SHANAWA YA YI HADAKAR WAKA DA J. MARTINS

0 255

Fitaccen mawakin nishadantarwa, Ahmad Shanawa ya yi hadaka da shahararren mawakin Hip-Hop na Kudancin kasar nan, Martins Okechukwu Joshua Kalu Okwun wanda aka fi sani da J. Martins wajen yin waka mai taken ‘Baban Chakwai’ Remid.

Ahmad Shanawa wanda haifaffen garin Jos ne ya bayyana wa Aminiya cewa ya dade yana mafarkin yin waka da J. Martins inda a yanzu mafarkinsa ya zama gaskiya.

Shanawa wanda shi ne Babban Daraktan Gudanawarwa na Kmfanin Plan B Record da ke Jos ya bayyana farin cikinsa kan hadakar da ya yi da J. Martins.

Ya ce, “A gaskiya na ji dadin hadakata da J. Martins wajen rera wakar ‘Baban Chakwai Remid,’ kamar da wasa na nemi mu yi hadakar amma kuma ya amince ba tare da bata lokaci ba.”

Wakar mai tsawon minti 4 da dakika 5 wadda wakilin Aminiya ya saurara ya gano an yi ta da harshen Hausa da Ingilishi da kuma gurbataccen Ingilshin da ake kira Pidgin.

Ya ce, “J. Martins fitaccen mawaki ne da kowane mawaki zai so su yi waka tare da shi, na yi aiki da shi, kuma na ji dadin yin aiki da shi, domin yana da saukin kai da kuma fahimta.”

Shanawa wanda ya rera wakokin irin su ‘Kamas’ da ‘Gaskiya’ da kuma ‘Bawan Mata’ ya bayyana cewa a mako mai zuwa za a fara daukar bidiyon wakar a garin Jos.

Leave A Reply

Your email address will not be published.