RUWAN KASHE GOBARA! 65

0 221

_65_

RUWAN KASHE GOBARA 1

Gaba d’aya ikhlas jin maganganun da Lamido yake yi mata take kamar acikin mafarki,maganar da yaci gaba dayi ce ta katse mata tunaninta,
“Pretty wannan zoben dake hannunki zobe nane, nine nan na sanya miki shi saboda nasan zan sake haduwa dake har mu rayu tare a matsayin ma’aurata mata da miji, i love you pretty… I love you,… I love you..!”
Duk da cewar jikinta babu karfi amma hakan bai hanata zabura ta mike zaune ba, hankadeshi tayi wanda saura k’iris yakai k’asa,
Jikinshi zafi zau ya d’ago yana kallonta “pretty kar kiyi min haka, wallahi zan iya shiga mummunan hali muddin kika juya min baya..”
“Sai dai ka mutu dan indai nice to nagama zaman aure dakai…”
Lamido najin haka bai san lokacin da ya zabura ya mik’e ba,
“Idan mun rabu muyi yaya da yaronmu? Haba pretty kiyi nazar…”
Hannu ta d’aga ta katseshi, “wanne yaron? Wallahi ko cikine ajikina sai na b’arar dashi ballantana yaron da ya fito duniya…”
“Cikin nawa zaki b’arar pretty?” Ya tambayeta cikin tashin hankali,
“Kwarai kuwa dan bazan haihu dakai ba balle har wata rana azo ana yiwa d’ana gorin ubanshi mazinacine ba…”
Ras ras lamido yaji gabanshi ya harba tab lallai indai hakane akwai aiki ja agabanshi, kafin ya farga har ikhlas ta dira daga kan gadon ta nufi wurinda kayan sawarta suke nan ta bude drewar din tafara kwaso kayan tana watsa su kan gado, cikin sauri lamido ya bi bayanta ya fara kokarin rirriketa,
“Pretty dan Allah kiyi hakuri amma kar ki tafi ki barni, kiyi min duk wani hukunci da kika ga ya dace dani amma karki tafi ki barni…”
“Akan me zanci gaba da zama da mazinaci irinka wanda ya kasa hadiye kwalamarsa ya afkawa mahaukaciya, ahaka kake son in zauna dakai? Kana bin yaran mutane kana lalatawa ciki harda mahaukata, wallahi da nasan haka halinka yake da ban yarda an daura mana aure da kaiba, macuci azzalumi, marar tausayi marar tsoron Allah, mazinaci kawai..” Duk wadannan maganganun tana yinsu ne yayinda hawaye yake bin kumatunta, shima lamidon hakan take domin shima hawayen yake sonyi sai dai a wannan karon yayi juriyar hanasu zubowa fuskarshi sai dai acikin zuciyarsa suke kwarara, amma idanuwanshi sun hadu sun kad’a sunyi jajajur,
“Naji koma dame zaki kirani ki kirani dashi sai dai karki manta ita kaddara ba a tab’a iya guje mata,abinda ya faru tsakanina dake kaddarace rubutacciya..”
Toshe kunnuwanta tayi da hannuwanta guda biyu “kaddara? Kaddara fa kace? Kar ka sake yimin magana saboda yanzu bana son jin maganarka ka fice min daga cikin daki, ban son ganinka, i hate you…!”
Arazane ya nufeta yana zuwa tafara ja da baya “karka tabani, karka kuskura ka tabani da k’azamin jikinka, wallahi da ace nasan kai mazinacine da ban bari kazamin jikinka ya shafi nawaba..”
Duk da wad’annan mugayen kalaman da take jifanshi dashi bai hanashi dosarta ba, ja da baya take har ta isa gaban mirror,
“Wallahi indai baka rabu daniba sai na kashe ka ko na kashe kaina domin na tsaneka..”
Kwalbar turare ta dauko ta bugi bango da ita take kwalbar ta fashe turaren ciki ya tsiyaye,
“Da inci gaba da zama da kai gara na kashe kaina na mutu..”
“Ikhlass.. Dan Allah kar kiyi min haka”
Inda take ya karasa ya riketa yana kokarin kwace kwalbar, yana jin kwalbar ta yanke shi a hannu amma haka ya daure yaci gaba da kokarin kwacewa saboda ya lura ikhlas zata iya aikata abinda tace gashi da alamar bata cikin hankalinta yanzu,
Kokawa suke sosai, wata irin fusga tayi take ta yankeshi a goshinsa kafin wani lokaci har jini ya b’ata masa fuska, amma bai barta ba har sai da ya kwace kwalbar,
“Ka fita min daga cikin daki mugu kawai azzalumi macuci, mazinaci..”
Ba tare da ya sake bi ta kanta ba yasa kai ya fita, key din kofar falon ya zare ya rufeta ta ciki ya tafi da key din domin baya son ta tafi,ko fadanne gara ta zauna suyi tayi har ranar da zata hakura amma kalmar data fada cewar ta tsaneshi tafi komai razanashi domin baya son ta tsaneshi,
Bedroom dinshi ya shiga ya watsa kwalbar acikin dustbin ya shiga toilet ya wanke fuskarshi, ga hannunshi duk ya yanyanke,
Kan gado yaje ya kwanta take kuma maganganun da ikhlas ta fada masa suka fara dawowa cikin kwakwalwarshi wanda yake jinsu tamkar saukar aradu,
Wani zazzafan zazzabine ya sake rufeshi mai hadeda ciwon kai, nan yafara kukan zuci wanda yafi na fili ciwo amma ga hawaye nan suna faman sintiri akan kumatunsa.
A b’angaren ikhlash kuwa lokacin da lamido ya fita ya barta wani kuka mai ratsa zuciya ta fashe dashi ta fad’a kan gado ta kwanta taci gaba da kukan da takeyi amma har cikin ranta wani irin tsanar lamido taji yana shigarta,sannan ga wani zazzabi mai zafi da yake saukar mata ajikinta,
Zanin gadonta ta damke da hannuwanta tana kukan bakin ciki, take abubuwan da suka faru acikin rayuwarta suka fara dawo mata cikin kwanyarta tiryan tiryan, tun daga kan korar karen da abbanta yayi mata har zuwa kan auranta da lamido, haba sai yanzu ta gano tsantsar kamar da abdallah yake yi da lamido wanda abaya ta kasa fahimtar hakan sai yanzu,
“Bazan zauna dakai ba saboda na tsaneka, na tsaneka lamido, babu abinda zai Sa naci gaba da rayuwa da mutumin da bai dauki sab’on Allah a matsayin komai ba, Allah ne kadai yasan yawan matan da kayiwa fyade bazan zauna dakai ba bare abinda kayiwa yaran wasu nima ayiwa yarana.., Bazan taba yafe maka ba” tafada bayan ta sake fashewa da kuka,
Kamar wacce aka tsikara sai kuma ta mike zunbur ta dauki hijabinta ta nufi kofar fita,tana zuwa taji kofar a kulle k’yam ko ba afad’a mata ba tasan lamido ne ya rufeta aciki saboda kar ta tafi,
Bugun k’ofar ta fara yi da hannunta kamar zata b’alle ta gashi k’ofar k’ark’arfa ce ba irin wacce zata budu a dad’in rai bace, dukan k’ofar taci gaba dayi da hannunta wanda take jin zafin had’uwar kofar da hannunta yana shigarta tamkar hannunta zai cire dan rad’ad’i amma hakan baisa ta hak’ura ba sai ma k’ara k’aimi da tayi wurin cigaba da bugun,
Lamido yana kwance yana jinta amma ya kasa tashi domin zazzabine ajikinsa sosai ga wata hajijiya da yaji tana d’aukarshi, jin bugun k’ofar da ikhlas take yi yak’i k’arewa gashi yana tsoron kar taje taji ciwo a hannunta garin bugun k’ofar hakan yasashi tashi da k’yar ya d’auki key din bedroom din nata ya fita, yana tafe yana had’a hanya kamar wanda yasha abin maye,
Bud’e k’ofar yayi take ta yunk’uro zata fito nan yayi saurin tare bakin k’ofar ta yanda bazata iya wucewa ba,
Ciki ta koma bayan ta sake fashewa da wani sabon kukan, rufe k’ofar yayi ya bita cikin dakin, akan gadonta ya sameta a kwance tana gunjin kuka, ta bayanta ya k’arasa ya zauna ya kai hannunshi da niyyar kamo hannunta domin jikinshi ya bashi taji ciwo ajikin hannun saboda gashi nan har ya kumbure,
Cikeda masifa fuskarta dauke da bala’i ta tashi zaune, “karka kuskura ka tab’ani da k’azamin hannunka wanda kaje ka gama yawon bin mata dashi…” Tafad’i hakan idonta cikin nashi domin yanzu kunyar dake tsakaninsu tuni ta saka k’afa tayi fatali da ita,
Idonshi jajur a k’ank’ance yake kallonta gaba d’aya ma ya rasa abinda zai ce mata amma kuma zuciyarsa jinta yake yi kamar ana had’a mishi wuta aciki dan zafi,
“Ikhlas naji nayarda da duk abinda zaki kirani dashi,amma dan Allah kar ki nemi illata kanki idan kika yi haka to tamkar kina neman illata rayuwata ne..” Yace da ita yayinda hawaye ke sauka akan kumatunshi,
“Sai me dan na illata rayuwarka? Ai ayanda nake jin zuciyata ahalin yanzu zan iya kasheka domin a duniya idan akwai wanda nafi tsana to kaine..”
Kallon k’wayar idonta kawai yake yi yana hadiyar bakin cikin da take kunsa masa,bai sake magana ba amma duk da haka saida ya mik’e yaje inda take, zabura tayi yayi saurin saka k’afarshi tayi tutub’e ta fad’a jikinshi,
Wani ihu ta saka domin ita yanzu bata son jikinta yana shafar nashi, matseta yayi gam gam ajikinshi ya kamo hannuwanta yana dubawa domin shi ayanzu nema yake jin wani irin zazzafan sonta yana ratsashi domin daren jiya darene wanda bashida na biyunshi acikin rayuwarshi,
Ganin hannuwan nata yayi duka biyun sun kumbura sunyi ja, kallo yabi hannun nata dashi hawaye yana zuba daga idonshi domin yau ga abinda yake so amma kuma babu damar nishad’antuwa dashi saboda ba acikin kwanciyar hankali yake ba,
“Ka sakeni ka daina yunk’urin tab’ani na fad’a maka na tsaneka na tsaneka..”
Muryar ikhlas ta katse masa tunaninshi, cikin sauri ya saketa ya mik’e, yana kallonta ta fad’a kan gado taci gaba da rusar kuka Wanda jin kukan yake yi har cikin zuciyarshi amma kuma zuciyarshi ta fara bashi shawarar indai sakin ikhlas shine farin cikin rayuwarta da burinta to ya kamata ya saketa domin ta samu farin cikin saboda bashida burin da ya wuce na yaganta cikin farin ciki.

WhatsApp: 08161892123

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.