RUWAN KASHE GOBARA! 7

0 136

_7_

Bud’e mata kofar motar yayi ta shiga ta zauna, ita dai binsa take kawai da kallo hakama dukkan wuraren binsu take da kallo ba tare da tace uffan ba,

Motar yayiwa key suka fita daga harabar asibitin, cikin gari suka hara yana tuki sannu ahankali cikin nutsuwa da kwarewa har suka isa wata unguwa mai karancin gine gine,

Agaban wani dan madaidaicin gida ya yayi packing yafita ya bude gate ya shigar dasu cikin gidan, fitowa tayi daga cikin motar kamar yadda shima ya fito, bin bayanshi tayi suka tasamma cikin gidan Wanda daga gani babu tambaya gidan mace daya ne,

Matar gidan tana hakince acikin falo suka sameta tadora daya akan daya, ganinsu ya sanyata mikewa tsaye tana kare musu kallo,

“Barrister wacece wannan?” Ta tambayeshi tana huci,

“Ki kwantar da hankalinki ni’ima zaki san ko wacece nan bada jimawa ba amma yanzu abinda nake so dake kinga ayanayin da take to ina so ki kaita tayi wanka ta shiga ruwan zafi sosai kibata kaya ta shirya ta saka kafin tazo taci abinci”

Kamar zata sake magana sai kuma ta fasa ta juya tayi gaba,

“Bi bayanta” yace mata yana nuna mata hanya,

Binta tayi sumi sumi duk kanta adaddaure, amma daga gani tasan za asamu matsala,

Wani daki taga matar ta shiga dan haka itama tabita ciki,

“Ga towel, ki shiga bathroom akwai dukkan abun bukata aciki sannan idan akwai wani abu wanda kike bukata sai kiyi min magana”

Karbar towel din tayi ta shiga bathroom din batare da tayi magana ba, fuuuu! Ni’ima  tayi falo inda elmustapha yake zaune tana zuwa ta tsaya agabanshi cikin masifa tafara magana,

“Wai wacce yarinyace waccen ka kawo min ita gidannan sannan tsabar rainin hankali har kana sanar dani cewar wai ta shiga cikin ruwan zafi sosai, meye alakarka da ita?”

“Haba ni’ima ki kara hakuri mana ai zan sanar dake komai”

“Kaga malam babu wani hakuri kawai ka sanar dani inda ka samota”

“Ni’ima wallahi ban santa ba mahaukaciya ce kuma muna kyautata tsammanin ta samu lafiya yanzu shiyasa nayi niyyar taimakon ta”

“Yanzu naji batu” tafada tana murmushi,

“Bari naje na fiddo mata da kayan da zata saka,juyawa tayi tafita daga falon tabar elmustapha tsaye yana kallonta yana murmushi saboda sanin zafin kishi irin na ni’ima.

  Tsayawa tayi agaban mudubin dake manne a bangon bathroom din tana kallon jikinta da fuskarta, hawaye ne suka fara bin fuskarta, dakyar ta iya samu ta tsaida hawayen ta tari ruwan zafi ta zauna aciki,gashin kanta mai mutukar tsawo da yawa tafara wankewa wanda sai da yaci ruwa bokiti 3 kafin dattin dake jiki ya fita,

Wanka tayi ta sake karawa sannan ta dauraye jikinta tafito bayan ta yi alwala,

Jinta take kamar sabuwar halitta gashi iska sai shigarta take yi tako ina, acikin dakin ta iske ni’ima tana tsaye tana zabo mata sutturar da zata sanya ajikinta,

“Har kin fito?” Ni’ima ta tambayeta cikeda fara’a, kai kawai ta daga mata batayi magana ba,

“Kiyi hakuri kinji,ki sanar min da sunanki saboda ban san da wanne suna zan kiraki ba” ni’ima tasake yi mata wata maganar tana kokarin rufe akwati,

“Sunana IKHLAS”

Yanda tayi maganar asanyaye ahankali cikin sanyin murya ya sanya ni’ima jin tausayinta,

“Allah sarki ikhlas, to ki shirya ga kaya nan ki saka sai kifito muci abinci kinji”

“Nagode” ikhlas ta bata amsa tareda dosar wurin da ta ajiye mata kayan,juyawa ni’ima tayi tafita daga cikin dakin tabar ikhlas domin ta shirya.

WhatsApp: 08161892123

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.