RUWAN KASHE GOBARA! 62

0 262

_62_

RUWAN KASHE GOBARA 1

Murmushi tayi ta rike hannunshi tafara kokarin dakatar dashi amma bai barta ba har sai da ya gama lashe ice cream din fuskarta gaba daya,
“Ki goge min abinda kika Shafa min a fuska..” Yafada yana rikeda ita,
Kafada ta make alamun tak’i, idanuwanshi ya rufe ya fara yar kara kadan,
“Washh idona… Samomin ruwa na wanke fuskata..”
Ai ikhlas najin haka ta rude bata san lokacin da ta makalkaleshi ba takai bakinta kan fuskarshi ba ta soma lashe masa ice cream din dake fuskarshi,
Lasar fuskarshi take babu kakkautawa har sai da ta gama lashe ice cream din tsaf,
“Abban sadiq ya fita ko akwai saura?” Ta tambayeshi tana girgiza shi,
Bude idonshi yayi yana kallonta ta cikin hasken street light din data haskesu, tsura mata ido yayi sai kuma ta ga ya kwashe da dariya yana kallonta,
Ta ganeshi sarai cewar wayo yayi mata dama can babu wani abunda ya shiga cikin idonshi,
Juyawa tayi ta soma kokarin sauka daga jikinshi tana cikeda kunya,
“Menene abin kunya kuma bayan kin riga da kin gama lasar min fuska..” Yafada tareda rikota,
“Ga ice cream din kasha” ta mika masa guntun na cikin robar wanda ya rage,
“Sha ki bani” ya mayar mata dashi yana yi mata wani irin shu’umin murmushi,
Girgiza kai tayi ta sake mika mishi, murmushi ya dan saki ya kalli kwayar idanuwanta, hakika yau ya yarda babu abinda yafi rayuwa da masoyi dadi domin shi ya tabbatar da hakan saboda wani irin shauki yau yake ji atare dashi sanadiyyar yana tare da abar sonshi prettynshi, karba robar yayi yana mai cigaba da kallon fuskarta ita kuma duk kunya ta gama cikata,
“Nasha na rage miki?”
“A’a ka shanye”
Hannunshi yasa ya shafi fuskarshi wanda duk dankon ice cream ya gama baibayeta,
“Fuskata danko…”
Kafin ya rufe bakinshi tuni ikhlas ta sake fakar idonshi ta debo ta zuba masa a fuska, nan ta shiga shafe masa fuskarshi dashi,
Kokawa suka shiga yi yana rirrike hannunta amma bata daina shafa masa ba,
“Yau dai ice cream dinnan ahaka zamu shanyeshi ko?”
Yace da ita gamida saka hannunshi ya debo ya yaba mata, “Abban Sadig wallahi zanyi mura..”
“Za muyi dai tunda haka kika zaba”
“Allah dagaske nake”
“To zo in lashe miki, kawo fuskarki…”
Sai da ya lashe ice cream din tsaf sannan ya dago da kanta yana cewa,
“Saura ni…, kinji”
Cike da kunyarshi tasa harshenta ta soma lasar fuskarshi har ta gama idonta arufe,
Sakinta yayi ya tashi ya koma kujerar zamanshi yana murmushin farin ciki,
“Mu koma gida ko? Amma pls rakani mu fara zuwa wani wuri”
Batayi magana ba ta mika hannunta sit din baya ta dauko sadiq wanda keta faman bacci,
Ita kanta ikhlas din yau wani nishadi takeji bata taba sanin haka lamido yake ba sai yau da yafara nuna mata irin salon soyayyarshi,
Titin gidanshi ya dauka dasu ya juyo yana kallonta,
“Banji kince komai ba”
“Game da mefa?” Ta bukata batare data kalleshi ba,
“Bakiga inda na dosa bane? Bakya tsoron tanan nakaiki dakinki”,
Murmushi tayi ta dan saci kallonshi kadan,
“Ai nasan ba Zaka yimin haka ba”
Murmushi shi dinma yayi “waye ya fada miki? Tab ai ni banki ace na daukoki kenan ba daga nan sai gidana”
Daidai lokacin suka karasa kofar gidan nashi, awaje yayi packing ya bude motar zai fita,
“Ko zaki rakani?”
“A’a”
“Saboda me? Tsoro kikeyi? Shikenan bari naje na fito”
Kallo ta bishi dashi har ya shige cikin gidan, murmushi ta saki sam bata zaci haka lamido yake da iya soyayyaba sai tsakanin jiya zuwa yau da suka zauna awuri guda, ita da kallon murdadden namiji take yi masa marar sanin yanda soyayya take ashe abin ba haka bane, jinginar da kanta tayi ajikin kujerar motar tana murmushi,
Batare da taga tahowarsa ba kawai sai shigowarsa cikin motar taji, tashin motar yayi ya juya ya nufi gidan Baffa dasu.
Lokacin da suka isa gidan a kafada ta dauki sadiq ta nufi cikin gida shikuma lamido ya wuce masallaci,
Yana fitowa daga salla ya shiga gidan nan ya isketa itama tana sallar ta kwantar da sadiq a gabanta,
Daukar sadiq yayi zuwa kan gado ya dorashi akan ruwan cikinshi ya fara yi masa wasa. Tana idar da sallar ta mike tana ninke abin sallar,
“Zuba min ruwa zanyi wanka, fuskata danko take yi har yanzu” lamido yace da ita yana kallonta,
“Tom” ta bashi amsa ta shige cikin toilet ta hada mishi ruwan ta fito, sadiq ta dauka ta fita dashi falo tabar lamido yana shirin shiga wanka,
Abinda suka shigo dashi na makulashe su ta bude ta fara ci, tana nan zaune lamido ya fito daga shi sai t shirt dark brown da boxer iya cinyarshi,
Akusa da ita ya zauna ya fara cin abinda take ci,
“Sadiq kai ka koshi ko?”
Murmushi tayi “uhm”
“Dama uhm zakice tunda kina barinshi da yunwa”
Murmushi tayi ta mike ta nufi cikin daki, wanka ta shiga tayi wanda tun tana cikin toilet din taji kukan sadiq ya yawaita danma a hannun lamido yake, hanzartawa tayi ta gama ta fito daure da zani daurin kirji da towel karami wanda ta rufe jikinta dashi,
“Ungo shi” lamido ya fada yana dan harararta saboda tabar sadiq yana kuka,
Karbarshi tayi ta zauna tafara shayar dashi bayan ta sakashi acikin towel din ta lullubeshi, tari ya fara yi alamun ya kware ai nan lamido yace bai san zance ba ya matsa kusa da ita ya yaye towel din yana fadin,
“Wallahi ba zaki cutar min da yaro inaji ina gani ba”
Dolenta babu yanda ta iya haka taci gaba da feeding din sadiq lamido yana tsaye yana kallonsu har sai da ya tabbatar da cewar ya koshi sannan ya karbeshi yaje ya haye gado ya kwanta ya rungumeshi,
Gaban mirror taje ta dan gyara fuskarta tasha turare kala kala ta je ta dauko kayan baccinta sai da ta waiwaya ta tabbatar da cewa lamido baya ganinta sannan ta saka kayan wanda suka kasance riga da wando milk colour masu laushi,
Bayanshi taje ta kwanta tana kallon sumar kanshi,
“Abban sadiq idan ka tashi yin kitso na iya” tafada ahankali, sadiq ya kwantar ya juya gareta ya rungumeta,
“Gobe zanje nayi aski ai, yau da naje wurin Baffa yace ya kamata na rage sumar nan”
Murmushi tayi “ai tashen samartaka kake yi shiyasa”
Murmushi yayi ya sake shigewa cikin jikinta “tunda kin iya kitson to yimin naji”
Hannuwanta ta nutsa cikin sumar tashi ta soma shafawa ahankali can taji ya rike hannunta,
“Bari da zafi fa”
“Kai abban sadiq ashe da kai mace ne da anga me kukan kitso” tafada tana murmushi, juyawa yayi da ita ya zame hular kanta,
“Tunda kema kanki a tsefe yake bari inyi miki kitson kiji idan babu zafi”
Idanuwanta ta rufe ta fara sauraron kalar sakon da yake son aika mata dashi.
Sun dade basu runtsa ba har wurin karfe 2:30 nadare, karfe 6 ikhlas ta tashi tayi salla ta tashi lamido, tashi yayi yana hamma,
Toilet ya shiga sai da yayi wanka sannan ya fito da gajeren wando a jikinsa,
Kayansa ya saka yayi salla ya koma ya kwanta.
Ta bayanshi ta je ta kwanta take wani bacci yayi awon gaba da ita nan ta murgina ta rungume lamido acikin baccin batare da ta saniba, juyowa yayi ya sake rungumeta yana mai kallon kyakkyawar fuskarta, tunda ya kura mata ido bai iya daina kallonta ba har sai da ta farka,
Hamma tayi ta bude idonta nan suka hada ido da lamido yana yi mata wani kayataccen murmushi, kunya ce ta kamata saboda ganin yanda ta rungumeshi kamar tana tsoron kar wani ya kwace mata shi,
“Abban sadiq.., ina sadiq yake?” Ta tambayeshi tana zaro idanuwanta,
“Gashi can a bayana, me zaki yi mishi bayan kin zo kin rungume mijinki kin manta dashi, sai yanzu kika tuna dashi?”
Ya fad’i hakan yana kallon kwayar idonta,
Saukar da idonta k’asa tayi cikeda kunya nan tafara kokarin tashi lamido yayi saurin riketa,
“Ina zakije kuma?”
“Wanka zanyi” ta bashi amsa har lokacin idonta yana kasa,
“Wanne irin wanka?” Ya bukata yana lumshe mata idanuwanshi,
“Normal wanka” ta bashi amsa cikeda kunya domin ta gano inda tambayar tashi ta dosa,
“Ni kuwa kinga….” Hannunta takai kan bakinshi da sauri ta rufe masa baki,
“Please abban sadiq ya isa dan Allah..” Tace dashi bayan ta langabar da kanta cikeda kunya,
“Au kar na fada? Bakya son kiji damuwata? Shikenan tunda hakane” yace da ita cikin kalar tausayi,
“Nifa ba haka bane” ta fada a shagwabance,
“To yaya ne fada min…!” Ya fadi hakan yana matsa yan yatsunta,
“Please kabarni naje nayi wankan” ta sake fadi idonta yana kallon kasa,
“Nifa ba wani abu zance ba dama cewa zanyi ni kuwa tun ranar da na fara kwana a cikin dakin nan sai nayi wanka sannan nake yin salla..” Ya fada ahankali kamar me yin rada, kanta ta kawar daga barin da yake ta soma kokarin tashi ba tare da ta bashi amsa ba,
Sakinta yayi ya juya ya rungume sadiq.
Zani ta dauka ta shiga toilet tayi wanka sai da ta leko ta tabbatar da cewa lamido bacci yake sannan ta lallaba ta fito ta shirya agurguje cikin jan material mai laushi, kwalliya ta dan yiwa fuskarta ciki harda saka jan janbaki, turaruka masu dadi ta fesa ta fita zuwa kitchen,
Ruwan zafi kawai ta dafa ta soya kwai ta dauka ta kai falo daidai lokacin lamido ya fito da sadiq a hannunshi,
Bata kalleshi ba ta dauki breakfast din baffa ta tafi ta kai masa ta dawo, karbar sadiq tayi domin yi mishi wanka amma duk motsin da zatayi idon lamido na kanta saboda tayi asalin yi mishi kyau.

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.