Sharhin Fim Din – Fuska Biyu

Sharhin Fina Finai

0 298

Suna: Fuska Biyu
Tsara Labari: Yakubu M. Kumo
Kamfani: UK Entertainment
Shriyawa: Umar Kofar Mazugal
Umarni: Yaseen Auwal
Jarumai: Adam A. Zango, Lawan Ahmad, Halima Atete, Falalu A. Dorayi, Hauwa Waraka, Amal Umar, Hajara Usman, Umar Gombe, Hamza Indabawa. Da sauran su.
Sharhi: Hamza Gambo Umar

A farkon fim din an nuna Ubale (Adam A. Zango) a wajen sana’ar sa ta siyar da kifi tare da wani abokin tsamar da Haruna (Umar Gombe) wanda ya tsaya yana jagwalgwala masa kifi, yayin da Ubale yake yi masa korafin cewa duk garin babu wanda yake wulakanta masa kayan sana’a sai shi, a haka dai Haruna ya sayi kifin yana kushewa sannan suka bar wajen shi da abokin sa. Daga nan kuma Ubale sai ya tafi raka budurwar sa gida Rashida (Amal Umar) bayan ta tashi daga wajen da take siyar da abinci, kafin shigar ta gida sai Ubale ya bata kyautar dubu hudu amma dai tayi mamaki saboda tana ganin cewa sana’ar sa bata kai ya bata kyautar kudi me yawa haka ba, amma a haka yayi mata dadin baki har ta karba, haka bayan ta koma gida mahaifiyar ta take yiwa mahaifin Rashida korafi (Hamza Indabawa) akan kudin da yake bawa Rashida yafi abinda yake samu yawa, amma sai mahaifin Rashida ya nuna hakan ba komai bane.

Wata rana wani matashin saurayi yaje ya sayi kifi a wajen Ubale sai ya lura da agogon hannun Ubale wanda ya kasan ce me tsadar gaske, ganin agogon ne yasa yaje ya fadawa sauran abokan sa su Haruna, amma jin hakan sai suka kasa yarda suke zaton ko jabun agogo ne ba na ainahin me tsada ba, amma sai matashin ya tabbatar musu da lallai agogon da ya gani a hannun Ubale dan gasken ne ba me araha ba, jin hakan ne yasa suka tafi wajen Ubale gaba daya don ganewa idanun su gaskiyar lamari, saidai kuma lokacin da suka je wajen Ubale sai ba su ga agogon a hannun sa ba hakan ya basu mamaki. Bayan dan lokaci kadan soyayyar Ubale da Rashida tayi karfi har ma ya nuna ta nemo masa izinin iyayen ta don ya turo iyayen sa, amma bayan taje wajen iyayen ta akan maganar sai mahaifiyar Rashida ta nuna rashin goyon bayan ta akan auren, saboda ba’asan dangin Ubale ba kuma basu san inda yake kwana da duk wasu abubuwa da suka shafe sa ba, amma sai mahaifin Rashida ya nuna duk hakan ba hujja bace tunda dai Ubale musulmi ne kuma yana da sana’a to ba makawa zai aura masa ‘yar sa Rashida.

Cikin dan lokaci kadan waliyyan Ubale suka zo wajen mahaifin Rashida aka saka ranar aure ba tare da mahaifin Rashida din ya nemi sanin komai daga garesu ba, ganin hakan ne yasa bayan tafiyar su sai wan mahaifin Rashida ya soma korafi akan rashin yin tambayoyin su ga dangin Ubale, amma mahaifin Rashida ya nuna hakan ba komai bane domin Ubale musulmi ne. Kwatsam wata rana Ubale ya fito daga cikin wani hotel da nufin hawa motar da yazo da ita, kafin ya fita daga cikin hotel din sai wani me sayen kifi a wajen sa ya gan sa, duk da bai gama gane fuskar Ubale ba amma sai ya bi sa da sauri yana kiran sunan sa saboda mamakin ganin sa a hotel kuma ga kafafun sa da yasan yana dingishi amma a wajen yaga kafafun shi basu da wata matsala, haka yana gani Ubale ya shige mota ya bar wajen. Washe gari kuwa mutumin me suna Alhaji Sani wanda yaga Ubale a hotel sai yazo wajen Ubale sayen kifi yana jan Ubale da wasa har zuwa lokacin da Ubale ya miko masa ledar kifi motar sa, anan ne Alhaji Sani yake tambayar Ubale da cewar kamar shi ya gani a hotel, amma sai Ubale ya nuna sam ba shi bane, ganin yadda yanayin Ubale ya sauya sai Alhaji Sani ya kasa gasgata cewar ba shi ya gani din ba. Kwatsam iyalan Alhaji Sani suka wayi gari suka ga an yanka Alhaji Sani an yi masa kisan gilla da wuka. Nan fa jami’an tsaro suka fara bincike don neman wanda ya kashe Alhaji Sani.

A wannan lokacin ne suka kama wasu ‘yan daba suka tafi dasu ofishin su gami da tuhumar su akan sai sun fada musu inda wani kasurgumin dan ta’adda na cikin su yake. Ana cikin haka ne Ubale sun jero suna hira shi da budurwar sa Rashida sai take yi masa korafi akan surutan da mutane suke yi na cewar ba’asan asalin sa da kowa nasa ba. Anan ne Ubale ya nuna mata cewar ya dace ya bata labarin rayuwar sa tunda aure za su yi don haka yana da kyau ta san asalin sa. Anan Ubale ya soma bawa Rashida labarin asalin sa cewar tun kafin mahaifiyar sa ta haife shi suka fara samun matsala a tsakanin iyayen sa saboda mahaifin sa Rabi’u (Falalu A. Dorayi) yace zai karo aure hakan ne yasa mahaifiyar Ubale ta tayar da hankalin ta gami da nuna sam bata yarda ba, ganin hakan ne yasa Rabi’u yaje yakai karar ta wajen mahaifiyar ta Inna Tabawa (Hajara Usman) itama jin za’a yiwa ‘yar ta kishiya sai ta nuna goyon bayan ta akan rashin mutuncin da ‘yar ta take yi masa, haka sauran ‘ya’yan ta zaurawa su (Hauwa Waraka) wadanda suma suka goyi da bayan yayar sa akan ba su yarda a yi mata kishiya ba, nan suka soma yiwa Rabi’u rashin kunya har suka rabu baram-baram. Ganin haka ne yasa Rabi’u yaje ya samu wadda zai aura Mairo (Halima Atete) ya fada mata halin da ake ciki, amma sai Mairo ta nuna zata iya auran sa bata damu da matsalar kishiya ba. Jin hakan ne yasa Rabi’u ya auro ta ya ajiye a gidan sa bayan yaje ya saki uwargidan sa wato mahaifiyar Ubale wadda bai so ya saketa ba amma rashin mutuncin mahaifiyar ta Inna Tabawa da kuma ‘yan uwan ta su suka ja ya sake ta. Bayan Rabi’u ya saki mahaifiyar Ubale da tsohon ciki sai kannen ta su (Hauwa Waraka) suka zo gidan sa suka yiwa amaryar sa Mero duka, haka kuma bayan an haifi Ubale ko ganin sa mahaifiyar sa bata yi ba aka dauko shi aka kawowa mahaifin sa Rabi’u, nan fa amaryar sa Mero tayi tsalle ta dire ta nuna sam ba zata rike masa jariri sabuwar haihuwa ba, haka Rabi’u ya koma da jaririn yana rokon surikar sa mahaifiyar matar sa akan su rike yaron amma suka ki karba har sai da kotu ta nuna musu sai an yaye jaririn sannan Rabi’u ke da ikon karba, ai kuwa a ranar da aka yaye Ubale aka kawo shi wajen mahaifin sa a tsakiyar kasuwa aka damka masa dan sa, mahaifin Ubale ya karba yaje ya kaiwa yayan sa amma yaki rike masa yaron, haka ya koma wajen matar sa Mero itama sai da kyar ta karbi yaron a bisa sharadin mijin ta Rabi’u zai din ga bata kudin rainon yaron.

Haka Ubale ya taso cikin tsangwama da rashin gata har girman sa, dalilin hakan yasa ya fada muguwar sana’a ta yin garkuwa da mutane. Bayan Ubale ya gama bawa budurwar sa Rashida labari sai suka yi sallama suka rabu, ba’a dau lokaci ba kuwa aka daura auren Ubale da Rashida saidai bayan an daura aure tun kafin Jama’a su watse sai jami’an tsaro suka zo neman Ubale a motar su. Ganin motar ‘yan sanda ne yasa Ubale ya sulale daga cikin jama’a ya gudu ba tare da an gane ba, jami’an tsaro suka bi shi gami da bude masa wuta da harbi har suka garbe shi a kafar sa, amma duk da haka Ubale bai kamu ba har sai da yaje dakin sa ya hada kayan sa da kudaden sa da nufin guduwa, sai katsam wani jami’in tsaron farin kaya Bilya (Lawan Ahmad) wanda yake sana’ar wankin takalmi a wajen da Ubale ke sayar da kifi, shine ya shigo dakin ya kama Ubale ya tafi dashi ofishin su. A can ne Ubale ya fadi wasu daga cikin wadanda yayi garkuwa dasu a cikin mutane da kuma wadanda ya kashe, sannan kuma ya tabbatar wa da hukuma cewar shi ya kashe Alhaji Sani. A bangaren Rashida kuwa mahaifin ta tuni yayi nadamar rashin bincike da bai yi ba har aka riga aka daura auren ta da Ubale, nan suka fara shawarwarin yadda zasu je kotu a warware auren yayin da Rashida ta nuna sam bata yarda a raba auren ta da Ubale ba.

Abubuwan Birgewa:

1- An yi kokari wajen nuna illar rashin taimakon Dan Adam a rayuwa wanda hakan zai iya jefa rayuwar sa a mummunar hanya irin wadda abin zai zo ya shafi al’umma.
2- An nuna illar kwadayi na wasu iyayen gami da yiwa ‘ya’ya aure ba tare da zurfafa bincike ba wanda a karshe hakan yakan jefa iyaye tarkon da na sani da nadama.
3- An yi kokari wajen samar da wuraren da suka dace da labarin. (Locations)
4- Daraktan yayi kokari sosai wajen tafiyar da labarin, haka su ma jaruman sun yi kokari wajen taka rawar da ta dace.
5- Sauti ya fita radau, haka ma Camera ta fidda hoto me kyau, sannan kuma mai daukar hotan yayin kokari wajen nuna salon aikin sa.

Kurakurai:

1- Lokacin da Ubale ya raka budurwar sa gida, me kallo yaga lokacin da Ubale ya bata kudi har Rashida tayi korafin cewa kudin sun kai adadin cinikin sa na ranar, sai Ubale yace dubu hudu ce ai, amma bayan Rashida ta koma gida a sanda iyayen ta suke jayayya akan kudin da Ubale ya bayar, me kallo yaji lokacin da mahaifin ta yake cewa don yaro yayi kyautar Dubu Uku meye a ciki. Tunda an nuna kudin da Rashida ta kawo a hannun mahaifin nata, shin bai san cewa dubu hudu aka bata ba dubu uku ba?

2- Lokacin da wani matashi yazo siyan kifi yaga agogo me tsada a hannun Ubale, wanda dalilin hakan yasa yaje ya sake tahowa da sauran abokan sa don su tabbatar da abin da suke zargi, amma bayan sun dawo sai aka ga babu agogon a hannun Ubale. Shin Ubale yasan matashin zai sake dawowa ne da har ya cire agogon? Tunda ba’a nuna wata ‘yar tazara me nisa a tsakanin sanda matashin yaga agogon hannun Ubale da sanda yaje ya dawo ba, ya dace a samar da dalilin da yasa bayan dawowar matashin da abokin sa ba’a sake ganin agogon ba a hannun Ubale.

3- Lokacin da Bilya me wankin takalmi (Lawan Ahmad) yaje ya bude boot din motar Alhaji Sani don dauko takalman sa da za’a wanke, bayan Bilya me ya bude boot din me kallo yaga lokacin da ya firgita gami da dago kai yana kallon boot din cikin tsoro, kafin daga bisani da ya dau waya ya soma kira. Shin me Bilya ya gani a cikin boot din motar wanda ya firgita shi? Tunda an nuna Bilya matsayin jami’in tsaron farin kaya, to ya dace a nunawa me kallo abinda ya gani a motar wanda ya firgita shi.

4- Lokacin da asirin Ubale ya tonu a wajen daurin aure sanda jami’an tsaro suka biyo sa gami da harbin sa da bindiga a kafa, bayan Ubale ya shiga dakin sa ya hada kaya zai gudu, me kallo yaga sa’in da Bilya ya shigo cikin dakin ya rutsa shi da bindiga sannan ya tafi dashi. Sam bai dace Bilya yazo ya kama babban mai laifi irin Ubale shi kadai ba, ya dace ace Bilya sun zo kama Ubale tare da wasu abokan aikin sa, domin a yadda aka nuna Ubale mara tsoro kuma jajirtacce, to zai iya guduwa daga hannun Bilya saboda bindigar da ya nuna masa ba lallai ne ta tsorata shi ba.

5- Kwatsam me kallo sai yaga an nuno wasu ‘yan daba wadanda jami’an tsaro suka kama su suna tuhumar su don su fada musu inda wani mutum mai suna Dijango yake. Shin ta ya akayi jami’an tsaro suka fahimci cewar Ubale yana da alaka da wadannan ‘yan daba? Ya dace a nuna wa me kallo yadda aka bibiye sa har aka san yana da alaka dasu, ko da kuma ta hanyar nuna Bilya ya bibiye sa ne tunda an nuna shi a jami’in farin kaya. Haka kuma bai dace jami’an tsaro su tsaya tuhumar ‘yan daba a wajen ba, ya dace su tafi dasu kai tsaye zuwa ofishin su kafin su tuhumesu akan abinda suke so su sani a can.
6- Shin wane irin hukunci hukuma ta yanke wa Ubale? Duk da irin kisan gilla tare da garkuwa da mutane da aka nuna yayi, amma bayan an kama shi ko a fuskar shi ba’a ga nadamar abinda ya aikata ba, kuma ba’a nuna makomar sa ba, shin yaci bulus kenan?

Karkarewa:

Fim din ya fadakar kuma ya rike me kallo, sai dai kuma labarin bai dire har karshen sa ba, saboda ya dace a bayyana yadda karshen Ubale ya kasance, domin har fim din ya kare bayan an kama shi ba’a nuna wa me kallo irin hukuncin da hukuma tayi masa ba. Ya dace a bayyana yadda karshen sa ya kasan ce ko don hakan ya zamo izina ga mutane masu aikata dabi’u marasa kyau irin nasa. Wallahu a’alamu!

Leave A Reply

Your email address will not be published.