Shin Meke Tsakanin Hadiza Gabon Da Nafisa Abdullahi?

0 274

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi, ta ce tana zaune da kowacce jaruma ne “a kan yadda take so su zauna.”

Nafisa, ta yi wannan bayani ne, a cikin wata hira da ta yi da BBC a kwanakin baya.

Jarumar ta ce, “duk wadda ke son zama da ita lafiya lau, to za su zauna lafiya, wadda kuma ke da akasin hakan to takan tafiyarta da ita a kan yadda take so.”

Ta ce ita yanzu a tsakaninta da ‘yan fim, “babu wadda ba sa zaman lafiya.”

Jarumar ta kuma yi karin haske a kan dangantakarsu da jaruma Hadiza Gabon, wadda suka samu sabani a baya.

Ta ce bayan sabanin da suka samu a baya, a yanzu sun fahimci juna.

Nafisa ta ce, “ko da yake ba mu cika haduwa ba, idan dai har mun hadu muna gaisawa.”

“Tsammanin da mutane ke yi na cewa har yanzu muna gaba da juna, wannan ya kau,” in ji ‘yar wasan.

Ta ce “dama shi zaman duniya idan dai har ana tare to wata rana dole a samu sabani, domin ko harshe da hakori ma su kan saba.”

A shekarar 2017 ne fitattun jaruman biyu suka yi fada inda wasu rahotanni suka ce har da duka yayin da suke tsakar shirya wani fim.

BBCHAUSA

Leave A Reply

Your email address will not be published.