Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari Yayi Wasu Sababbain Nade-Nade a wasu Hukumomin kasar

0 147
Shugaba Muhammadu Buhari Yayi Sababbin Nade-nade a wasu Hukumomin Kasar Nan.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi sabbin nade-nade a wadansu hukumomin gwamnatin kasar a ranar Alhamis.

Wadanan nan nade-nade na zuwa ne a daidai lokacin da ake tunkarar zaben 2019, wanda shugaban ke takara domin neman wa’adi na biyu.

A baya dai an soki shugaban da jan-kafa wurin yin nade-nade abin da ya sa wasu ‘yan jam’iyyar sa ta APC ke cewa “sun tura mota amma ta budesu da kura”.

Ya nada Dokta Anas “Ahmad Sabir” a matsayin babban daraktan asibitin koyarwa na Jami’ar Usman Dan-Fodio dake Sakkwato.

Sai Dokta “Theresa Obumneme Okoli” wadda ya nada shi sabon shugaban Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Horas da Malamai da ke garin Umunze a jihar Anambra.

Akwai kuma Dokta Emmanuel Ikenyiri wanda ya nada shugaban Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Horas da Malamai da ke garin Omoku a jihar Rivers.

Har ila yauShugaba Buhari ya nada Dokta Pius Olakunle Osunyikanmi a matsayin daraktan wata hukumar ba da agaji wanda ake kira Technical Aid Corps.

karshe shugaban ya bukaci mutanen da su yi aiki tukuru kuma su kasance masu mutunta dokokin aiki.
Wasu na ganin wadannan nade-naden da shugaban keyi a ‘yan kwanakin nan baza su rasa nasaba da kokarin gyara kura-kuran da yayi ba kafin babban zaben na gaba.

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.