Sababbin Albums din Wakoki Masu Fitowa A Wannan Shekarar 2019

0 2,276

Assalamu alaikum nasan masoya wakokin hausa suna nan sun shirya sun dakon sababbin kundin wakokin hausa masu fitowa a wannan sabuwar shekara da muka shigo.

Insha Allahu wayannan kudaddakin album din suna nan isowa gareku nan ba da jimawa ba.

Nasan mafi yawancinku kunfi jira kudin album din nan na babban mawaki wato Nura M Inuwa wanda kunsan duk shekara yake sakinsa.

Nura M Inuwa yana tafe da Kudin wakoki Guda biyu.

1. Mai Zamani

Munsan dai Allah ne mai zamani, to kawai wannan wani kundine da mawakin yasa masa suna mai zamani domin faranta ran masoyansa.

2. Ango

Hmmm to kudaga jin sunan wannan kundi ai kunsan wakokin ba na gauraye bane, to kuna ina angwaye kuzo ku rakashe cikin wannan wakokin.

2- Hamisu breaker

Hamisu breaker shima mawakin yana nan da kundin wakokinsa guda biyu zuwa daya.

Nasan kunsan kudin waka guda daya mai suna Haseena to shima insha Allahu wannan kudin wakar yana nan tafe a cikin wannan shekarar

3- Hairat Abdullahi 

Mawakiya hairat wace zan iya cewa kusan itace mace wace a harkar amshin waka kuma mawakiya mace tauraruwarta zata fara yawo a duniya Insha Allahu.

kusan yanzu itace mai yiwa duk wani mawaki amshi musammani Shareef Family Studio.

Nasan wasu zasuyi mamaki ganin tasa wa album dinta da sauran kallo kuma bacin a baya wani mawaki shima yayi, to wannan ba farau bane, idan baku manta ba Umar m shareef yayi Wasika, Sannan Nura ma haka, Husaini danko yayi Manyan Mata, Nura Ma Haka,

4- Sammani AA 

Mawaki sammani aa a shekarar da ta wuce ya kawo muku wani album dinsa mai suna Yarinya Ina Kika Dosa to wannan shekarar insha Allahu yana tafe da wani.

kudin wakokin nasa mai suna Afnan iya nan tafe cikin wannan sabuwar shekarar insha Allahu

5- Anas A Ibrahim

Anas a ibrahim nasan wasunku sun sanshi wasu ko suna dai ji ana fada, shima yazo da sabon kudin wakokinsa mai suna..

Sabon mawakin ya zowa da matasa tsaraba mai gwabi musamman nishadantar dasu da wakokin soyayya.

Shima insha Allahu yana tafe cikin wannan shekarar

6- Sani B Haruna 

Mawaki Sani b Haruna a baya mai suna Dakwan So wasuku nasan sun san album din wasu basu sani ba to sai kuje ku nemi naku.

Album din yar fulani daga bakin Sani B Haruna  kawai ku kasance damu a cikin wannan shekarar domin nishadantar daku da zafafan wakoki.

7- Halifa SK 

Mawaki halifa sk yace shima ba za abarshi a baya ba wajan nishadantar daku da wakoki masu zafi, shin ko kunsan waye Halifa SK? shine mai fassara a kamfanin Sultan Film factory.

Bakon yanayi wani album ne da zai gamsar daku da zakakan wakoki na musamman a cikinsa

8- Buhari Surajo Dorayi 

Buhari Surajo wanda kukafi sani da BSD shima yana nan tafe da sabon kundin wakokinsa mai suna.

Cikar so album wani kundin wakoki ne na musamman ga masoya wakokin hausa nanaye.

Dama sauran wasu kundaddakin wakoki masu zafi suna nan zuwa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.