Shekaru 20 A Matsayin Sarkin KannyWood – Ali Nuhu

0 327

SHEKARU 20 A MATSAYIN SARKIN KANNYWOOD


Sirrin daukakarsa ya samo asali ne daga jajircewa, sadaukarwa gami da daukar sana’arsa da gaske.

 1. Watarana na ganshi kwance cikin mota a yanayin rashin lafiya ya tattakure yana ta kyarma. Na ce Ali ya ba ka da lafiya ka zo nan? Ya ce na riga na amshi kudinsu shi ya sa ya zama dole na zo. Abin mamakin shine shine mutum na farko da ya zo wajen ba Furodusa ba Darakta ba sauran ma’aikata.
 2. Wani lokaci na ziyarci ofishinsa FKD yana koyar da rawar fim din KHUSUFI ya dakatar muka kebe. Me ya sa mutane suke cewa kana da girman kai? Kai tsaye na tambaye shi. “Ka san kowane mutum da yadda Allah Ya halicce shi, ni mutum ne mai zafin rai, sannan su kuma wasu mutanen ba su da manner of approach ma’ana ba su iya mu’amala ba. Wani lokacin za su same ni cikin cajin kai, wani lokacin su yi maka abinda zai hasala ka”.
  Kusan na san masu suna ALI suna da zafin rai ko zuciya, kamar yadda na san ‘yan fim da ba su kai shi ba amma sun ninka shi girman kai da raina mutane.
 3. Yayin da muke kan hanyar zuwa jihar Kaduna Darakta Hassan Giggs tare da Mudassir Haladu suke fadin alherin sa, mutum ne da abin hannun sa bai rufe masa ido ba. Idan ya yi maka kyauta za ka sha matukar mamaki. Bisa abubuwan da suka rika fada sai na tabbatar ya cancanci ci gaba da jagorancin Masarautar KANNYWOOD.
 4. Ranar sadakar ukun Marigayi Ahmad S. Nuhu wanda shine abokina, kuma jarumin shirin Fim dina #JUYAYI, manyan ‘yan wasa da yanzu suke sharafinsu kewaye da Ali ba wanda ya iya daga kai ya kalle ni. Amma haka ya daga murya, ya ce Sarkin Marubuta karaso mana. Ya ce musu wannan shine Maje El-Hajeej Hotoro shine ya sa na fara Darektin.
 5. Kananan ‘yan fim da dama idan aka zalince su suka rasa mafita wajen Ali suke garzayawa ya kwato musu hakkin su.
 6. Lokacin da rikici ya hada Adam A. Zango da Dan jarida Aliyu A. Gora II ‘yan jaridu sun kudiri aniyar yakarsa don nuna halacci ga Ibrahim Sheme amma Ali ne ya tafi Abuja ya kashe wutar.
 7. Yau kusan duk wani fitaccen FIM ko wani Dan FIM da ya shahara za a samu Ali Nuhu a ciki.
  Ina taya Sarkin KANNYWOOD Ali Nuhu Mohammed murnar cika Shekaru 20 bisa karagar mulki.

Thanks @majeelhajeej

Leave A Reply

Your email address will not be published.