RUWAN KASHE GOBARA! 66

0 348

_66_

RUWAN KASHE GOBARA 1

Ba tare da ya jiyo ya kalleta ba ya juya zai fita, cikin azama ikhlas tayi kukan kura ta bi bayanshi tareda kamoshi ta baya,
“Babu inda zakaje har sai ka rubuta min takardar sakina ka bani saboda na fada maka bazan zauna dakai ba, i hate you…”
Ayanda yake tsaye ahaka ya ci gaba da tsayuwar ba tareda ya juyo ba amma acikin zuciyarshi tunani yake yi wannan wacce irin masifa ce take kokarin kunno kai a tsakaninshi da ikhlas? Bayan sai da yagama shan wahala akanta yanzu kuma lokaci yayi wanda yake ganin zai samu farin ciki da daddad’ar rayuwa sai kawai fitina ta b’ullo musu?
Dafe goshinshi yayi da hannunshi “ohhh God..!” Ya fad’i ahankali,
“Ka sakeni nace maka,wallahi idan baka sakeni ba zan iya illata ka na illata kaina..” Muryar ikhlas ta katse masa tunaninshi,
Girgiza shi tafara yi da karfinta, “ka sakeni nace..”
Juyawa yayi ya b’anb’are hannunta daga jikinshi ya juya yayi saurin ficewa daga cikin d’akin,
Da gudu ta taso amma kafin tazo tuni yayi nasarar rufe k’ofar dakin, bedroom dinshi ya koma yaje ya d’auko key din motarshi ya fice daga gidan,
Wani chemist yaje aka yi masa dressing din ciwon da yaji,ya siyo maganin zazzab’i dana ciwon kai sannan ya siyowa ikhlas maganin ciwon da taji garin bugun k’ofa,
Kallo daya zaka yi masa ka gane yayi bankwana da kwanciyar hankali, yana driving yana goge kwallar dake taruwa acikin idonshi da haka ya k’arasa gidan, lokacin da yaje sai da yayi ta maza sannan ya samu nasarar tsayar da hawayen idonshi, jiki babu k’wari ya fito daga cikin motar ya nufi cikin gidan, bedroom din ihsan ya lek’a babu kowa aciki gashi iya falonne kawai a bud’e duk yadda aka yi ta tafi makaranta, d’akin fadila ya zarce itama bata nan anan ya tabbatar da cewar itama makarantar ta tafi domin duk dakunansu a kulle suke,
D’akinshi yaje ya zauna ya dafe kansa yayi tagumi domin gaba d’aya duniyar tayi masa zafi ji yake yi kamar ya barta ya huta,
“Kodai na saki yarinyar nanne kamar yadda ta buk’ata??” Ya tambayi zuciyarshi,
“Amma kuwa da ka zama ragon namiji indai ka saketa akan wannan d’an k’aramin haukan da tayi,kenan ma ba sonta kake yi idan har ka iya sakinta, ka manta wahalar da kasha a dalilin rashinta? Ita fa dama soyayya ta k’unshi farin ciki da sab’anin haka amma indai aka jajurce to daga k’arshe za ayi achieving abunda ake so” wata zuciyar ta bashi amsa, mikewa yayi cike da k’warin gwiwa domin yanzu yaji ajikinsa zai iya jure kowacce irin bak’ar magana wacce ikhlas zata fad’a masa,sannan zai iya zama da ita ko acikin wanne irin haline.
D’akin nata ya bud’e ya shiga, tana zaune dab’as a k’asa ta d’ora kanta akan gado har lokacin kuka take yi ga hannuwanta sun yi suntum saboda tsabar kumburin da suka yi,
“Pretty…” Ya kira sunanta ahankali bayan ya tsugunna agabanta,
Ko kallonshi bata yiba taci gaba da kukan da takeyi,
“Kiyi hakuri ki daina kukan nan, bari na kawo miki abinci kici ga magani nan sai kisha” ya karashe maganar kamar wanda yake koyonta,
Nan dinma shiru tayi masa, tashi yayi ya fita zuwa kitchen anan kuma ya tsaya yayi sororo domin bai san ta inda zai faraba kasancewar babu abinda ya iya dafawa abu daya yasan zai iya shine soya kwai da dafa ruwan zafi domin wannan dama ko lokacin da yana school yana yi,
Gas ya kunna ya fasa kwai guda hud’u ya yanka albasa harda tumatur yasa maggi da curry ya soya, saukewa yayi ya tafasa ruwa kad’an ya zuba a cup yasa lipton da sauran kayan had’a tea ya kinkima ya nufi d’akin ikhlas,
Tana nan a inda ya barta amma yanzu ta daina kukan saboda wani irin zazzabi da ya saukar mata ga ciwon kai kamar kanta zai rabe gida biyu dan haka dolenta ta hakura tayi shiru, shi kanshi lamido shima zazzabinne ajikinshi kawai daurewa yake yi,
Agabanta ya ajiye kayan ya daga kai yana kallonta, “ga abinci na kawo miki, dan Allah ki daure kici..”
Tana jinshi bata kulashi ba, ledar maganin ya bude ya ciro maganin ciwon hannun da ya siyo mata wanda ya kasance na shafawa, hannunta ya kamo ahankali wanda yake zafi zau, maganin ya bude ya fara lakuta yana shafa mata, bin tafin hannunta yake da kallo saboda yanda kunshin hannun nata yayi kyau sosai gashi ya fito radau,
Ko motsi batayi ba har yayi ya gama, “ikhlas nasan nayi miki ba daidai ba amma kiyi min afuwa, wallahi bazan iya rabuwa dake ba domin kece rayuwata you are my life, i can’t survive without you,ina yi miki son da ni kaina ban san adadinshi ba”
Hannunshi ya mik’a mata yana nuna mata”kalli hannuna kiga yanda na tsagashi da reza na rubuta sunanki saboda tsananin son da nake yi miki, wallahi bazan iya sakinki ba pretty da ace zan iya to da nayi mutukar yin hakan zai haifar miki da farin ciki, amma karki manta da wasiyyar da dan uwana ya bar miki ta cewar karki auri wani idan bani ba, shin zaki yi watsi da wasiyyar da ya bar miki ne?”
Sanin bazata amsaba yasashi tashi ya fice, yana fita ta koma kan gado ta kwanta ta tukunkuna cikin bargo tana hawaye domin tunowa da tayi da wasiyyar da Abubakar sadiq ya bar mata, ita shaf da ta mance ma da wannan maganar sai yanzu, indai hakane kuwa to dole ta hakura taci gaba da zama da lamido domin cikawa Abubakar sadiq burinshi.
Shima Lamido yana fita daga dakin ikhlas dakinshi ya koma ya kwanta bayan ya lulluba acikin bargo sakamakon zazzabin da yaketa faman damunshi.
Daga shi har ita akwance suka wuni sai dai idan lokacin salla yayi su tashi suyi su koma su kwanta, har magrib tayi kowannensu yana kwance babu abinda yaci, sai misalin karfe shida sannan lamido ya tashi yayi wanka yayi salla yanzu kam yaji saukin zazzabin dake damunshi,
Tashi yayi ya fita afalo ya iske fadila da ihsan suna zaune suna hira yayinda fadila ke cin indomie da dafaffen kwai,
“Ango sai yanzu aka samu damar fitowa?” Ihsan tace dashi tana kallon goshinsa ganinshi nannad’e da bandeji,
“Ni ai nazata ko sai ka gama kwana ukun naka a dakin amarya sannan zaka fito” fadila ta fada tana murmushi,
A kusa da fadila ya zauna yana murmushi, “ni kaina da banyi niyyar fitowar ba har sai nagama kwana ukun” ya mayarwa da fadila amsa tareda karbar spoon din hannunta ya debi indomie din da take ci yafara ci,
“Darling ya naga goshinka da bandeji? Ciwo kaji?” Ihsan ta tambayeshi,
“Ehh wallahi” ya bata amsa,
“Garin yaya? Kai da kake tareda amarya ai bai kamata kaji ciwo ba” fadila tace dashi tana d’agawa ihsan gira,
“Naje gidan innane zan kai mata sadiq shine na buge”
Ya basu amsa yana cigaba da zukulkular abincin fadila,
“Ayya sorry” suka ce dashi atare,
“Kodai asake dafa maka wani indomie din?” Ihsan ta tambayeshi tana murmushi,
“No wannan ya isa” ya bata amsa, yana nan zaune sunata zolayarshi har ya cinye abincin ya mike,
“Bari naje na dauko sadiq daga gidan innah”
“Adawo lafiya” fadila ta amsa mishi amma ihsan ko sake kallonshi bata yiba har ya fice daga falon, yana fita suka fara gulmarshi,
“Jishi kamar wani marar lafiya dan Allah” inji ihsan,
“Bashida lafiya mana ai daga gani kin san akwai dalili, bakiga idonshi yayi jaba, ke nidai ina jin on top ba kalau ba”
“Koma meye shi ya jiyo badai yanata rawar kai dan yayi sabuwar amarya ba”
“Hmmm rabu dashi damuwarsu ce dashi da ita” fadila ta fadi tana turo dan kwalinta gaban goshi,
“Muna nan zai dawo garemu” inji ihsan,
Tashi fadila tayi “bari naje na cire kayannan na dawo”
“To sai kin dawo nima kitchen zan shiga na dafa lipton”,wucewa fadila tayi ita kuma ihsan ta shiga kitchen.
Lamido yana fita gidan innah yaje, samunta yayi goye da sadiq yanata bacci ita kuma tana zaune tana jijjigashi,
“Innah sai ke kadai? Gashi sadiq dinma naga bacci yake yi”
“Ni kadaice lamido, ai tun yamma yake baccin nan sai dai Allah yasa kar ya hanaku bacci anjima” innah tace dashi tana murmushi,
“Amin dan maman tashi bata da lafiya”
Sauko da sadiq innah tayi ta mikawa lamido tana cewa “Allah ya bata lafiya”
“Amin” ya amsa tareda tashi ya fita, a gaban motarshi ya kwantar da sadiq ya nufi gida dashi,
Gabanshi ne yafara faduwa lokacin da ya nufi dakin ikhlas domin bai san irin karbar da zata yiwa sadiq dashi ba, akan abin salla ya sameta zaune ta idar da salla tana addu’a,zama yayi agefen gadonta yana rungume da sadiq, nan idonshi yakai kan tea da soyayyen kwan da ya soya mata da safe amma ko tabashi bata yiba,
Kwantar da sadiq yayi yana kallonta,
“Ga sadiq nan ya dawo amma dan Allah na rokeki karki barshi da yunwa..”
Ko niyyar bashi amsa bata dashi ganin haka ya sanyashi tashi ya fita ya koma dakinshi ya kwanta.
Har dare ya tsala idonshi biyu ya kasa bacci ganin haka yasashi fita ya nufi dakin ikhlas, baiyi mamakin ganinta ido biyuba,
“Waye?” Ya jiyota tana fada daga cikin bedroom dinta,
“Nine” ya bata amsa gamida kwanciya akan doguwar kujerar cikin falon, bata sake magana ba ta gyara kwanciyarta ta kwanta tana ji sadiq ya fara kuka tayi biris dashi domin laifin abbanshi ya shafeshi shima,
Tashi lamido yayi ya shiga cikin dakin saboda jin kukan yake yi har cikin ranshi, samunta yayi ta juyawa sadiq din baya ta barshi yana kuka, saka hannu yayi ya daukeshi,
“Ikhlas kar ki hukunta wannan yaron da laifina domin shi bashida laifi ko kadan”
Kyaleshi tayi ya Karaci maganganunshi ya gama ya fita da sadiq din a hannunshi yana jijjigashi,mintuna kadan ya koma baccin dan haka ya sake mayar dashi kusa da ita ya kwantar.
Daga lamido har ikhlas yanda suka ga rana haka suka ga dare har asuba tayi, dakin ya leka ya sameta zaune da kayan bacci tana feeding din sadiq, juyawa yayi da baya ya fita domin baya son ta ganshi ta cire sadiq daga jikinta.

WhatsApp: 08161892123

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.