Shahararren Jarumin Fina-Finan Hausa Ali Nuhu Yayi Aski Mafi Tsada A Tarihin Masana’antar KannyWood

0 339

Kowa yasan Jarumi Ali Nuhu ya sanshi da wani aski da ake kira FKD, wato aski ne wanda ake aske suma sama-sama.

kuma Ali Nuhu ya dade yana wannan aski tun shekaru da dama da suka wuce Sai dai A tsawon wannan lokacin bamu taba ganin Ali Nuhu ya aske Gashin kansa ba koda kuwa zai fito a film wanda za’a nuna baida suma misali film din Barde.

Sai dai wani abun da ba’ayi tsammani ba ba Ali Nuhun ya aske Gashin kan nasa duk da dai ba duka ba amma zamu iya kiransa da Aski mafi tsada a kannywood.

Domin kuwa ta wata majiyar tace furodusa Mustapha Ahmad ( Alhaji Sheshe) ya biya Ali Nuhu Naira dubu dari Biyar kafin a aske masa sumar tasa domin fitowa acikin film dinsa mai Suna Kazamin Shiri wanda yanzu haka ake kan daukarsa, Da muka tuntubeshi domin Jin ta bakinsa,  Furodusa mai film din Alhaji Sheshe ya tabbatar mana da labarin.

Shirin Kazamin Shiri ya kunshi Yan wasa irinsu Ali Nuhu, Fati washa, Bilkisu Shema, Aminu momoh,Rabi’u Rikadawa da dai sauransu Directer Sanusi Oscar 442 ne yake bada Umurni.

Leave A Reply

Your email address will not be published.