SIYASAR KANO: Kano Ta Ganduje Ko Ta Kwankwaso?

0 193

Babban abun mamaki da kuma ban takaici tsakanin siyasar jihar Kano, shine yadda aka samu rarrabuwar kawuna tsakanin tsohon gwamnan jahar Kano, Dr Rabi’u Musa Kwankwaso, da kuma gwamna ma ici yanzu Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Yau an kai kusan tsawon shekara daya zuwa biyu babu jituwa tsakanin wadannan mutane guda biyu.

Kowanne daga cikinsu dan siyasa ne sananne, kana hamshakin masanin siyasa, wannan shine ke diga alamar tambaya akan cikinsu wa ya fi magoya baya dakan iya dakile tauraruwar wani?

Sau da yawa za ka ga kowanne daga cikinsu yana jefar dayan da kalamai masu ban takaici akan siyasar cikin gida, da kuma waje.

Duk da cewa kowanne daga cikinsu ya yi wa jihar Kano aiki, sai dai akwai ban mamaki kan yadda jama’ar Kano keci gaba da nuna soyayar su ga Tsohon Gwamnan Dr Kwankwaso.

Haka shi ma Ganduje fa ba a bar magoya bayan sa a baya ba, domin shi ma hamshakin dan siyasa ne da ya yi wa Kano aiki tukuru.

Kira na tare da fatana ga Kanawa, da kuma ‘yan siyasar jihar shine su hada kai wuri daya kamar yadda aka san su a baya, domin ta haka ne za su iya maida Birnin Kano kamar Birnin Landan.

Daga Abdullahi Muhammad Maiyama

Leave A Reply

Your email address will not be published.