Sababbin Fina-Finan Masana’antar KannyWood Da Zasu Fito A Shekarar Nan 2019

0 382

Mun leka bangaren fina-finan Hausa na Kannywood inda mu ka kawo muku jerin fina-finan Hausa da za a saki a wannan shekarar da aka shiga ta 2019. Jaridar mu ta zakulo wasu kadan daga cikin wadannan fina-finai.
Daga cikin manyan fim din da za a fitar a shekarar nan akwai:


1. SAREENA
Ali Nuhu da kuma Abubakar Bashir Mai Shadda ne su ka shirya wannan fim mai suna SAREENA. Taurarin wannan fim din sun hada da Umar M. Shareef, Abba El Mustapha da Ali Nuhu da kuma  Maryam Yahaya.


2. HAFEEZ
Daga cikin fim din da ake tunani za su yi tashe a bana akwai shirin Hafeez wanda shi ma Abubakar Mai Shadda ne yake shirya sa. Ali Nuhu ne babban Daraktan wannan fim din mai dauke da Taurarin da ke cikin Sareena da wasun su.


3. SADAUKI
Wani fim kuma da aka kagu a fara kallo shi ne SADAUKI wanda Hassan Giggs ya shirya kuma yake bada umarni. Taurarin fim din sun hada da Adam A Zango, Fati Washa, Fateema, Alhassan Kwalle da wasu manyan Taurarin yan wasan Hausa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.