Salah ne gwarzon kwallon kafar Afirka na 2018

0 100

Dan wasan Liverpool, Mohamed Salah ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na 2018.

Dan wasan tawagar Masar ya yi nasara ne a kan Sadio Mane na Liverpool dan wasan tawagar Senegal da Pierre-Emerick Aubameyang na Gabon mai wasa a Arsenal.

An gudanar da bikin karrama ‘yan wasan Afirka da suka yi fice ne a 2018 a fagen tamaula a Senegal.

Salah shi ne ya lashe kyautar 2017 da aka yi a Ghana.

Leave A Reply

Your email address will not be published.