Siyasa ba da gaba ba: Gidan Danja ya zama abin kwatance

0 488

Siyasa ra’ayi ce, zaka ga wa na son jam’iyyar daban da wadda kani ke so ko kuma uba na son jam’iyya ko dan takara daban da wadda danshi yake so,hakan ma na faruwa tsakanin mata da miji.

Ga inda aka samu ilimi da wayewar Dimokradiyya wannan banbancin baya haifar da matsalar dangantaka tsakanin makusanta.

Irin wannan ne ya faru kwanannan a masana’antar fina-finan Hausa.
Tauraron fina-finan Hausa, Sani Musa Danja, Zaki sannannen dan jam’iyyar PDPne dan kuwa indai kana bibiyarshi a shafukanshi na sada zumunta zaka tabbatar da haka.
To sai gashi matarshi kuma tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa, Mansurah Isah da yanzu ta koma bangaren taimakawa mabukata ita kuma tana goyon bayan jam’iyyar APC.
Wannan lamari da ya faru a tsakanin ma’auratan ya zama wani abin misali da akaita amfani dashi musamman a shafukan sada zumunta ana nusar da mutane, musamma  matasa cewa siyasa ba tana nufin gaba ko fada ba dan ra’ayinka ya banbanta dana wancan ba.
Da dama sun yabawa ma’auratan.
Haka kuma shima wani hoto da aka ga Ibrahim Maishunku wanda Masoyin APC da Buharine da kuma Zaharadeen Sani wanda shi kuma masoyin PDP da Atikune da kuma Abdulamart Maikwashewa wanda shi kuma masoyin Buhari da APCne suna raha shima ya zama abin kwatance da birgewa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.