Shin Malaman Addini Zasu Iya Sa A Zabi Atiku Ko Buhari?

0 181

Daga Aliyu Dahiru Aliyu

Zaben 2019 na kara gabatowa kuma kamfen din siyasa na ci gaba da gudana a tsakanin sababbi da tsofaffin jam’iyyu.

Kusan kowane lungu da sako ka shiga za ka tarar maganar da ake kenan, daga teburin mai shayi zuwa shagunan kasuwanni.

A lokuta da yawa hakan yana tsallakawa ya tafi masallatan Juma’a da majami’u inda malaman addini ke shiga gaba wajen bayar da gudunmawarsu ta hanyoyin da suke ganin zai taimaki mabiya addinansu.

Tare da cewa muryoyin jagororin addini na da karfi wajen mahangar mabiyansu ta fuskar siyasa amma wasu lokutan ana zargin cewa wasu daga malaman na amfani da addinin ba ta hanyoyin da suka dace ba.

Maimakon su zamo masu kare muradu da hakkokin mabiyansu baki daya sai wasu daga gurbatattun ‘yan siyasa su yi amfani da muryoyinsu wajen juya akalar muradinsu daga taimakon talaka zuwa amfani da talakan ta hanyoyin da ba su dace ba.

Wannan ya janyo wasu daga mabiyan su na bijirewa zabin malaman nasu.

Tare da cewa kabilanci da bangarenci na taka muhimmiyar rawa wajen rayuwar ‘yan Najeriya, to amma addini ya fi tasiri a mahangar ‘yan kasar idan aka yi la’akari da cewa Najeriya tana da kabilu sama da 300 amma kabilun da suka fi tasiri ba su wuce guda uku da suka hada da Hausa-Fulani, Ibo da Yoruba ba.


Masana ilimin zaman jama’a na ganin cewa babu abin da yake da karfin tabbatar da alaka tsakanin mabanbantan mutane fiye da addini. Wannan ta sanya addini yake da tasiri wajen juya al’ummar da ta kasa juyuwa ko ta hanya mai kyau ko mara kyau.

Najeriya ita ce kasa mafi yawan mutane a nahiyar Afirka da mutum miliyan 182 a shekarar 2015.

Giwar Afrika, kamar yadda ake mata take, ta rabu gida biyu tsakanin Kudu mai yawan mabiya addinin Kirista da kuma Arewa mai yawan mabiya addinin Islama.

A tsakaninsu akwai mabiya addinin gargajiya kadan da ba su da ta cewa a siyasar kasar da ta cakude da kabilanci, bangarenci da kuma rarrabuwar kan mabiya addinai.

Har ya zuwa yanzu dai ba a da tabbacin kididdigar yawan Musulmi da na Kirista a Kasar, amma dai iya abin da aka iya ganowa ya nuna Musulmi sun fi Kirista yawa da kaso kadan.

Su kam mabiya addinin gargajiya ba su fi a kididdige cikin karamin lokaci ba. ‘Yan tsirarun da ba sa bin addini kuwa ba su kai yawan da har sai an tsaya dogon lissafi a kansu ba.

A Najeriya da aka tabbatar da cewa tana daga cikin manyan kasashen da ake bin addini sau-da-kafa, malaman addini na Islama da na Kiristanci suna da matukar tasiri wajen juya akalar ‘yan kasar.


A wasu lokutan malaman addini suna kokari su bayyana cewa kokarinsu na zabar ko kin zabar wani dan takara yana da alaka da hidimar addini ta hanyar daukaka ko kariya.

Wani abu da yake karawa mabiya armashin mika wuyansu ga malaman addini domin zabin siyasa shi ne tsoro da fargabar da take cikin rayukan wasu na cewa addininsu yana cikin hadari matukar suka zabi wani ba dan cikinsu ba.

Babban misali a nan shi ne, shekarun baya jama’ar kudancin Najeriya sun ta ganin cewa Shugaba Muhammadu Buhari na shirin kafa shari’ar Musulinci ne a kasar.

Wannan farfaganda ta sanya dole Buhari ya dinga dauko manyan malamai mabiya addinin Kiristanci domin su zamar masa mataimaka.

A wasu bangarorin kuma, da yawan malaman addinai suna kokari wajen ilimantar da mabiyansu kan harkokin zabe da kuma zaben shugabanni na gari.

Tamkar shugabannin gargajiya, ana ganin malaman addini a matsayin iyayen al’umma da suke haskawa mutane wadanda za su jagorancesu a lokutan zabe.

Malaman addinai na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da an yi zabe cikin kwanciyar hankali da lumana hade da addu’o’in wanzar da zaman lafiya da ci gaban kasa.

Akwai manyan malaman addinan Islama da na Kirista da za su iya tasiri a zaben da ke karatowa na 2019, musamman a arewacin Najeriya.

Malaman na da mabiya masu yawa a fadin Najeriya da suke sauraron muryarsu har ta zamo mai tasiri ga mahangarsu. Manya daga cikinsu da muryarsu ke yawan fitowa sun hada da:

Sheikh Dahiru Usman Bauchi


Dattijo ne kuma jagora ga mabiya darikar Tijjaniya a fadin Najeriya.

Tare da cewa tsufa ya kama shi amma har yanzu muryarsa na garawa a fanni daban-daban na rayuwar musulmin kasar, musamman ‘yan darikarsa ta Tijjaniyya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.