sha’awa ce tasa na shiga harkar fina finai – Inji wani jarumi

0 315

– Tsabar sha’awa ce ta sa na shiga harkar fina finai

– Jarumin sunan sa Garzali Miko – Yace ya fara harkar fim din kusan shekaru 10 da suka shude A kokarin mu na cigaba da kawo maku labaran da suka shafi masana’antar shirya fina-finan Hausa da ake yi wa lakani da Kannywood, yau ma gamu dake da wata fita da daya daga cikin fitattun jarumai kuma sabuwar fuska a masana’antar yayi da majiyar mu.

Jarumin dai ba boyayye bane ba ga mafiya yawa daga cikin masu sha’awa tare da bibiyar harkokin fina-finan Hausa din kuma wannan ba kowa bane ba face Garzali Miko. Legit.ng ta samu cewa fitaccen jarumin kuma dan rawa ya bayyana cewa ya fara harkar fina-finan Hausa ne kimanin shekaru sama da goma da suka shude inda a da yake aikin bayar da haske kafin daga bisani ya kara samun matsayi a harkar. Haka zalika jarumin ya bayyana cewa tsabar sha’awa ce kawai ta jefa shi cikin harkar shi yasa ma ya faro ta tun daga tushe watau a matsayin karami a harkar ya ya zuwa yanzu da ya soma zama fitacce kuma jarumi. Garzali ya kuma kara da cewa akwai kalubale a harkar ta fim kamar dai sauran fannonin rayuwa da ma duk abinda dan Adam keyi wani lokaci a samu farin ciki wani lokaci kuwa a sami akasin haka.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.