RUWAN KASHE GOBARA! 67

0 221

_67_

RUWAN KASHE GOBARA 1

Bedroom dinshi ya koma yayi alwala yayi salla ya zauna akan abin sallar ya fara lazimi amma kuma acan kasan ranshi damuwa ce acike fal,
Lallab’awa yayi ya tashi ya nufi kan gadonshi ya kwanta ya rungume pillow yana tunanin ikhlas acikin ranshi domin a kowanne lokaci jin sonta yake yana sake shiga cikin jinin jikinshi yana yawo, ko kad’an ya kasa jin haushinta ko kuma haushin abinda take yi masa, yana nan kwance rungume da pillow har gari ya waye rana ta fito,
Wanka yayi ya shirya ya saka bakar t shirt da farin trouser duk da cewar yana cikin damuwa hakan bai hana kyawunshi bayyana ba, turaren active man ya fesa ya fita ya tasamma dakin ikhlas.
Tana zaune tayi wanka ta shirya cikin jar atamfa tana shirya sadiq, ai sadiq na yin ido biyu da lamido ya hau tsalle yana son yaje wurinshi, k’arasa shiryashi tayi fuskarta babu walwala domin kamar wacce aka aikowa da sak’on mutuwa haka ta zama,
Sai da ta kammala shirya sadiq sannan ta ajiyeshi ta juyawa lamido baya, k’arasawa cikin d’akin yayi ya dauki sadiq yana mai bin jikin ikhlas da kallo domin ba karamin kyau tayiba gashi ta tufke gashinta a keyarta ya sauko har kan dokin wuyanta, wani kamshin dad’ine ya rink’a kaiwa hancinsa ziyara tun farkon shigowarshi cikin d’akin,
Ba tare da yayi magana ba ya juya zai fita domin yasan ko yayi mata magana ita ba yi mishi zatayi ba, fita yayi dauke da sadiq ya fice yabar gidan, gidan innah yaje yayi breakfast da wainar shinkafa da miyar agushi, bai bar sadiq awurin innah ba dashi ya fita ya nufi gidansu bash,
Yana zuwa yayi packing awaje daidai lokacin bash ya fito daga shi sai three quarter da wata karamar riga, gaban motar bash ya bud’e ya shiga yana kallon lamido,
“On top ya akayi ne? Kaga sabon ango”
Murmushin karfin hali Lamido yayi ya kalli bash “bash wallahi babu kanta, an yanka ta tashi..”
“Me kuma ya faru?” Bash ya tambayeshi domin dama ya ga alamun hakan atare dashi,
“Bash maman yaron nan ta dauke min wuta kwata kwata, zancen da nake yi maka ma yanzu ko magana bata yimin, fushi take dani sosai”
“Fushi? Me kayi mata? Ya daga tarewarta ko kwana uku ba ayiba har zaku fara samun sab’ani..”
“Bash akan abinda ya farune tsakanina da ita, tunda taji cewar nine mutumin da yayi mata fyade shikenan ta d’auki karan tsana ta d’ora min..”
“Kai da waye ya saka fada mata?” Bash ya tambayeshi cikin mamaki,
“Tsautsayi bash, bash tsautsayine ya sani na fada mata kuma wallahi ma ni ban san lokacin da na fada ba domin banida lafiya zazzabi nake yi..”
“Kaji ai, dan me zaka fada? Ai dole ta juya maka baya, laifinka ne”
Kallonshi lamido yayi idonshi jajur,
“Bash nidai yanzu so nake kazo muje ka bata hakuri dan Allah”
“To bari naje na sauyo wasu kayan nasa wanda zata fi ganina da mutumci”
Fita bash yayi ya koma cikin gida yaje ya sako riga da wando na shadda ya fito,
D’unguma suka yi suka nufi gidan lamido bash yana ta faman tsokanar Lamido “kai yanzu har ka sake yiwa yaron nan k’ani? Gaskiya kai jarababbe ne shiyasa dama su innah suka hanata tarewa domin sun san hali”
Murmushi lamido yayi “waye ya fad’a maka k’ani nayiwa sadiq? Kawai zazzabi ne babu wani abu”
“Kai dai kawai jarababbe ne malam”
“Ehh naji” lamido yabashi amsa da haka suka karasa gidan suka shiga.
Ikhlas na kwance akan doguwar kujera ta gama cin cake da meat pie ta kamo tashar zee world tana kallo amma kuma fuskarta gaba d’aya a d’aure take,
Lamido ne yayi sallama ya shiga, aciki ciki ta amsa sallamar tashi batare da ta dago ta kalleshi ba,
“Bash k’araso” Lamido ya ce da bash wanda yake waje a tsaye,
Shiga bash yayi hakan ya sata tashi zaune, babu sakin fuska babu komai ahaka suka gaisa da bash ya babbata hakuri ya tashi ya fita, ko kad’an bada hakurin da bash yayi baiyi tasiri agareta ba domin ayanda take gani zata dad’e bata huce da lamido ba dan haka hakurin da bash ya bata maimakon ya sassautawa zuciyarta sai ma sake tunzurata da yayi, komawa tayi tai kwanciyarta zuciyarta tana yi mata tuk’uk’i.
Har yamma lis tayi tana kwance a dakinta asalima tun zuwanta gidan bata taba fita tsakar gidan ba balle taga yanda yake, har dare yayi lamido bai dawo ba domin tun lokacin da suka fita da bash suke tare yana d’auke da sadiq,
Sai misalin karfe 8 sannan lamido ya koma gida, babu kowa a falo dan haka ya zarce dakin ikhlas tana kwance akan doguwar kujera tana kallo, sallama yayi amma da kyar ta amsa,
“Gashi karbeshi” yace da ita yana kallonta, ko kallonsa bata yiba balle ya saka ran zata karbi sadiq din, ya dan jima atsaye amma bata kulashi ba, d’ora mata sadiq din yayi ajikinta ya juya zai fita, bata kulaba shi kuma sadiq ya juya yana kallon lamido ji kake timm!! Ya fad’o kasa take ya callara k’ara yahau kuka, da sauri lamido ya dawo ya daukeshi, kallonta yayi azuciye nan da nan idonshi yayi ja, bai yi mata maganaba ya juya ya fita ya nufi dakinshi da sadiq din,
Kukan da yaron yake tayine yasa hankalin lamido tashi nan ya soma duba jikin yaron ko ciwo yaji, hannunshi na dama yaga ya dan karkace nan ya tab’a hannun yana tab’awa yaron ya k’ara tsananta kukanshi, cikin hanzari Lamido ya tashi ya fita da sadiq din a hannunshi ya nufi motarshi ya shiga, a sukwane ya figi motar zuwa gidansu bash fata daya yake yi Allah yasa yaron ba karyewa yayiba idan kuwa har karyewa yayi to lallai lokaci yayi wanda zai nunawa ikhlas halinshi.
Daukar bash yayi suka tafi gidan masu gyaran targad’e da karaya, suna zuwa aka duba hannun sadiq din anan aka gane cewar targad’e yayi nan aka gyara masa Lamido ya daukosu yaje ya ajiye bash ya wuce gida,
Dakinshi yaje ya kwantar da sadiq ya nufi dakin ikhlas ko ta kanta bai biba ya dauko friso cream din sadiq da madararshi ya fito,
Dakinshi ya koma ya had’a masa friso cream ya daukeshi ya fara bashi duk ransa abace, gashi saboda rashin sabo duk ya b’ab’b’ata jikinshi da jikin sadiq din da friso cream din, haka dai ya samu ya gama bashi ya daukeshi zuwa toilet yayi masa wanka ya fito ya kwantar dashi shima ya shiga yayi ya fito.
Komawa dakin ikhlas yayi yadauko kayan sadiq da pampers ya koma dakinshi rasa ta yadda ake saka pampers din yayi dan haka ya daukeshi ya nufi dakin fadila dashi, tana kwance tana waya da kawarta,
“My fadila dan Allah sakawa yaron nan pampers”
Tashi fadila tayi ta karbi sadiq ta saka masa pampers din ta koma taci gaba da wayarta, dakinshi ya koma ya saka masa kaya ya kwantar dashi asaman jikinshi, mintuna kadan yaji yaron yayi bacci, tausayin kansa da na yaron ya fara ji, nan kuma abinda ikhlas tayi ya dawo cikin kwakwalwarsa hakika abinda kake so shi yake wahalar da kai domin shidai hakan ta faru agareshi,tabbas yanzu lokaci yayi wanda ikhlas zata ga nashi salon fushin saboda akan sadiq zai iya k’aurace mata shi indai tashine zai iya jure duk wani abu da zata yi masa amma bazai iya jure ganin tana nunawa sadiq halin ko in kula ba.
Yana nan kwance sai sak’e sak’e yake yi yaji wayarshi ta fara tsuwwa kamar bazai d’auka ba saboda damuwar da yake ciki amma sai ya daure ya mik’a hannu ya ciro wayar, sunan Xahar yagani dama kuma sai da jikinsa ya bashi cewar itace, cikin rashin k’warin jiki ya d’aga wayar tata,
“Xahar…” Ya fad’i ahankali,
“Ranka ya dad’e barka da wannan lokaci ina fata ban tasheka a bacci ba domin na sanka da saurin bacci sai kace sadiq” Xahar ta fadi cikin yanga,
Murmushi yayi yace “meyasa kika san da wuri nake yin bacci?”
“Saboda ina sonka ina k’aunarka hakan yasa nasan duk wani motsinka”
Murmushi ya sake yi, “to nagode amma yanzun dai idona biyu banyi baccin ba”
“Ayya shine kuma yau baka zo ka ganni ba?”
“Ki bari gobe zan zo kinji?”
“Da yaushe?”
“Expect me in any time xahar..” Ya bata amsa yana kissing din sadiq wanda ke kwance ajikinshi,
“Tom ina jiranka, sai da safe have a nice sweet dream..”
“You too”
Ya katse wayar yana jin farin ciki yana shigarshi, duk bacin ran da yake ranshi yanzu ya samu saukin shi, alokacin ya dan fara jin xahar acikin ranshi domin tana tsananin sonshi kuma tana nuna mishi hakan,
“I hate you…” Kalmar da ikhlas ta fada mishi ce ta dawo cikin kunnensa, sake rungume sadiq yayi acikin zuciyarshi yana tunanin da mutum ya manne a wurinda ba a sonshi ai gara ya rungumi masoyinshi koda kuwa zai rinka zaginshi kullum domin masoyi yafi makiyi kuma wanda yace yana sonka ai yafi wanda yace ya tsaneka wannan dalilinne ya sanyashi d’aura aniyar rungumar matanshi ihsan da fadila masu sonshi da nuna masa soyayya akoda yaushe, kuma zai koyawa kanshi sonsu da kaunarsu, haka itama xahar zai dage wurin tursasa zuciyarshi har ta sota.
Baccin dan takaitaccen lokaci yayi yaji an fara kiraye kirayen salla a masallaci, bai iya tashi ba har sai da 6 tayi a lokacin ya tashi yayi salla ya sake kwanciya, sai 8 sannan ya samu damar tashi, sadiq ya kalla wanda ke kwance kusa dashi yanata bacci wani tausayin yaron yaji yana ratsashi, mikewa yayi ya fita zuwa dakin ihsan, tana kwance akan gadonta ta rungume pillow amma ba barci take yiba,
Pillow din ya zare ya shiga jikinta ya rungumeta, “my ihsan good morning”
Bude idonta tayi ta kalleshi ta sakar masa murmushi,
“Morning Darling, how was your night?”
“Normal, yau ba zakije school bane?”
“Zanje sai 9 zanyi lecture..”
“Ok, Allah ya kaimu” tashi yayi zai fita ihsan ta riko hannunshi, “i soo much missed you darling” tafadi idonta rau rau kamar zatayi kuka,
“Sorry my ihsan zan dawo gareki soon”
Sakin hannunshi tayi ta koma ta kwanta idonta cike da kwalla hakan yasa lamido komawa kusa da ita ya zauna ya kamo hannunta ya rik’e ya fara rarrashinta,
“Haba my ihsan karki zama raguwa mana, uhm..!, daina kuka my ihsan daga yau fa shikenan gobe zan dawo wurinki..”
Hannunshi ta rike wanda ya fara shafar cikinta dashi, “ka bari..!” Ta fadi cikin shagwaba,
“Dama tab’awa nayi naji ko inada ajiya aciki..”
“Babu, baka da wata ajiya anan”
Tashi yayi yana murmushi “shikenan tunda haka kikace Allah ya kaimu gobe”
Murmushin itama tayi mishi batace komai ba har ya fice daga cikin dakin, bedroom din fadila ya shiga anan ya jiyo motsinta a toilet tana wanka,
Cikin bathroom din ya bita “hello my fadila, inzo in tayaki wankan?”
“Um um..!” Fadila tace dashi tana daga ciki,
Sunkuyawa yayi ya nannade kafar wandonshi ya bita cikin bathroom din,
“Allah sai na tayaki, shine harda saurin cewa um um ko?”
Shower ya sakar mata a kanta ya fara tayata wankan, sai da yaga ta kammala sannan suka fito tare duk kayanshi sun jijjik’e,
“Kinga yanda kika jikani ko?” Yace da ita yana kallonta,
“Sorry dear ai laifinka ne” ta bashi amsa tana balle mishi botiran gaban rigarshi,
“Kaje ka sauya kaya kar kayi mura kaji..” Fadila ta fada cikin kulawa,
“To my fadila, see you later..” Ya fada tareda nufar k’ofar fita,
“Bye bye dear” fadila ta fadi tana daga mishi hannu,
Bedroom dinshi ya tasamma yana cikeda farin ciki, “haba shiyasa mata biyu koma fiyeda haka suke da dad’i domin idan wannan ta b’ata maka to wannan zata faranta maka” ya fadi hakan acikin zuciyarshi,
Har lokacin sadiq bai tashiba dan haka ya shiga wanka ya fito, shiryawa yayi cikin milk colour din shadda dinkin tazarce ya saka hula designer itama milk colour ya feshe jikinshi da turare ya dauki sadiq ya fita dashi,
Bedroom din ikhlas ya shiga har lokacin tana kwance akan gado, fuska ya b’ata ya ajiye mata sadiq akusa da ita,
“Gashi nan nasake dawo miki dashi, idan kin gadama yauma ki barshi ya fad’o yaji ciwo, duk abinda kika gadama kiyi masa, jiya kin barshi ya fado yayi targade to yau sai ki barshi ya fado ya karye ko ya mutu, na tabbata duk abinda ya sameshi sai kin fini jin b’acin rai kuma sai abun yafi damunki fiye dani saboda ke kika haifeshi ba ni ba”
Yana gama fadin haka ya juya yayi ficewarshi ya barta da kamshin turaren da ya saka yana ziyartar hancinta.

WhatsApp: 08161892123

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.