshi ido,
“To sai kazo ina nan ina jiranka” ya jiyo xahar tafada cikeda murna,
“Ok bye” yace da ita tareda kashe wayar,
Wani abune ya fara ratsa zuciyar ikhlas wanda bazata iya tantance ko menene ba amma tafi tunanin kishine,
“Kishi kuma? To ni me ya hadani da kishin abban sadiq..?” Ta tambayi kanta acikin zuciyarta,
“Saboda mijinki ne” wata zuciyar ta bata amsa,
“To amma akan me zanyi kishinsa bayan matanshi biyu nice ta uku kuma nasan sauran matan sonsu yake shiyasa ya aure su sabanin ni da ya aureni domin cikawa dan uwanshi burinshi” take taji wani bakin ciki da kunci ya rufeta ya lullube zuciyarta,
Hannunta taji lamido ya kama yana kokarin zaunar da ita akan jikinshi,
“Tunanin me kike yi?” Ya tambayeta yana mai kallon idanuwanta wadanda suke mutukar burgeshi domin kalarsu daban suke dana sauran mata,
Ajiye kwayar idonta tayi akasa tana son tambayarshi wacece wacce ta kirashi awaya kuma me zaije yi awurinta sannan menene matsayinta agareshi? Amma kuma sai taji ta kasa tambayar tashi domin nauyinshi take ji,
Karar wayarshi ne ta sake katse mata tunanin da take yi,
“Hello fadila” taji yafada yana shafar gashin girarta wanda yake kwance lif,
“My fadila ai ina son kiranki rigani kawai kikayi, ya hidimar biki?” Yafadi tamkar me yin rada,
Shiru ikhlas tayi tana jinshi amma aranta ji take kamar ta fashe da kuka amma wata zuciyar hanata take tana cewa “dama tunda kika auri mai mata har biyu ai kin san dole sai kinyi hakuri”
Ji tayi ya kwantar da kanta akan kirjinsa yana shafa fuskarta, shagala tayi ta ma manta da batun wayar da yake yi domin har ya kammala bata sani ba har sai da taji ya sunkuyo da fuskarshi saitin tata yana kallonta,
“Bacci kikayi?” Taji ya tambayeta ahankali,idanuwanta ta bude ta yi saurin kokarin tashi daga jikinsa, hannunta ya rike yana murmushi,
“Ina zaki je?”
“Nagama hada breakfast tun dazu fa”
Mikewa yayi yana rike da hannunta amma ita duk ta gama takura,
Tana baya yana gaba har sukaje falon ta tsugunna tafara zuba mishi abincin,
“Kar ki hada min tea bazan sha ba wannan ya isa” yace da ita yana kallonta,
“To” ta amsa mishi a takaice,
Daukar abincin tayi ta mika mishi ta koma nesa dashi ta zauna, tana kallonshi yafara ci har ya kammala ya mike,
“Bari naje gida nayi wanka”
“To, baffa yace yana nemanka”
“Ok bari naje”
Tana kallonshi ya wuce ya shiga dakinta ya dauko wayoyinshi ya fito ya wuce kallonshi tayi ta yi har ya fice daga falon,
Zama ta koma tayi aranta tana tunanin to Kodai lamido wani auren zai sake yi? Dakyar ta samu ta yakice wannan tunanin daga ranta.
Har yamma tayi shiru lamido bai dawo ba har akayi sallar magrib nan kuma hankalin ikhlas ya tattara ya koma kanshi domin shirun yayi yawa,
Wayarshi ta kira gabanta yanata faduwa,
“Hello” taji ya fada lokacin da ya dauki wayar,
“Abban sadiq mun jika shiru shikuma sadiq yanata nemanka..”
“Gani nan zuwa” yafada gamida tsinke wayar,
Tana zaune a falo tasha ado cikin pink din leshi dinkin fitet tana feeding din sadiq, ba karamin kyau tayi ba amma bata ga shigowarshi ba,
Rankwafawa yayi agabanta yana cewa,
“Saddiqu na abinci ake…” Tun kafin ya karasa ikhlas ta zabura ta janye sadiq ta saki rigarta,
“Me yake damunki ne?” Ya fada yana kallonta,
Shiru tayi tana kallonsa amma ta kasa magana, “ni narasa me kike boyewa bayan nafada miki cewar na dade da ganin abinda kiketa boye min”
Sunkuyar da kanta tayi, “karfa ki manta jiya…”
“Gashi” ta katseshi ta hanyar mika mishi sadiq,
Karbarshi yayi ya juya dashi zai fita fuskarshi dauke da murmushi domin lamarin ikhlas dariya yake sakashi ko bai shirya ba, mikewa ikhlas tayi tabi bayanshi tana rikeda mayafinta a hannu domin yin rakiya amma sai satar kallon lamido take domin yayi mutukar yi mata kyau saboda bakar riga ya saka da blue din wando abinka da farar fata nan yafito fes dashi,lumshe idonta tayi tana jin kamar taje ta rungumeshi “you look soo fine handsome” ta fadi hakan acikin ranta,amma afili sai tace dashi,
“Abban sadiq ina ka shigane baka zo kaci abinci ba alhalin kuma yanzu kai gwauro ne balle nace kaci awurin…”
Katseta yayi ta hanyar cewa,
“Nine gwauron? Me mata uku ai baza a kirashi da gwauro ba domin idan wasu basa nan to wata tana nan danma dai kin hanani angoncewa”
Murmushi tayi tana gyarawa sadiq kwanciyarshi akan cinyarta amma duk yasata taji kunya saboda maganar da ya fada dan haka tayi gaggawar kawar da zancen ta hanyar cewa,
“To meyasa baka zo kaci abincin ba?”
“Na koshine wallahi, tun abincin da kika bani da safe har yanzu jina nake a koshe may be da daddare ma ruwan lipton kawai zan sha”
Murmushi tayi tana kallon kyakkyawar fuskarshi wacce take kyalli tamkar mudubi.
Daukarsu yayi ya fita dasu cikin gari sune har wani hadadden store inda lamido ya fita ya siyo musu kayan makulashe ya hado da ice cream kwallo daya,
“Abban sadiq ya naga ice cream din guda daya? Kai bazaka sha bane?”
“Kece dai ba zaki shaba amma ni zan sha” yabata amsa tareda tashin motar ya fara driving,
“Saboda me kace haka?”
“Saboda bana son sanyi ya harbi sadiq saboda duk abinda kika ci shima ajiki zai samu”
“Tabb” ta fadi gamida budewa ice cream din tafara sha, packing yayi a gefen titi ya dauki sadiq ya mika shi kujerar baya ya kwantar ya dawo mazauninshi ya juya yana kallonta,
“Miko min abuna” ya ce da ita tareda mika mata hannunshi, ganin bata da niyyar bashi ya sashi matsawa jikinta ya matseta, kokawa suka fara yafara kokarin kwatar robar ice cream din amma ikhlas ta boye a bayanta, kujerar da take kai ya kwantar ya koma yaci gaba da kokarin kwacewa ice cream din,
A hannunta ta debo ta shafa masa a fuska tana dariya hakan ya sashi shima debowa ya fara shafe mata fuskarta dashi,
“Abban sadiq kabari wlh akwai sanyi..” Ta fada tana kare fuskarta tana dariya,
“Amma shine ni zaki Shafa min bayan kin san cewa akwai sanyin?”
Matsawa yayi jikinta sosai yasaka harshensa akan fuskarta yafara lashe mata ice cream din da ya shafa mata.RUWAN KASHE GOBARA 1

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.