Shawara Akan Turanci Ga Mawakan Hausa HipHop Masu Tasowa – Daga Dabo Daprof

0 1,776

SHAWARA AKAN TURANCI GA MAWAKAN HAUSA HIPHOP MA SU TASOWA…

Daga Dabo Daprof

Dan Allah kira ga mafi yawancin ku yan uwan mu mawakan Hausa Hip Hop ma su tasowa, ku daina turancin da ba daidai ba ne ko ku rage inya zama dole ku yi turancin da ba daidai ba ne a wakar ku, kuna bada Arewa da ma jihar Kano ne, domin babu anfanin ka yi yaran da ba ka iya ba daidai a waka bayan ga na ka yaran na asali wanda ka kware a kai. San nan sama da kashi 70% na wannan turancin da su ke yi ba daidai ba ne, gashi kuma sama da kashi 80% na ma su sauraron wakokin ku ba sosai su ke jin turancin nan ba, kunga asara biyu kenan, ka yi waka amma kai kan ka ba ka san abun da kake fada ba a ciki, kuma ga sakon ka bai kai ga wadan da su ya kamata ya kaiwa ba. Ba laifi ba ne yin turanci a waka dan kai bahaushe ne ko dan kai Hausa Hip Hop kake, amma ka yi shi daidai kuma ka yi shi dan kadan, san nan in baka san kalma ko ma’anar ta ba, karka yi anfani da shi dan ta maka dadi a baki. Tashi ka je har wajan babban mawakin da ka san ya san waka sosai kuma ya ji turanci dan ya duba ma ka ya gyara ma, ku daina tura mu su baitin ku ta WhatsApp dan su gyara mu ku, da yan su ba wulakanci ko girman kai ba ne, ba su da lokacin da za su duba ma gyara a social media. Amma idan ta social media din ka ne mi zuwa ganin sa dan ya taimaka ya ma ka gyara, yawancin su ba za su ki ba. Akwai ma su zuwa neman gyaran har studio, gida ko wajan aikin wa su manyan mawakan, kuma ana sauraran su a kuma sa su a hanya. Billy-O a dala fm yana yi, Dr pure a rahma radio yana yi, da dai sauran su. Amma su ma ana mu su yawa, dan haka su ma manyan mawakan da ba sa sauraron kananan ya kamata su gyara dan zagin mutun daya zagin duk kan mu ne a Hausa Hip Hop na Kano dama Arewa.

Misali: Billy-O malamin turanci ne a makarantar koyan turanci ta Jammaje a nan kano, amma kowa yasan hausa ya fi yi a waka kuma ya daukaka da hakan, ga shima Dr pure, ga Classic, Dj Ab, ga Lil tea makaranta ce guda dashi primary da secondary, ga Buzo dan fillo, ga morel, ga lyrical Dr smith, ga Sonikman, ga A-styl ga Hazy D-star, ga AleeGee, ga khengs, ga David swuazo, ga M-kay, ga Bmeri Aboki, ga mixter bash, ga likitan waka, ga Aryan DC, ga B.O.C ga ga ga ga ga ga……suna nan ba adadi wanda duk sun daukaka a Hausa Hip Hop kuma suna jin turancin kamar ba gobe, amma duk da hakan turanci sai dai su dan jefa shi a cikin waka dan kadan amma Hausa tafi yawa. Saboda ita ce yaran da masoyan su suka fi ji kuma da ita suka tara masoya, amma kai da yanzu kake kokarin sanin ma mai harkar wakar, ka fara waka da turanci gashi kuma ba ma mai kyau ba, ta yaya zaka kai inda kake hari? Shawara ce ga mai tunani kuma darashi ga wanda ya shafa. Allah sa kuji kuma ku gyara Amin.

Sako daga Dabo Daprof
@dabo_daprof

Waka ta sabuwa mai suna MAI KAUNA TA zai fito ranar 30 ga wannan watan insha Allah fatan za ku neme ta inta fito.

Leave A Reply

Your email address will not be published.