Shin Me Ya Kawo Gaba Tsakanin Jarumi Ali Nuhu Da Abba Al-Mustapha

0 255

Abba Al-Mustapha yayi kira ga jama’a da suyi koyi dasu duba da yanda suka raba gari a siyasance

Fitattun jaruman Kannywood Abba Al-Mustapha da Ali Nuhu sun gargadi jama da suyi siyasa ba tare da gaba ba.

A sakon da ya wallafa a shafin sa na Instagram, Al-mustapha ya rubuta cewa kasancewa ra’ayin su ba daya bane a siyasa, shi da Ali Nuhu na cigaba da tattaunawa wajen farfado da ayyukan samun cigaba.

Yayi kira ga jama’a da suyi koyi dasu duba da yanda suka raba gari a siyasance. Shima Ali Nuhu ya sake maimaita sakon da takwaranshi ya wallafa a shafin sa.

Jaruman dai sun kasance daga cikin fitattun jaruman kannywood dake goyon bayan jam’iyu daban-daban gabanin zaben 2019.

Ali Nuhu yana goyon bayan dan takarar APC, General Muhammadu Buhari yayin da shi kuma Abba Al-mustapha ke goyon bayan Atiku Abubakar na jam’iyar adawa ta PDP.

Dukanin su suna taka rawar gani wajen yakin neman zaben dukanin yan takarar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.