Salon Kamfen: Mai Dakin Ganduje Ta Yiwa Matan Kano Wani Babban Albishir

0 240

Uwargidan gwamnan Jihar Kano, Hafsat Ganduje tayi yiwa matan jihar alkawarin cewa za ta tabbatar anyi musu karin nadin mukamai idan mijinta ya yi nasarar lashe zaben shekarar 2019.

Mrs Ganduje tayi wannan alkawarin ne yayin da ta ke jawabi a wurin wani shirin tallafi ga mata 1,500 da akayi a karamar hukumar Dawakin Tofa na jihar a ranar Alhamis.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito cewa dan majalisar wakilai mai wakiltar Tofa/Dawakin Tofa/Rimin Gado, Tijjani Abdulkadir-Jobe ya tallafawa mata 1,500 da N10,000 kowanensu.
Mai dakin Ganduje ta yiwa matan Kano wani albishir
Ta ce, “Idan Gwamna Abudllahi Ganduje ya lashe zabe, zamu tabbatar cewa an kara bawa mata mukamai a cikin gwamnati.”

Leave A Reply

Your email address will not be published.