Sarki Sanusi Na II zai nada mawakin Kannywood “sarkin mawakan sarkin Kano”

0 339

Fadar sarkin Kano ta sanar da cewar za ta nada mawakin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Naziru Ahmad, a matsayin sarkin mawakan sarkin Kano.

Hakan na kunshe ne cikin wata takardar sanarwa da Munir Sanusi, shugaban ma’aikatan sarkin Kano, ya aikewa da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a yau, Lahadi. Sanarwar ta ce fadar za ta yiwa mawakin sarautar ne bisa la’akari da yabon wakokin yabo da ya ke yiwa sarki Sanusi II tun yana Dan Majen Kano. Naziru ya rera wakoki ga sarki Sanusi II da su ka yi fice a kasar Hausa. A daya daga cikin wakokin da ya rera, Naziru ya ambaci cewar Sanusi zai zama sarkin Kano tun lokacin da ya ke rike da mukamin gwamnan babban bankin kasa (CBN).

Sanarwar ta umarci mawakin da ya sadu da shugaban ma’aikatan fadar sarkin Kano domin kammala shirye-shirye a kan nadin sarautar da za a yi masa. A kwanakin baya ne rahotanni su ka yada cewar sarki Sanusi II ya nada fitaccen mawakin kudu, Korede Bello, a matsayin sarkin mawakansa bayan an ga mawakin yayin hawan sallah a Kano.

Sai dai masarautar ta Kano ta fitar da sanarwar karyata rahoton tare da bayyana cewar mawakin aboki ne ga dan sarkin Kano. Za a nada Naziru Ahmad a matsayin sarkin mawakan sarkin Kano ranar 27 ga watan Disamba, a fadar mai martaba sarkin Kano.

Leave A Reply

Your email address will not be published.