RUWAN KASHE GOBARA!

0 179

*RUWAN KASHE GOBARA…!*?

(Labari mai tab’a zuciya)

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN KAI..!
*1*
~~~” _*LAMIDO*_ yanzu wai shikenan idan katafi mun rabu kenan ba zamu sake ganinka ba? Kai gaskiya wallahi zamu yi missing dinka bama ni kadai ba harda sauran students domin kowa yana amfanuwa dakai”
Wannan shine furucin da wani matashin saurayi yayi daidai lokacin da suke zaune a farfajiyar hotel din _Zango hotel_ acikin garin yola babban birnin jihar yola ta arewacin Nigeria,
Wanda aka kira da suna Lamido yana sanye cikin bakar t shirt mai gajeren hannu tareda blue din jeans, hannunshi daure da agogon azurfa na _Rolex_ ,farine tatas dogo marar kiba, yana da manyan idanuwa masu shape din kwai, gashi da dogon hanci kamar biro, lips dinshi jajaye ne masu dauke da dan madaidaicin bakinshi, ya dan aje saje a fuskar tashi, gashin kansa kuwa kallo daya zaka yi masa ka gane cikakken bufulatani ne gaba da baya domin sumarshi akanannade take yalo yalo tamkar yana yi mata shanfo,
Zamanshi ya gyara akan motar da yake wacce ta kasance red colour kirar BMW,
Fuska ya dan ya mutsa take dimples dinshi suka bayyana wadanda kusan ko magana yake yi sai sun lotsa,
“Bash ka bari kawai, ni kaina bana son tafiyar nan amma baffa ya dage sai nabar kasar nan saboda wa indai ina tare daku bazan taba shiryuwa ba”
Yafada cikin daddadar muryarshi mai hadeda maganarshi irin ta fulani,
“To kai ya kagani on top?” Bash yace dashi yana kallonsa,
“Bash kenan kana ganin zan iya daina halayyata? Kawai dai aci gaba da addu’a may be zan iya shiryuwar nan gaba”
Yafada yana wani basaraken murmushi,
“Kai dan duniyane Lamido harma wani aci gaba da addu’a?”
“Atoh kai ya ka gani” Lamido yafada yana duba agogon hannunshi,”karfe 10:30 agogon ya nuna dan haka yayi tsalle ya diro daga kan motarshi wacce ajiki aka rubuta *ON TOP*
“Bash muje gida kasan yau baffa zai dawo kuma kasan halinshi da zarar ya dawo ya tarar bana nan fada zai hau yi”
“Ok muje”
Motar suka shiga bash yana gefenshi shikuma yana driving, aljihunshi ya karkace ya ciro kodin yafara sha,
Suna tafe suna shan disco har suka yi tafiya mai dan nisa, gefen titi Lamido yasamu yayi packing ya jiyo yana kallon bash, hannunshi yakai ya dafa mararshi ya rike cikinshi,
“Bash…! Marata tafara ciwo gashi mun baro club a baya” Lamido yafada yana yayyamutsa fuska,
“Kawai kai dai jarabarka ta motsa kawai, fito”
Fita bash yayi ya zagaya bangaren da driver yake zama yana mita,
“Ace mutum kullum bashida wani abu sai jarabar mata?”
Fitowa lamido yayi yana rike da mararshi har lokacin,
“Zanyi maka rashin mutunci, yau kwana na 3 rabona dasu ai nayi kokari”
Zagayawa yayi ya koma kujerar kusa data driver ya zauna yana runtse idonshi domin shi kadai yasan abinda yake ji,
“Yanzu ina muka dosa” bash ya tambayeshi yana tsaki,
“Muje kawai, idan mun shiga cikin gari 11 ba tayiba sai ka kaini guest house dinnan idan kuma 11 yayi sai asan abin yi”
Wuta bash ya kara suka tasamma cikin gari, daf da zasu shiga garin abakin titi kusa da wasu shaguna Lamido ya bude idonshi wadanda suka yi jajur suka sauya launi,
Wata mahaukaciya ya hango takure acikin runfar wani shago ta hada kanta da gwiwa tana sanye cikin wani Pakistan ja riga da wando wadanda suka yi dukun dukun saboda tsananin daudar dake jiki, kanta babu dankwali sai uban tulin gashi wanda yake har gadon bayanta duk da cewar a cukurkude yake gashi duk ya dundunkule harda kasa da yayi ajiki amma hakan bai hanashi sauka akan kafadunta ba,kafarta babu takalmi da gani ta dade tana dauke da wannan lalurar ta tabin hankali,
Cikin wata irin murya lamido yace, “bash wait, kaga wata yarinya can tsaya naje wurinta”
Burki bash yaja ya waiwaya ya kalli inda mahaukaciyar take ya jiyo yana kallon Lamido,
“Lamido me zakayi? Badai waccar mahaukaciyar zaka nema ba?”
Kallonshi Lamido yayi da rinannun idanuwanshi “bash ba kasan yanda nake ji bane, wallahi wurinta zanje tun kafin na mutu..!”
“Lamido mahaukaciyar? Ka kalli fa a halin da take ciki hali irin na kazanta na rashin tsafta, wanda ba lallai ne ma ka iya samun nutsuwar da kake so ba”
“Waya fada maka? *AI RUWAN KASHE GOBARA BA SAI MAI KYAU BA* wallahi zuwa zanyi, bari ma ka gani”
Lamido yafada yana kokarin bude kofar motar, kafin bash ya sake magana tuni har ya fita ya tunkari wurin da mahaukaciyar ke zaune atakure kanta cikin gwiwoyinta.

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.