Sanarwa Daga Nura M Inuwa Zuwa Ga Wa `Yanda Aka Danfara

0 307

SANARWA!!SANARWA!!!

A madadin nura_m_inuwa da daukacin ma’aikatan abnur_entertainment muna bawa mutanen da aka damfara da wadannan nombobin waya hakuri (07063114829,07037639211,07035141458).

Dan munsan mai damfarar ya damfaresune da zimmar cewa nura_m_inuwa ne shi zaiyi musu waqa ko kuma su bashi ko suyi mishi wani abu shima zai biya musu wata buqata.

Wadancan nombobi bana nura_m_inuwa bane kawai na wani dan damfarane wanda yake batawa nura_m_inuwa suna a idon duniya baki daya.

Yanzu haka Allah ya bamu nasanar cafkeshi mun mikashi ga hukuma.

Ga wadanda aka damfara kuma suke buqatar hakkinsu zasu iya garzayowa police station na tashar kofar ruwa a nan cikin garin Kano dan yin gamsasshen bayani a mayar musu da abun da aka karba a hannunsu.

Ga masu buqatar business da nura_m_inuwa kuma zasu iya garzayowa kai tsaye abnur_entertainment dake kallon tsohuwar BUK no 4 gidan Mariya sanusi dantata, ko kuma su kiramu a wadannan nombobi 08036206793 ko 07033617888.

Sanarwa daga annur_h_abnur manager na nura_m_inuwa .

Nagode.

Leave A Reply

Your email address will not be published.