Shugaba Muhammad Buhari Ya Ce Obasinjo Na Bukatar Likita Ya Duba Lafiyarsa

0 196

Gwamnatin Shugaban Najeriya ta mayar da martani kan wasikar da tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo ya fitar wadda a ciki ya soki lamirin gwamnatin.

Mallam Garba Shehu, kakakin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke nan ke mayar da martani a kan wasikar da tsohon shugaban kasar Cif Olusegun Obasanjo ya fitar a kan mulkin gwamnati mai ci gabanin zaben shugaban kasa da ke tafe a watan gobe.

Kakakin ya bayyana wasikar da tsohon Shugaban Kasa Cif Olusegun Obasanjo ya fitar a jiya a matsayin wani yunkurin wasu ‘yan siyasa da ba za su iya ja da Shugaba Buhari ba a siyasance sai dai su rika cin dunduniyarsa.

Sanarwar ta ce da alama tsohon shugaban kasar na bukatar kwararren likita ya duba lafiyarsa, inda ta yi masa fatan samun waraka cikin sauri:

“Shawara a gare shi, shi ne ya nemi likita, ya nemi magani. Muna yi masa fatan Allah Ya ba shi lafiya”.

Sannan sanarwar ta kuma bayyana Obasanjo a matsayin mai hassada saboda ya san Shugaba Buhari ya fi shi martaba a idan duniya, kamar yadda sanarwar ta ce.

Ta kuma ce Cif Obasanjo na juya wa duk mutumin da ya ga ba zai kyale shi ya yi abin da ya so ba, kuma ya fitar da wasikarsa ta sa a yau ne domin ya rasa mafita domin ci gaba da tatsar haramtacciyar dukiyar da ya saba yi a shekarun baya.

Kakakin shugaban na Najeriya ya kuma ce zaben shugaban kasa da za a yi a watan gobe zai kasance sahihi kamar yadda Shugaba Buharin ya alkarwarta wa kasar da duniya baki daya.

Ga yadda ya bayyana abin da ya kira makomar tsohon shugaban kasa Obasanjo da abokan tafiyarsa bayan an bayyana sakamakon zaben shugaban kasa da ke tafe:

“Abin da muke so mu nuna masu a nan shi ne, kayin da suka sha a wancan karon somin tabi ne, kuma wanda za su gani a zabe mai zuwa sai ya rugurguza su a siyasance.”

Ya kara da cewa, “Daga wannan lokacin ba za a sake jin kansu ba, domin karshen siyasarsu ta zo. Jama’a za su kada kuri’a luma za su yi masu kayen da ba su taba tsammanin zai same su ba.”

Yaki da cin hanci da rashawa

A fagen yaki da cin hanci da rashawa kuwa, sanarwar ta kira tsohon shugaba Obasanjo babban matsoraci, bayan ta zarge shi da karkatar da dala biliyan 16, kudin da ta ce an ware domin samar da wutar lantarki a lokacin mulkinsa, aikin da ta ce ba a yi ba samsam, ta kuma ce yana cike da tsoron ranar da za a tuhume shi ya bayyana abin da yayi da kudaden.


Hakkin mallakar hotoGETTY IMAGESImage captionTsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo

Yaki da kungiyoyin ta’adda

A kan batun yaki da kungiyar Boko Haram kuwa, Mallam Garba Shehu ya yi watsi da ikirarin tsohon shugaban cewa gwamnatin Shugaba Buhari na da hannu wajen fadawar da Libya ta yi cikin rikici:

Garba Shehu “Ka dubi Najeriya, ka ce wai Boko Haram a karkashin mulkin Shugaba Buhari ta fi karfi, wannan magana ce ta mafarki.”

Ya kuma ce, “Ko kuma ka ce za ka zargi Shugaba Buhari don kasar Libya ta rushe… ai a lokacin gwamnatinsu ta PDP ce ke mulki, wane mataki suka dauka akai?”

A karshe, sanarwar da Mallam Garba Shehu ya sanya wa hannu ta yi watsi da wasikar ta Cif Oasanjo musamman inda ya ke cewa Shugaba Buhari ya shirya murde zaben shugaban kasa wanda zai gudana kasa da mako hudu mai zuwa.

Garba Shehun ya ce abin takaici ne a ce dan shekara 90 da haihuwa ya zama “tsohon makaryaci”, kuma shugaba Buhari zai ba mara da kunya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.