shin Kun san sabon babban sufeton ‘yan sandan Najeriya?

0 240

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada sabon babban sufeton riko na ‘yan sandan kasar.


Sabon babban sufeton ‘yan sandan shi ne Adamu Mohammed.
Ya maye gurbin Ibrahim Idris, wanda ya sauka daga kan mukaminsa bayan ya kai shekara 60 da haihuwa kamar yadda doka ta tanada.
‘Yan sanda sun kama Sanata Dino MelayeTun da fari, mai taimaka wa shugaba Buhari kan shafukan sada zumunta, Bashir Ahmed ya wallafa sako a shafinsa na Twitter da ke cewa manyan jami’an ‘yan sandan na ganawa da Shugaba Buhari a fadarsa da ke Abuja.

A cewar Bashir Ahmed, “Yanzu haka sabon babban sufeton ‘yan sandan Najeriya da babban sufeto mai barin gado suna ganawa da shugaban kasa.”


Daga bisani an nuna Shugaba Buhari da Ibrahim Idris suna makala wa Adamu Mohammed alamar mukamin babban sufeton ‘yan sandan.
Wata sanarwa daga kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya ya fitar ta ce sabon babban sufeto janar din na riko, gogaggen jami’in dan sanda ne da ya yi aiki da kuma karatu a fannoni daban-daban, a ciki da wajen kasar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.